HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Ke! Fiddausi ya isheki haka idan bak’ya cikin hayyacinki to kiyi saurin dawowa hankalinki tunkafin insab’a miki, ki sani zan jure kowanne rashin mutuncinki Amman ba zan jure ki dinga ciwa d’an uwana mutunci shida iyalinshiba ko a bayan idonshi balle agabanshi, don haka inaso kisani munriga mun yanke hukunci aure tsakanin Zahra da faruoq tamkar anyishine donke baki isa ki sauya abinda Allah ya tsaraba…..!”

Cewar dadyn faruoq, itama a zafafe ta katseshi

” to ni ban aminceba bada yawuna donko bayan raina ban amince ya auretaba, kome zakace saidai Kace Amman nidai nace banyarda ya auri wannan figaggiyar yarinyarba mai siffar Aljanu,”

Azuciye daddy ya kawo mata wani bahagon mari saidai da sauri uncle Aminu ya rike mai hannu yana tausarshi akan ba a biyewa mace subi komai a hankali shi kuwa cewa yake yasakeshi ya koya mata hankali shi kuwa sai tausarshi yake yana nunamai kodan yaran ya rabu da ita da kyar ya damu ya rarrashi ya yan nashi don yasan tun suna k’anana bai iya fushiba yana da hakuri sosai Amman inka kaishi bango anan zakaga kafiyarshi, faruoq ne ya rrarrafo gaban mahaifiyartashi ya rike mata k’afa yana fad’in

“Dan girman Allah mamy ki taimakeni ki taimaki rayuwata karki rabani da Zahra,wallahi mamy ba had’amu su daddy sukaiba daman can inasonta Dan Allah ki sawa abin albarka kamar yadda kowa yasa mana wallahi mamy ba zan IYA rayuwa da kowacce maceba inba Zahra ba nikadai nasan irin sonda nakeyi mat……….”!

KUNA IYA SIYAN DATA NA MTN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA A NIGERIA
1GB = 250 NAIRA
2GB = 480 NAIRA
3GB = 700 NAIRA
4GB = 950 NAIRA
5GB = 1200 NAIRA
10GB = 2400 NAIRA
15GB = 3500 NAIRA

IDAN KUNA BUKATA KUYI MANA MAGANA TA WANNAN NAMBAR 08140419490, TA WATHASSAP KO KU KIRA MU

Wani irin hantsilawa yayi sakamakon hanb’arar dashi da tayi da k’afar da ya rike mata,

” nikake cewa kanason wannan mai kama da kazar mayun? Har kanacemin bazaka IYA rayuwa da kowacce maceba sai ita? Lallai bansan husna da Aminu Na haifawa kaiba saiyau da har kake shirin k’etare umarnina danka faranta musuba, to yayi muku kyau nidai na gama magana ban aminceba.”

Tana kaiwa nan tai d’akinta ta banko k,’ofa, ko a dakinma sintiri ta dingayi takai ta kawo gaba d’aya ranta a jagule yake jin abin take tamkar a mafarki wai Zahra zata zama sirikarta tayaya ma zata yarda da hakan yarinyarda tun da aka haifeta taji duk tsanar da taiwa mahaifiyarta ya dawo kanta sannan ace wai yanzu ta zama sirikarta ai abinda bazai taba yiyuwa bane, hakadai ta dinga sak’a da warwara ita kad’ai, acan kuwa kowa yai jigum jigum anrasa mai magana koya abin baimai d’adiba, musamman faruoq da bai tab’a zaton zai sami matsalaba akan auren saigashi ya samu ga k’arin takaicinshi abinda bai taba ganin ya faru tsakanin iyayen nashiba dai gashi yau ya faru ta silarshi
sauran k’annenshima sunshiga damuwar hakan sosai musamman Aunty Jidda da takejin kunyar had a ido da su Zahra SBD abinda mahaifiyarsu tayi , itakuwa Zahra inbanda sharar hawaye ba abinda takeyi Na cin mutuncin da akayiwa iyayenta agabanta aranta kuwa ta k’uduri aniyar rabuwa da faruoq duk da sonda takeyimai,
itama Momy husna ranta ya baci sosai dan duk abinda fiddausin ke yimata bata tabajin zafi irin Na yauba itama ganinta gwara a hakura kawai shiyafi, shi ma uncle Aminu jiyai abin ya fitadaga ranshi, shi kuwa daddy yanzune ma yaji k’arfin gwiyar yin had’in don saiya nunawa fiddausi iyakarta, kallon faruoq yai yace,

” Babana karka sa wannan abin aranka ka kwantar da hankalinka aure babu fashi, kaje ka fara shirye shiryen aurenka nan kusa,”

Daddy mamy fa tace,,,,”

“Kaudai kaje kayi abinda nace ka barni zan ji da komai tashi kaje,”

Shima mikewa yai ya tafi kamar yadda sauranma sukai wajen ya zama su biyu kawai dagashi sai k’aninshi uncle Aminu shi yaso an hak’ura da abin Amman daddyn yace baza a fasa komaiba shidai yabar komai a hannunshi, cike da kwarin gwiwa ya nufi part dinsu ko dayajema sosai ya kwantarwa da Momy husna hankali ya nuna mata hakan k’arin karfin zumunci ne atsakaninsu don haka itama ta fara duk shirye shiryen da tasan zatayi, itama hankalinta ya kwanta don Harta taushi Zahra ta mata nasiha sosai kuma itama zahran ta d’auka don da ko wayar faruoq din kin d’auka tayi,

Ahakadai kwanakin suketa juyewa satika ayanzu shirye shiryen bikin Aunty Jidda ake tayi kowa ya sake don ba Wanda ya kara tada maganar itama mamy fiddausin tun tana jiran hukuncin da mijinnata zai mata harta sake, yanzu shirye shiryen biki kawai tasa gaba itada Babbar aminiyar ta suke komai kuma da ita take shawara wato HAJIYA SALAMATU,

Bangaren Zahra ma sosai takeshan gyara ciki da waje don musamman Momy husna ta d’auko wata yayarta AUNTY AYSHA take zuwa har gida tana gyara zahran,

haka kwanakin da sukai saura sukazo ayanzu saura kwana biyu bikin Aunty jidda, yauma d’akin cike yake da k’awayen Amarya anata kwasar fira da shewa kowacce taci kwalliyar zuwa dinner Amarya kawai ake jira a gama shiryata a tafi

faruoq ne ya lek’o d’akin yaci ado kamar ango sai walwali yake yace,

“Wai Jidda me kuke a d’akin darefa nayi kuna kinsan dakyar daddy ya bari”,

Kafin tayi magana tsagal wata daga k’awayen amarya ta bashi amsa,
” ayi hakuri babban yaya gamunan fitowa,”
Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai donshi kwata kwata yarinyar batamaiba ta cika rawar kai ga wani matsatstsen din ki da ke jikinta sai wani taunar cimgam takeyi sai Kace akuya,
tsaki yayi sannan ya fice da kallo ta bishi don itadai yayi mata sosai, kallon Jidda tai “jiddah wannan yayankine yaushe ya dawo?”

Eh yayanane yaya faruq bai Dade da dawowaba shiyasa Baki sanshiba kinga ma wacce zai aura insha Allah,
da sauri suka kalli kuna, itada Zahra tab’e baki yarinyar tayi mai suna JAMILA Amman anfi kiranta da JAMCY itace ‘ya d’aya tilo agurin mahaifiyarta HAJIYA salamatu babbar aminiyar mamy fiddausi,
duk ficewa sukai suka nufi wajen dinner, ko a canma sosai jamcy ta dinga shishshigewa faruoq shi kuwa ko kallo bata isheshiba balls yakulata har aka tashi, washe gari walima akayi a harabar gidan, ana gobe d’aurin aure,

Washe gari
Ta kama ranar d’aura aure gaba d’aya unguwar ta d’inke da mutane anyi duk abinda ya dace sannan marok’i ya sanarda d’aurin Auren JIDDA ABUBAKAR UMAR
Tare da angonta Bilyamin Abdullahi,
Can kuma akaji marok’in Na fad’in jama a Ku shaida and’aura auren

UMAR FARUOQ ABUBAKAR
Tare da Amaryarshi

FATIMA ZAHRA AMINU
Akan sadaki dubu d’ari lakadan ba Ajalanba…………..!
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 75_80

Mutuwar zaune faruoq yayi ya kasa motsawa daga inda yake jin abinda marok’in ke fad’a, hak’ik’a abin ya zomai unexpected asanda bai tab’a zatoba, Amman kuma cikin. Zuciyarshi hamdala kawai yakeyi da tasbihi ga ubangiji don yasan wannan ikonshine shiya nufi hakan, Abokinshine Dr Ahmed ya dawo dashi daga shork din da ya shiga sakamakon girgizashi da yayi yana fad’in,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button