HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

A haka taci gaba da renon fuad saida yai wata 5 alokacin yai wayo sosai sannan suka fara shirin zuwa gida, a ranar Fatima cikin farin ciki ta tashi zataje tags momynta aikuwa da wuri suka shirya suka d’au hanya, shikuwa gabanshi fad’uwa kawai yakeyi don baisan wanne irin hukunci zaije ya tararba wajen mamyn shi Dan yasan shimai laifine agurinta, sai can wajen k’arfe uku suka isa gidan, bayan ya tsayar da motarne suka fito sannan suka nufi ciki, Bangaren Momy husna suka fara isa sun Tarar da ita zaune a parlor tana kallo, jin sallamane yasa ta waigo sosai ta fad’ad’a fara arta cike da Murna take musu sannu da zuwa ita kuwa Zahra da gudu taje ta rungume mahaifiyar tata tana murnar ganinta shikuwa gefe ya sami ya zauna yana gaisheda momyn tasu, fuska sake take amsawa, Amsar fuad tayi tana kallonshi cike da farn ciki da k’aunar yaron, sun d’an jima anan sannan suka nufi bangaren mamy fiddausi sallama Duke tayi Amman shiru ganin basu ganta a parlour ba ya sa faruoq ya nufi cikin bedroom don kiranta ita kuma Fatima a nan ta zauna kan kujera cike da zullumi, shiga d’akin yayi nan yai turus ganinta zaune a Bakin gado da alama ma taji shigowarsu, wata sallamar ya karayi a karo Na ba adadi wani mugun kallo ta d’ago ta watsamai sannan ta d’auke kanta, “ina yini mamy”? A fusace ta d’ago ta d’ora da fad’in,

” Wai kurma ka maidani ko kuma bebiya da kazo ka isheni da sallama da gaisuwa, yanzu daka kwaso wannan abar kazo ka ajiyemin ita a parlour me kuke buk’ata a gurina? Aini Tini Na cireka daga sahun ‘ya’yana tunda ni ban isa nace kayi Abu kayishiba, don haka kajecan Ku k’arata kaida ubannaka tunda shi yake saka bijirewa umarnina, don haka ka tashi ka ficemin a nan gurin ka kwashi waccen Abar da ka ajiyemin kayi gaba kuma kar in kara ganin k’afarka ta tako b’angarena,”

Kuka sosai faruoq ya fashe dashi najin maganganun da mahaifiyar tashi ke jifanshi dashi don ya lurama daf take da yimai baki, cikin tashin hankali yake magana,

” many Dan Allah kiyi hak’uri ki dena cewa kincireni daga yaranki,Ashe mamy duk tsawon lokacinnan a cikin fushinki nake?, yanzu da Na mutu a wannan yanayin mezanje incewa ubangijina, kinsan Cewar fushin uwa akan d’anta babbar musibace? Dan Allah mamy kid’au Auren nan a matsayin k’addara kisa mana Albarka,Dan Allah mamy,” Akace tsakanin d’a da uwa sai Allah, Jikintane kuma yai sanyi ganin yanda faruk din ke kuka, duk sai taji tausayinshi Amman duk da haka baza ta fa sa abinda tai niyyaba, don haka tace,

“Zan yafe maka Amman da sharad’in zaka yimin abinda Na umarceka,” da Sauri ya gyad’a kanshi alamar amincewa,
“Sharad’in nawa shine inason ka k’ara aure kuma Jamila nakeson ka aura ‘Yar gidan HAJIYA salamatu”, a gigice ya d’ago yana kallonta yana shirin magana ta dakatar dashi,
Umarni Na baka ban neni jin ta bakinkaba inkuma a yanzuma zaka bijirewa maganata to bissimilla, inason ayau kaje kaga yarinyar, kuma kasanarda mahaifinka aje a Neman maka aurenta, sannan banason sunana yya fito a maganar auren nan inason ka nuna musu Kaine kai ta ayin k’ara auren kuma wata d’aya za a sa gaba d’aya don baza kubar nanba sai tare da Amaryarka, ka tashi kaje in kayi abinda nace ka taimaki kanka inkuma kak’iyi to kasa aranka bakada wata uwa a duniya, tashi Kaje,”

Tashi faruoq yai ya fice daga d’akin yana had’a hanya harya fito inda Fatima ke zaune,ganin yanayinshine yasagabanta fad’uwa da Sauri ta zo ta rikeshi tana tambayar lfy? Rik’o hannunta kawai yayi suka fice daga part d’in a wani d’an corridor suka tsaya gaba d’aya ya zuba mata ido ya kasa magana, “ka sanardani meke faruwa Dan Allah ka tayarmin da hankali” fatiman ta f’ad’a,ajiyar zuciya ya sauke mai k’arfi sannan ya kwashe yadda sukai da mahaifiyarshi ya Samar da ita ba abinda ya b’oye mata shiru yayi yanajiran jin ta bakinta, ita kuwa wani irin kallo ta kemai da ya kasa gane ma anarshi………………..!
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

 

*_Z• W• F•????_*
Page 85_90

****** sosai shima ya zuba mata ido yana fargabar abinda zai fito daga Bakin ta, sunkuyar da kai tayi tadanyi murmushin da iya lebbanta ya tsaya sannan tace,

“Yanzu Abban fu’ad har kana tinanin zansa ka bijirewa umarnin mahaifiyarka? Yanzu kana tinanin zan iya hanaka yin aure? To inason kasani wallahi ko kai ka gani yarinyar kacemin zaka aura bazsn taba k’in amincewa ba saboda nasan ubangijine ya halarta muku yin hakan, bayan ni ma zaka iya auro 3 mu zama mu hud’u Dan haka har cikin rains na amince da k’arin aurenka,”
Tunda ta fara magana yake kallonta ganin tayi shiru yace, “yanzu kina nufin har ranki kin amince nayi aure? Bakya kishi nane ko me? Banga alamun damuwa a fuskarkiba kwata kwata,”

“Abban fuad kenan! Ka sani ina matukar k’aunarka kuma ina kishinka Amman kishina ni kishina irin na matan sahabbai nakeyi, kuma ka sani mu mata ba kishiya Mike tsoroba halinta muke gudu, akwai wacce zata shigo gidan badan Ku zauna lfy ba saidon ta fitarda ta ciki ita ta zauna ita kad’ai wata kuma ta rabaki da mijinki, to irin wannance bamaso, Amman indai ta kirkice tazo kishiya ai Yar uwace,ni yanzu fatana Allah yasa ta garice wacce zata zo mu had’u mu had’u mu faranta maka har mu sami Aljanna ta silarka,,,,,,,,,,,,,,,”

Hakadai ta dinga k’arfafamai gwiya tana rarrashinshi bayan ita ya dace a rarrasa a yanzu MACE TA GARI kenan, daganan bangaren Momy husna suka koma anan yake wa momyn bayani itama k,arfafamai gwiwa tayi sannan ya fita ya bar Fatima anan, kai tsaye wajen mamyn shi yaje yace tamai kwatancen gidan su yarinyar, cike da farin ciki tamai kwatancen, bayan fitarshi ta kira HAJIYA salamatu tace ga faruk nan zaizo gurin Jamila yanzunnan, ita ma cike da d’oki ta sanarda jamcy nanfa jamcy aka shiga rawar kai don daman kullum cikin zuba idon ganinshi take,nan aka shiga wanna aka zauna aka cab’a kwalliya sosai sannan akayi b’arin tirare ajiki aka sanya wasu matsatstsun kaya aka cokala d’auri ana jiran isowar saurayi, tana cikin gwsda irin tafiyar da zatayimai yaro ya shigo yace Wai ana kiranta,aikuwa ba wani Jan aji tare suka fice da yaron, tunda taganshi ta zubamai ido ta kasa d’auke idonta akanshi, “hye my sweat heat ykk,” da sauri ya d’ago jin muryarta daf da kunnenshi ido ya zaro yana fad’in ” daman kece wacce Mamy kesan na aura,”? Fari tayi da ido tana wani kwarkwasa” nice mana Ashe ka ganeni, to mu shiga daga mortar mana akwai ranafa anan sosai saimunfi jin dadin tattaunawar,”

“Allah ya kiyaye kishigarmin mota kallekifa wata k’azama dake ke yanzu inbadon k’addaraba kinga na miki kama da Wanda zaizo gurinki da sugar soyayya? To wallahi ki sani zanyi biyayyane kawai na aureki amma ki sani bazaki tab’a samun soyayya daga gurinaba saboda bakiyi kala da irin macen da danakesoba,ke inda kunya take ma baki Santaba, ji yadda kike kallon cikin idona kina min magana, abinda Zahra bata tabayi ba kenan duk soyayyar da mukai da ita abaya, kuma ki sani daga yau bazaki kara ganina a kofar gidannanba,sai an daura auren, gashinan kije kiyi duk abinda kikesonyi na bikin Amman karki sake ki saka dani na fada miki,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button