HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Lallal faruoq abin ‘Yar hakace? Daman kasan hard a kai za a d’aurawa aure Amman shine kaki Sanar dani? Lallai yayi daidai,” isowar sauran abokanshine wajen nan suma suka fara tsokanarshi damai tsiyar b’oye musu da yayi don duk yawanci sunzo Amman bikin k’anwarshi yace musu, haka suka dinga tsokanarshi shidai inbanda murmushin jin dadi ba abinda yake aranshi yana k’ara jinjinawa iyayen nashi maza da girmansu da ya k’aru a idonshi a haka ya dinga gaisawa da mutane,
Abincin d’aurin aure aka dinga fitowa dashi anci ansha zuwa wani lokaci duk an watse sai ‘yan tsiraru Na jiki, Ango faruoq nacan inda ya sauki abokanshi anan yake musu bayanin yadda auren shima yazomai a baza ta k’arar wayarshine ya katseshi, zarota yayi daga aljihunshi sunan daddynshi ya gani dan haka da sauri yayi picking,cemai yai yazo ya sameshi a d’akin saukar bak’i yanzunnan, da toh ya amsa sannan yacemai gashinan zuwa ,uzuri ya basu yace musu yana zuwa sannan ya fita,

A can cikin gida ma Amarya zahrace keta kuka ta tasa iyayen nata agaba tana rizgar kuka don itama a baza ta auren ya zo mata don itadai ta Riga ta hamura da faruoq tin fadewa sabpda baza ta iya jure cin mutuncin mahaifiyarshiba, da acema abin zai tsaya akanta da sauk’i Amman ita sune batason a tab’a mata, sosai suka dinga rarrashinta da nuna mata haka ubangiji ya tsara don haka tayi hak’uri insha Allah Alkairine Auren, da kyar dai suka samu suka sa tai shiru sannan mahaifiyarta ta mata nasiha sosai akan zaman aure sannan ta tashi tabi bayan mahaifinta suka fice daman tin d’azu ya shigo ya tafi da ita ya sami suna kuka, itama Momy husna sosai tai kukan rabuwa da tilon yarta ta da take matukar kauna kefe d’aya kuma tanajin tausayinta yadda zatai rayuwar aure cikin tsangwamar uwar miji dukda mijinta yai mata bayani,sosai tabi zahran da adduoi kuma tai niyyar ko yaushe zata dinga sata a adduarta,

Kai tsaye parlour n saukar b’akin ya nufa da ita batare da ya bari wani ya gansuba, acan suka tarar da faruk harya iso bayan zamansu uncle Aminu ne yai musu nasiha sosai sannan daddy yai musu tashi, sannan ya d’ora da fad’in,

” inason daga nan zaku wuce gidanku basai kun koma cikiba,akwai address d’in gidan zan baka shine gidan da Na mallaka maka, gidan yanacan Abuja inason kuyi nesa da gida ne,kuma inkun tafi bana son kuzo gidan nan akwana kusa Ku bari sai and’auki lokaci sosai, lokacinda mahaifiyarka ta sauko tukunna, babu Wanda yasan inada gidan dagani sai Aminu,kuma anzuba muku komai ba abinda kuke bukatar tafiya dashi hatta lefen nata yana can don haka yanzu ka mik’omin layinka ka amshi wannan wannan zamu dinga gaisawa, ciro Layin yayi ya bashi ya amshi Na hannunshi, mukullin mota ya mik’omai tare da fad’in “tashi kuje Allah ya muku albarka ya sawa aurenku albarka,”
Da amin uncle Aminu ya amsa sannan suka tashi suka fita, bud’e wa Fatima motar yayi ta shiga sannan shima ya Shiga ya tada motar suka fice suka d’au hanya,

Bangaren mamy fiddausi kuwa tinda taji an d’aura auren zuciyarta ke tafarfasa gashi ba damar tayi fad’a ta b’atawa kanta taro Amman tabbas an rains mata hankali ita duk zatonta anbar maganar Ashe sunsan abinda suka shirya mata,? To kuwa tabbas anyanka ta tashi don kuwa a yau d’innan sai tasa faruoq ya saki ZAHRA ayau basai gobeba, gefe d’aya kuma JAMCY ta saka su agaba da kuka Wai ita dai faruoq takeso kuma inbata sameshiba saita kashe kanta, nanfa hankalin mahaifiyarta ya tashi najin abinda tace, mamy fiddausi ce ta dinga rarrashinta da cewa ta kwantar da hankalinta auren kanta zai dawo don ayau zai saki Zahra gobe kuma amaida Auren kanta, hakanne ya satayin shiru , saiidai har dare ya raba ba taga faruoq ya shigoba gashi sai Neman layinshi take a kashe gashi kuma daddyn ya shigo yace mata Indai ta taka bangaren husna da sunan cin mutunci to abakin aurenta,gaba d’aya bats hayyacinta har lokacinda aka watse aka tafi kai Aunty Jidda gidan mijinta bataga faruoq ba,

Su kuwa sai bayan magriba suka is a gidan baisha wahalar ganewaba kasancewar yasan wajen anan gidansu Amininshi Dr Ahmed yake, ita kuwa inbanda kuka ba abinda take tun tahowarsu har sukazo da kyar ya sami ya lallabata taje tai wanka tayo Alwala sukai sallahr magriba da isha,i sannan ya gabatar musu da abinda zasuci da ya taho musu dashi ahanya abaki ya dinga bata tin tanakin amsa harta d’anci,baki suka wanke sannan yace suyi Raka a biyu ta godiya ga Allah, bayan sun idar shi faruoq shirin kwanciya yai ita kuwa mik’ewa tai ta fara jero sallah ba adadi tun faruq Na kirga Raka ar da tayi harya fara manta lissafin donyanada tabbacin ita kanta batasan raka a nawa tayiba,murmushi yayi sannan yace aranshi” ko kwana zakiyi kina sallahr inanan inajiranki, don duk wayon amarya sai ansha romonta inji yan magana………………”
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
This page dedicated to lover’s of my book ❤️????????
thank you very much ????????????????????????????????

Page 80_85

**** Amarya Fatima Zahra tin tana sallahr da k’arfinta harta gaji kafafuwanta duk suka saki ta fara gyangyad’i a tsaye da kyar takai Raka ar don tana cikin sujjada bacci ya d’auketa ta b’ingire agurin daman a matuk’ar gajiye take kawai yau a tsorace take da ya yan nata shiyasa ta tsiri sallah r dole,saidai kuma bacci yazo ya sureta bata saniba,

Shikuwa ganin tayi bacci a hankali yazo ya d’auketa kamar wata baby SBD rashin k’iba yamaidata kan gadon sannan ya Zane mata hijab d’in ya gyara mata kwanciya shima kwanciyar yayi sannan ya ja musu blanket ya rufesu,

Asuba ta gari

Washe gari haka faruoq ya dinga tarayrayar amarshi da lallab’ata donji yake kamar ya maidata ciki don so haka ya dinga Sanya mata albarka da yi mata Alk’awarirrika da dama ranar haka ya wuni yana aikin rarrashi ita kuwa inbanda tab’ara da shagwaba ba abinda take zubamai,

Haka rayuwar maauratan taci gaba da gudana cikin far in ciki da k’aunar juna sosai suke tarayrayar junansu saidai damuwar Fatima d’aya rashin ganin mahaifiyarta kojin muryarta,

Ana haka Fatima ta sami ciki nanfa ya kara ninka kulawar da yake mata,a haka dai ta dinga rainin cikinta har ya isa haihuwa,tana fara nakuda ya kwasheta zuwa Asibiti don daman tunda cikinta ya tsufa ya daina fita ko nan da nan, suna zuwa kuwa kuwa ba dadewa ta haifo d’anta Na miji kyakykyawa mai kama da mahaifinshi, bayan sun dawo makotanta suka shishshigo yi mata barka don sun saba daman,
iyayen Dr Ahmed su suka dinga kula da zahran da jaririnta, ganin batada kowa a kusa, matar Dr Ahmed dinma kullum sai tazo wato minaksha don bai dad’e dayin aurenba Amman harsun saba sosai,

Ahaka ranar suna ta zagayo inda jaririn yaci sunan mahaifin Fatima AMINU Amman FU,AD ake kiranshi ‘yan uwan Dr Ahmed ne sukai komai tamkar sune danginta haka taro ya tashi lfy,
Faruoq ya kira daddynshi ya sanar dashi haihuwar aikuwa sai gashi sunzo sunga jariri shida uncle Aminu da tsohuwa mai ran k’arfe wato HAJIYA Jidda alokacinma da sanda take tafiya don ta tsufa sosai
Akodayaushe cikin godiyar Allah take da ya nuna mata yan jikokinta burinta ya cika ga kuma Auren su faruk din da take Alfahari dashi har gobe, Zahra ganin bataga anzo dasu momyn taba duk ta shiga damuwa daddyn ne yace ta kwantar da hankalinta in yaronsu yai wayo sai suje gidan haka ta hak’ura da zasu tafi suka ajiye mata kud’i da yawa da kayan barka sannan suka tafi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button