HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Kudi ya watsa mata sannan ya shiga mortar shi ya kuna ya bad’eta da k’ura yai tafiyarshiya nufi gida Dan magriba ta kusa, ita kuwa kudin ta kashe tai ciki zuciyarta cike da takaicin cin mutuncin dayai mata, saidai ita kadai tasan abinda zatayi don baza ta tabs yarda ta zama bora a gidanshiba,

Bayan shigarta gida nanta zauna suna tattauna yadda bikin zai kasance donkudin Suna da yawa sosai,
Shikuwa gaba d’aya ranshi ajagule yake,shi inyatuno tama ranshi baci yake ya rasa me mamynshi ta gani a wannan birsinsinan yarinyar takeson ya aureta shi tun ganin farko dayai mata a bays yaji bataimaiba,hakadai ya dinga tinane tinane harya iso gidan,ganin za a shiga sallahne yasa ya juya ya nufi masallaci, bayan ya dawo kai tsaye parlour n mahaifinshi ya nufa acan ya Tarar da uncle Aminu da Alana magana suke mai muhimmanci, guri ya sami ya zauna saida suka gama sannan ya gaidasu dukkansu sunji dadin zuwan nasu,bayan gaisuwarne, faruoq ya gyara zama sannan sannan ya sanardasu abinda ke tafe dashi, ido daddyn nashi ya zubamai jin abinda yake fad’a bai katseshiba harsaida ya gama sannan dadyn yace ” lallai sannunka da k’ok’ari kai yanzu bakaji nauyin zuwa Kace mana zakai wani aurenba? Yanzu fa ko shekara biyu ba ayi ßayin bikinkuba kuma kana ganindai har yanzu ba a daidai ta da mahaifiyarka akan wancen aurenba, mudai kasan bamuda wannan Auren auren don dukkanmu mata d’aya daya ne damu, don haka niban yarda da k’arin auren nanba,

“Haba yaya bai dace ka hanashi yin aureba, kasanfa mai d’aki shiyasan inda yakemai zuba kaga bamusan dalilinshi nasanyin aurenba, don haka Nina amince, babana a ina yarinyar take,?” Cikedajin nauyin uncle din nashi yaimai kwatance sannan ya dire kudin komai da za a buk’ata,sallama yai musu ya fita bayan uncle din ya sallameshi, hakance ta kasance uncle Aminu shiga shige gaba akayi komai na Neman auren don dady yace Shiva ruwanshi a auren kasancewar Vaasa da yawa ba ana saura sati d’aya bikin mamy ta kira faruoq akan yazo yakaisu suga gida, za a je Jere,aikwa harda AMARYAR akaje nanfa ta tibire ita d’akunan sama ta keso, nankuwa mamyn tace sai Fatima ta kwashe kayanta ta dawo k’asa ahaka bayadda zasuyi aka kwashe kayan Fatima daga sama akavdawo mata dasu kasa aka jera na jamcy, ranar d’aurin aurenma kin zuwa yai yai tafiyarshi aiki ko da ya fawoma dakin fatyma yai shigewarshi anan take sanar dashi ankawo amaryafa ya yafi wajenta, shikuma yace bazaijeba ganin ta matsamai da ya fita saiya tafi dakinshi, haka ya dingayi har ya cinye kwana 7 dinshi ya dawo uwargida ita kuwa bats taba sanin ba a dakin amarya yai kwana 7 dinshiba, Amarya jamcy kullum saita zuba idon ganin ango saitsji shiru har bacci ya dauketa, a was he gari mahaifiyarta tazo nan tasanar da ita tunda tazo gidan bai taba shigowa dakintaba, aikuwa cemata tayi bari taje ta dawo ba jimawa ta dawo Mata da wasu kullin magunguna da layoyin da zata binne, hakan kuwa tayi aikuwa aikin yayi don ranar girkinta ya shigo harya kwana adakin, tofa wannan shine mak’asudin fara tabarbarewar zaman Fatima da faruk don tindaganan jamcy ta fara shiga bokaye harsaida ta raba masoyan biyu ayanzu ko ganin Fatima bayasonyi kuma komai jamcy tace to shi za a yi,yanzu hatta girki Fatima keyi kullum maganar Rabon kwana kuma daman babu ita ahakanma jamcy sharri take kullamata wajen faruoq kuma ya yarda saboda kannashi ba a daidai yakeba yanzu, ana haka wata rana Fatima ta tashi ba lfy sakamakon yaye mihal da tayi don bayan bikinsu faruoq ta haifeta, ahakan ta lallaba take taje ta had a break fast din tajere tashige d’aki saidai ta.na tafiya jamcy tazo ta zugawa tea din gishiri sauranma ta zuba gishirin aikuwa dasukazo karin faruk yaji girkin haka, azuciye yavd’au flast din shayin ya nufi dakin Fatima yana kwallah mata kira ita kuwa Tini tai zurfi a tinani batajiba,shine har ya zuba mata wannan azababben marin, to wannan shine ainihin labarin wadannan maauratan,
mungama labari yanzu littafin zai saura,

Nannauyar ajiyar zuciya Fatima ta sauke bayan gama tino rayuwarsu ta bays da tayi, kallonta takai kan fuad da yaketa baccinshi har yanzu,,,,

INA BARAR ADDUOINKU KUSANI ADDUA ALLAH UBANGIJI YA BANI LAFIYA????????????????????

Pls comments
Wallahi dakyar nayi muku typing dinnnan????
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 91

***** Bayan farkawar fuad daga baccin dayai na wahala jikinshi ta tab’a anci sa a ba zazzav’in ya sauka, saidai gefen bakin dayake akumbure, tambayarshi tayi zaici abinci? Eh yace mata don haka ta fita ta shiga kitchen ta dafa musu indomie yadda zata ishesu, sannan ta juyo a babban flet ta d’auko musu ruwa ta dawo d’akin, tare sukaci suka k’oshi sannan suka sha magungunansu, kwanciya sukayi don dare yayi gashi kuma ba gama warwarewa sukaiba,

*** Abangaren jamcy kuwa gaba d’aya bacci ya gagareta batasan me ya dawo da Fatima gidanba ita ta Riga ta sake gida ya zama nata kwatsan su wani dawo suzo su takura mata?tabbas wannan karan dole ayita ta k’are, washe gari kuwa da sassafe tabar gidan,

Durk’ushe take gaban bokanta tana mai bayanin dawowar Fatima ta k’afa da fad’in,
” ni yanzu so nake ayi musu kurciya dukkansu su bazama duniya i nda bawanda zaiji ko labarinsu, kuma a rufe Bakin iyayen tayadda bazasu nemesuba,”

Tsubbace tsubbacenshi yayi sannan ya d’ago yana cewa, “bazai yiyuba abinda kikace saboda tayi tsarin jikinta sosai yanzu ma lek’o ki gani ” wata kwarya ya nuna mata da ruwan tsafi aciki, aikuwa saiga Fatima zaune akan dadduma tana ta raira karatun al,Qur’anic mai girma, komawa tayi ta zauna sannan tace ” to yanzu ya za a yi kenan boka? In wannan ya gagara to inason asa mata cutar kuturta k’uraje su fito mata su b’ata wannan fuskar tata ta yadda ko kallonta mutum tayi bazai iya had’iye yawuba, su kuma yaran a kwashesu akaisu can guri mai nisa a watsar dasu,”

Surk’ullen shi yayi sannan yace ” yarandai zamusa a kwashesu aje a ajiyesu awani guri Amman itace ba tabbas din muyi nasara akanta, Amman tunda kin Dade zamuyi aikin ammanfa tabbas inbaisametaba kanji zai dawo, kin amince ayi?”

“Eh na amince ainasan koyaushe nasara aguna take ba tayadda za ai nayi Abu ya dawo kaina,”
Cewa yai ta tashi taje za a yi abinda race kudi ta diremai sannan ta tashi ta tafi,

Acan d’aya bangaren kuma yau mamy fiddausi ce ta shirya zuwa gidan Aunty jidda Dan kwananan tana yawan mafarkinta daga nan kuma ta wuve gidan faruk don rabonta dashi Harta manta gashi ko eayarma yanzu baya bugo mata kuma kota kira bata samunshi don haka zataje taga ko lafiya,? Gidan Jidda ta fara zuwa saidai tayi turus ganin jiddan a harabar gidan tanata tik’ar wanki gaba daya tai bak”i ta rame duk ta sauya kamanni sai uban ciki tirtsitsi agaba sai nishi takeyi Amman ahaka take wankin,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button