BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 11 to 20

“Ke da akace min baki da lafiya kuma shine kike Son yin min ƙarya?”
Batasan sanda tasaki murmushi ba cike da tsananin farin cikin da yakusa kashe ta tace
“Ai naji sauƙi, dama zazzaɓi ne”.
Taɓe baki yayi sai kuma yagyaɗa kan sa, still kuma yace
“Ai naga alama tunda gashi kina min dariya”.
Kamar yana ganin ta tayi saurin rufe bakin ta tana faɗin
“Wlh ba da kai nake yi ba”.
“To da wa kike?” Yatambaye ta yana wani rage murya
Bilkisu ta kasa magana fa, sai kace ba abinda take nema bane yasamu amma kun ji tayi gumm kamar munafuka
“Kin yi shiru kuma? Ko bazaki faɗa min ba?”
“Uhm babu kowa”.
“Ok dama nakira naji jikin ki ne, tunda kin sami sauƙi naji daɗi, bye”.
Be jira cewar ta ba yakatse wayan.
Ita kam Bilkisu tana jin yakashe kiran sai tawani kurma ihu tana burgima saman gadon ta, Allah yasa ita kaɗai ce a gidan da har waje sai an ji
“Wayyo Allana yau daɗi zai kashe Ni, wai Ib ne yakira ni? Wayyo ko dai mafarki nake yi?”
Sai tamiƙe daga kwancen da take tana rarumar wayar ta taduba, washe baki tayi ganin dai ba mafarki bane, kwanciya takuma yi tana rarumo pilow tamatse tana cewa
“Wayyo daɗi kashe ni, wayyo ni Billy yau duniyar ta kai min inda nake so, gaskiya yau na kasance me Sa’a, wayyo Allana Wayyo Allana wa zai taya ni farin ciki?”
_(Ni kam nace *NAFEESA GROUP FAN’S* su taya ki, ko kuma *BRR. IBRAHIM KHALIL FAN’S* don Ni dai ban da lokacin ki lol???? ????????)_
Shi kuma da gama wayan miƙe wa yayi yaɗau rigan sa yasaka kafin yashige ɗaki, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, bayan ya idar da sallah yafito yakamo hanya, gab da yakusa isa gidan sa yahango Kausar tafito daga gida, tana sanye ne cikin wata Farar riga me dogon hannu zuwa cinyan ta, sai wani burgujejen wando Three qweater me manyan aljihu kalan Orange ????, sai tasanya hula facing cap shima kalan wandon, kitson da tayi guda biyu jelan tazubo shi gefe da gefen kafaɗan ta, tunda itama tahango shi tanufo shi da murmushi a fuskar ta, tana iso wa wajen sa tace
“Yanzu nake tunanin ka a raina sai ga ka”.
Yanda tayi maganar ne yasaka shi ɗan murmusawa yace
“Zaki bani wani abu ne?”
Sai ta langaɓar da kan ta tace
“Eh in dai kana so”.
“Why not?” Yafaɗa yana waro idanun sa
Sai tayi murmushi kana tace
“Dama ina so muhaɗu ne kawai, coz akwai tambayan da zan maka”.
Be ce mata komi ba sai dai ƙure ta da idanu da yayi, yana jiran abinda zatace
“An bani labarin kuna Shari’a da wani Alhaji Mubarak mai kuɗi, and nan da five days zaku koma Court, shine zan iya zuwa muyi hira akai, ina nufin ina son nasan komai”. Taƙarike maganar tana ɗan kwantar da murya tare da ƙifƙifta idanu
Shiru yayi still har yanzu idanun sa akan ta, sai tasake cewa
“Please kaji?”
“Ok”. Yafaɗa ataƙaice yana ɗage kafaɗa
“Tom gidan ka zamu je yanzu ko?” tayi maganar cike da zumuɗi
“No kibari zuwa gobe sai kizo”.
Daga haka yayi gaba, ita kuma tatsaya nan tana kallon shi har yashige, sai tasaki murmushi tanufi wajen gidan su tatsaya, dama abinda yafito da ita kenan shan iska, a cewar ta gidan yayi mata zafi, tana nan tsaye tana kallon tsare-tsaren gidajen mutane tana tunane-tunanen ta, wayan ta yasoma ringing, cirowa tayi cikin aljuhu takalli fuskar wayan, sunan HONEY ne yafito ɓaro-ɓaro hakan yasaka tasaki murmushi tana amsa call ɗin, tajuya tashige gida.
…….. ……….. ……….
Washe gari wajen ƙarfe 03:30pm. Kausar tashigo gidan Khalil, yau tana sanye cikin wata doguwar riga ce mare nauyi red colour, sai ɗankwalin shi da tayafa akan ta kawai, tansaya Hill shoes a ƙafafun ta, tana riƙe da wayan ta iPad fara, nocking tasoma yi amma shiru, hakan yasaka taci gaba da yi babu ƙauƙautawa, tafi minti goma a wajen tana nocking, sosai tagaji but kuma taƙi tafiya
A ciki kuwa tun da yadawo aiki yakwanta barci, sama-sama yake jiyo nocking ɗin daga ɗakin sa, ahankali yabuɗe idanun sa yana sake jiyo nocking ɗin, tsaki yaja yatashi zaune yana miƙa, sai da yafi 3min a zaune kafin yamiƙe yafito daga shi sai baƙar singlate ajikin sa, da gajeren wando yellow, ƙofan yabuɗe suka haɗa ido da ita, dasauri tasad da kai ƙasa tana jin matsananciyar kunya, cikin sanyin murya tace
“Sorry ban san kana barci bane, bari in koma zan dawo”.
“Kishigo”. Abinda yafaɗa kenan yajuya yashige ɗakin sa
Sai da taji ƙaran rufe ƙofa tukun taɗago kan ta, leƙawa tasoma yi kafin tashiga, saɗaf-sadaf haka take tafiya kamar wata munafuka, har ta’isa kan kujera tazauna tana kallon parlour’n, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, har yaso yafi nasu duk da su ma nasu yana da kyau, but wannan komi kakalla kasan ba ƙaramin abu me tsada bane, sosai aka kashe kuɗi cikin parlour’n duk da ba wani kaya ne a ciki ba, tana nan tana kalle-kallen ta kamar wacce bata taɓa ganin irin sa ba, yafito sanye da riga me ruwan zuma da zane-zanen fari ajiki, sai wando Three qweater fari, ƙariso wa yayi yazauna a kujeran dake facing ɗin ta yana kallon ta, ɗago kai tayi itama tana kallon shi tace
“Ina yini?”
“Lafiya”. Ya’amsa ataƙaice yana jingina bayan sa da kujera yalumshe idanu
Ita kuma sai tatsaya tana kallon shi cike da burgewa, komi nasa me kyau ne, yana da matuƙar kyau da kwarjini, babu macen da zata gan shi batayi fatan samun shi ba, buɗe idanun sa yayi yasauke a kan ta, sai tawayan ce takau da kai
Yace “me zaki sha?”
Sai tamaida idanun ta kan sa, kamar bashi yayi maganan ba
“I’m ok”. Tace dashi tana mayar da idanun ta kan wayan ta da taɗaura saman jikinta, tasoma latsawa kana tace
“Ko zamu iya farawa?”
“Ok”.
Daga nan yasoma bata bayani akan komi, har zuwa sanda suka gama yamiƙe yanufi hanyan kichen, wata iriyan yunwa yake ji, komi be saka a cikin sa ba tun tea ɗin safe, kuma da yadawo barci sosai yarufe masa idanu sakamakon jiya be yi ishashshe ba
Yana tsaye cikin kichen ɗin yana ƙoƙarin ɗaura tukunya, yaji muryan ta a bayan sa
“Me zaka dafa?”
Juyowa yayi yana kallon ta, don be tsammaci zuwan ta ba, murmushi tayi masa tatako ta’iso wajen sa tana faɗin
“Kaje sai in yi maka girkin”.
Tayi maganar tana ɗaura hannun ta saman tukunyan tana gyara mishi zama
Babu musu kuwa yajuya yatafi, be san meyasaka yarinyan take son shige masa ba, but ko kaɗan ba ta bashi haushi sai burge shi da take yi, yana nan zaune a Parlour yana kallo har tagama tazubo mishi, a gaban shi ta ajiye saman Centre table tace
“Bismillah ko”. Tayi maganar tana kallon sa da murmushi a face ɗin ta
Shima kallon ta yayi sai yakalli abincin, taliya ne me manygaɗa da yaji cUrry da yankakken ƙwai a sama, murmushi yasaki yace
“Thank you, kema ki zubo naki kici”.
Yarfe hannun ta tayi tace
“No ni na ƙoshi, ina sauri akwai inda zan je”.
Gyaɗa mata kai kawai yayi, sai tajuya tatafi shi kuma yabi ta da kallo, sai da takai bakin ƙofa tajuyo tana kallon sa taɗaga masa hannu sannan tafice.
[9/23/2020, 7:28 AM] نفيسة أم طاهرة: ????️????️????️????️????️????️????️????️????️????️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma’il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*????
*F.W.A????/*
“`ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH“`
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al’umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN ???? ya Allah._