HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

” Jiddah! Me zangani haka? Cuta k
Ikayi ko me dakika lalace haka?”

Ita gaba d’ayama bataji shigowar mahaifiyarta taba sai maganarta waive waige ta farayi kar HAJJO tajiyo, “Dan Allah mamy zo mushiga daga ciki,”

“Ba zan shigaba inashi mijin naki daman wahala ya ke baki a gidan? Shi kuma wannan wankin na uban waye kikeyi,?”

“Mamy na HAJJO ne mahaifiyarshi nake d’an taimaka mata na kusa gamawa ma Amman Dan Allah kiyi shiru mamy kartajiyoki,” k’arar takalmi sukajiyo a ba yansu wata dattijiwace ta iso wajen tana fad’in
” Wai tsayuwar me kikeyine da har yanzu baki gama wankinba bayan kuma kinsan rana tayi lokacin cin abincina ya kusa Amman kin tsaya nawa balle kije ki d’auramin,,,,,,,,,,”

“Amman dai matarnan baki da imani kina kallon yarinyar nafama da kanta kika bata wannan wankin? To bazatayiba kuma ba abinda zata kuma yi miki aiba baiwa na kawo mukuba,ke Jidda shiga ki d’auko mayafinki mu tafi”,
Nanfa abin ya zamar musu kamar fad’a don dukkansu ba hak’uri ga k’arin takaicin mamyn tayi tayi jiddan ta taho su tafi Amman fir tak’i binta Wai ita dai yanason mijinta kar a kashe mata aure, tamkar ta rufeta da duka haka taji ganin taki binta saima wankin data cigaba dayi,a k’ufule race ” saiki zauna wahala ta kasheki Dan ubanki inkikaji wuya da kanji zaki dawo ai ke ‘yar d’ad’i mijiko,?” Fita tayi daga gidan cike dajin haushin jiddan, Hartaisa unguwarsu faruoq d’in ranta a b’ace yake, Bayan isarta gidan ta dad’e atsaye tana knocking sannan jamcy tazo ta bud’e, ido hud’u sukayi Amman ta koma taci gaba da abinda takeyi ko kallo mamyn bata ishetaba duk da ranta yad’an sosu Amman saita daure tace “Jamila baki baki ganniba naga ko gaisheni bakiyiba ko baki ganenibane?
Ba tare data d’agoba tace na ganki mana naga har ido muka had’a dake nagane ki mana ba hajiya fiddausi bace,” dummmmm! Gaban mamyn ya buga,

“Jamila nice kike f’ad’ar sunana gatsal haka? Yaushe raini ya shiga tsakanina fake kokin manta mahaifiyar faruoq CE agabanki?”

“To mene Dan na fad’i sunanki nagadai Dan a fad’a aka rad’a,” sosai ta cika da mamakin jamila ayau don bata tab’a zaton hakan daga garetaba, “yanzu ina faruk d’in yake Donni gurinshi nazo ba Mara mutunci irinkiba,”

“Yana sama yanamin gyaran d’aki saidai ki jira don naji kamar toilet yake wankewa,”

Azabure ta mik’e tana fad’in………………!

COMMENT AND SHARE PLS

AM SICK????
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
page 92

“Kikace yanacan yana miki gyaran d’aki? Ke kuma mene amfanin ki a gidan me kika maidashi d’an aikinki ko me?” Jin alamar saukowa daga benen yasata d’agowa faruk ta gani yana saukowa shima gaba d’aya ya lallace sai uwar k’asumba data cikamai fuska ga wata suma da ta dank’are akan nashi da alama ko taza ba ta samu? Faruk da gaske kaikayi mata gyaran d’akin?

Maimakon ya bata amsa sai cewa yayi

“sannu da zuwa many”
“Nibashi nakeson jiba tukunna ma me ya hanaka zuwa gida tsawon wannan lokacin? Kuma meya sami wayarka daka dena nemana kuma kullum a kashe?”

Inda inda yafarayi ya rasa ma mezaice donshima baisan daliliba, kallonta ta maidani kan jamcy don gaba d’aya ta d’ora alamomin tambayarta akanta,

“Me kikayiwa yarona ya lalace haka akanki nace mai kikayimai ina tambayarki,” kallon sama da k’asa taiwa mamyn sannan taja tsaki,

“Aigaki kashinan ki tambayeshi mana,”
Azuciye ta kawo mata mari Dan taji haushin tsakin data I mata,saidai taji anrik’e mata hannu ta baya, faruoq ne ” Dan Allah mamy karki tab’a my jamcy gwara Niki mareni zanfi jurewa akan ki tab’ata,”

“Aida ka kyaleta ta tab’ani da wallahi kina sauke hannunki zan d’ora mini nawa don bazaki daki banzaba, kaga kasa matarnan tabar gidan nan yanzu don hayaniyarta ya fara hawamin kai,”

Kafin mamyn tayi wani Abu saiji tayi faruoq d’in na fad’in

“Many ki tafi Dan Allah kuma karki sake zuwa tunda kinga batason zuwanki kije Dan Allah inkina buk’atar wani Abu zanzo Amman yanzu dai ki tafi Dan Allah,”
Magana take sonyi Amman tasan tanayi kukan dayaci k’arfinta zai kufce mata, tabbas bata tab’a zaton haka jamilan takeba da bats had’ata da d’antaba gashinan tun yanzu ta fara Dana Sanin had’a auren juyawa tayi ta fice saga gidan zuciyarta na tukukin bak’in ciki,ada gida tai niyyar yi saidai ta juya akalarta zuwa gidan su jamilan, tin daga Bakin get take k’arewa gidan kallonta cike da mamakin yadda aka gyara gidan mamakintane ya k’aru ganin yadda HAJIYA salamatun ta zama hamshak’iya ko zama batayiba ta fara fad’a ” eh lallai duniya sabuwa dole adena Neman mutane wato keda yarki kun tatikemin d’a kuna fantamawa yadda kukeso, tukunnama kina sane da yadda jamila ta mallakemin d’a take juyashi son ranta? To wallahi kiyi mata magana tun wuri ta je ta karya abinda tamai inba hakaba da kaina zan raba auren dan saiya saketa daman Nina had’asu,”

“Indai kina ganin zaku iya sawa ya saketa to bisdimillah, ke yanzu inba fitinaba meya kaiki gidan yara? Ko da yake daman Ku iyayen miji daga kunga ana zaman lafiya saikuce an mallakemuku d’a,ke ba asirce naki mijin kikayiba gashinan ke kadaice matarshi har yanzu duk da iskancin da kikemai,? Nandanan suka kacame da cacar baki aikuwa baram baram suka rabu kamar ba wad’annan Aminanba????

Aikuwa bayan komawarta gida sosai tai kukan abin tabbas tayi nadamar had’a wannan auren gashi ta rasa ta rasa Wanda zata fad’awa taji zanyi aranta,tunda ta kwanta take juye juye abubuwan da suka faru a yaud’inne suke ta dawo mata d’aya bayan d’aya shima daddyn ya lura tana cikin damuwa Amman ganin bata Samar dashiba saiya kyaleta,

******A can d’aya b’angaren kuwa Fatima ce ta wayi gari cikin tashin hankali na rashin ganin yaranta kuma tacuba ko ina acikin gidan Amman bata gansuba, saman tahalu donta sanarda faruoq saidai jamcy CE ta lek’o kuma tace bacci yake ba za a tasheshiba taje ta nemesu ita kad’ai saukowa tayi ta nufiv wajen baba maigadi, bayan ya bud’e ta tambayeshi koyaga su fuad? Nan ya Sanar da ita shi tunda ya rufe get bayan fitar mamy bai k’ara budewa ba kuma ba Wanda ya fitacdaga ciki, cike da mamaki take tambayarshi daman mamy tazo gidan? Nan ya Sanar da ita tazo, juyawa tayi ta nufi cikin gidan saidai kicib’is sukayi da jamcy da ta fito itama da alama bata cikin hayyacinta don wasu irin manya manyan bakaken k’urajene suka feso mata ajikinta tun cikin dare, agigice ta shiga motarta ta fice daga gidan da wani mugun gudu,

Itama Fatima ciki ta shiga ta d’auko mayafinta ta fice,

taci tafiya sosai kafin ta isa gidan kasancewar akwai nisa tsakaninsu, Dr Ahmed d’inne yazo ya bud’e mata sosai yai mamakin ganinta a wannan lokacin,

” Fatima meya faru daga ina kike da sassafennan,”? kuka ta fashe dashi sannan tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button