NOVELSUncategorized

KWARATA 86

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}

                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ ????????


*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

                         &

*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*



???? —— 84


    
       Kiran Ashiru ne ya shigo a wayarshi saida ya sake shafo fuskar Sultana ya ɗauki wayar tare da cewa ku shigo na gama , shigowa sukayi tayi dan duk wani yaron Dikko ya samu damar isowa a asibitin ɗakin baya anshe su , kallon Sultana Dikko yayi sannan ya kallesu yana cewa ku ɗan rage ina fitowa babu jimawa ya ƙarasa maganar yana kallon ƙannenshi yace ku kuma ku tafi gida kunji ngode , 

       Yaya ai zamu kwana a nan ne inji Dady munyi waya dashi , murmushi Dikko yayi kaɗan tare da tsareta da ido irin kallon nan na rage gulof yace Dadyn yace ku kwana ? Ah Yaya ta daburce , ɗaure fuska yayi tare da cewa ku wuce ku tafi zanzo gidan anjima kunji ya ƙarasa maganar cikin sanyi.

    Tou Yaya kuzo mu tafi tana jan “yan uwanta cikin rashin jin daɗi , har zasu fita Dikko yaga kamar babu daɗi yace Ni’ima zo ita ya kira dan itace babba a cikinsu , dawowa tayi ta tsaya gabanshi tana cewa gani kanta yana kallon ƙasa , me ne ne ? Kinji kamar ban kyauta ba ko ? A , a , Yaya , kun tabbata ? Ya ƙarasa yana kallon inda sauran suke tsaye , gaba ɗayansu suka ansa mun tabbata Yaya , yawwa to ngode ku huta gajiya , yawwa suka faɗa suna Allah ya bata lafiya…..

        Momy kuwa bayan Dikko ya ɗauki wayoyinshi ya fita itama bin bayanshi tayi ita da zugar ɗiyanta wai tunda har akan Dikko Dady ya faɗa mata magana ta bar mishi shi kuma kada wanda ya buga mishi waya ya jajanta mishi yayi rashin lafiya sai Dikko ya gane bashi da wayau su mata ne kuma suna da yawa su haɗe mishi kai idan har suka bari ya rinjayesu zasu sha wahalarshi karsu sake zuwa gidanshi kowa yaje yayi rayuwarshi , idan yaji ya takura zai kira Dady ya faɗa mishi a lokacin ita kuma zata faɗawa Dady magana ,

        Yazeed kuwa tunda ya tura hoto bugun zuciyar yaci gaba da halbawa ga abokinshi da aka kama wanda yayi ma Dikko magana ya fito dashi zasu shiga kotu , kuma ya daɗe da tura hoto baya goguwa kuma Dikko kaɗai ya isa ya tsaya mishi , matsala ta taho lallai haɗuwarshi da Dikko ba daɗi amma addu’arshi ɗaya Allah yasa Dikko ya saki Sultana…..

     Matar Dady kuwa ta shiga ta tsaya tsaff a cikin yinin ranar yau tasa Al ‘ Ameen ya samo mata lambar wayar Maman Sultana har gidan Kaka yaje ya samota da kanshi , bayan ya kawo mata ta rangaɗa mata kira babu daɗewa Inna ta ɗauka suka gaisa ta gabatar da kanta da cewa ita matar gwamnan katsina ce , Inna tace sai akayi ya kuma ? Dan ita a tunaninta Maman DK ce , ita kuma taci gaba da rattafa mata cewa Dikko ya jefo mata “ya daga saman benen kanta ya daki ƙasa saboda shi ya riga gangar jikinta zuwa ƙasa ta daku sosai idan ta yadda ta ɗauke “yarta kafin ya kashe ta dama tana ta shan wahalar dangin miji tsangwamar kishiya masifar miji ga duka ga zagi ga gori abundai ba kyan gani , bayan ta gama faɗar duk buƙatunta Inna tace tou ngode sosai amma ni bana tare ma Sultana faɗa a gidan aure kuma duk abinda mijinta zai mata ni bai shafeni ba ai ina sane da ita tunda nasan na haifeta , na barta ta gurzu da rayuwa dan dani da ita ba’a san gawar farko ba ta koyi rayuwa ta koyi riƙe damuwa haƙuri da rayuwa dan idan nice yau bani ce gobe ba dan nima kin ganni nan nima nabi mijina dan shine gatana kuma marufar asiri na , Sultana yanzu tabar ƙarƙashin iyayenta ta koma ƙarƙashin aure banda iko da ita kuma ita ba yarinya bace idan taji ta matsu tana da ƙafafuwa ta gudu , Allah ya bata lafiya……. Tana faɗin haka ta tsinke kiranta…. Hmmmm Inna kenan manyan duniya…

       Bayan awanni biyu da wasu “yan mintuna Sultana ta dawo , kamar mahaukaciya haka ta riƙa kallo tana motsa kanta kaɗan² tana kallo wurare , Ashiru yace sannu Hajiya , binshi tayi da ido ta kwalalo su sosai , Dikko dake zaune saman abin sallah ya tashi yaje wurinta An mata sannu , shima kallo tabishi dashi duk kamar dai mutane baƙi ne a wurinta sai kace wata sakara ,

       Murmushi Dikko yayi tare da duƙawa kusa da ita yace sannu An mata , bata iya magana kwata² ta riƙe wuri ɗaya da ido tana kallo , ke me ne ne ? Baki ganni ba ? Ashiru yace mai gida ai sai a hankali zata ganeka , ƙarya ne ta ganeni mana ke ba kin gane ni ba ? Yayi maganar yana juyo kanta ta yadda kallonta zai dawo wurinshi ,

        Kallo ɗaya tayi ma Dikko ta juyar da kanta gefe hawaye yana fita daga idonta , murmushi Dikko ya sakeyi tare da cewa bana faɗa maka ta gane ni ba , ɗan taɓe baki yayi yana cewa haushi na akeji baiwar Allah An mata ai koni saina baki shawara kiji haushin Dikko nima kaina haushin kaina nakeji , Ashiru jeka waje , Allah ya taimaki mai gida ya faɗa tare da fita daga ɗakin ,

      Gefen gadon ya zauna yace An mata kiyi haƙuri don Allah na bari bazan ƙaraba ki gafarceni na yadda ni mahaukaci ne ya ƙarasa maganar hawaye yana fita daga idonshi , girgiza kai tayi dan bata iya magana , kinyi haƙuri ko ? Da kanta ta nuna a , a , haba An matana nasan kinyi haƙuri kuma bakiji fushi ba ke mai yafiya ce a gareni ki ƙara yafemin kinji An matana….. Ya ƙarasa magannar cikin yanayin neman gafara….

     A , a , ta sake nunawa , hannunshi yasa saman idonta ya shafa ta rufe idon yace haba ƙaramar yarinya yau kuma Dikkon ake ma haka ? Abokin faɗan naki ? Kinyi min adalci kenan An mata ? Kiyi haƙuri mana nayi miki alƙawari bazan sake ba dan Allah ya riƙo hannun ta ɗaya ya soka “yan yatsunshi a ciki ya juyar da bayan hannun nata ya ɗora dai² saitin zuciyarshi ya danne da ɗayan hannun nashi yace kinji yadda zuciyata ke halbawa itama haƙuri take baki kiyi haƙuri An mata badan halin Dikko ba dan Allah ki rufamin asiri ki yafemin , karki yadda wani ya gano kinajin haushi na a gaban idon mutane ki nuna babu wani damuwa na yadda idan mun koma gida duk abinda kika ga dama kiyimin na yadda amma dan girman Allah idan kinga mutane ki riƙa sakin ranki karki wani haɗe rai kinji ko…….. ? Shiru tayi batayi magana , kalli ya nuna mata idonshi jifa Dikko yana kuka ke bakyajin ƙunya ina miki kuka “yar yarinya ya ƙarasa yana murmushin ƙarfin hali , kallonshi takeyi har yanzu ba magana , hannunta yasa ya shafa gemunshi tare da ɗaga mata gira yace na bari matar Dikko ya faɗa da wani irin yanayi , duba wayarshi yayi da saƙo ya shigo , ɗaure fuska yayi ya goge hawayen tare da kama kanshi wai likitoci zasu shigo inji Ashiru ya turo mishi a waya , shima ya maida da to….

    Hada Ashiru suka shigo , gaisawa sukayi da Dikko suna mishi yamai jiki , alhamdulillah daga haka bai sake magana saidai idan sunyi magana Ashiru yayi magana , bayan sun gama ɗaukar BP { blood pressure } nomal kamar yadda sukace aka wuce da ita C T Scan { Computered  Tumography }. Dikko dai baije ba sai Ashiru da sauran tawagar suka bi bayan a can sun gama abinda sukeyi suka buƙaci sa hannun Dikko ya sa ya tafi ansa kiran Dady bayan ya gama sa musu hannun zai dawo kafin su gama abinda sukeyi.

     Dady yayi ma Dikko faɗa sosai akan me yasa ya jefo ɗiyar mutane daga sama ko yayi hauka ne ? Waye yace masa ana dukan mace ma tun farko kenan ? Shi me yasa yakeyin abu kamar ƙaramin yaro wai ? Haƙuri yaba Dady shi bafa shine ya jefota ba faɗa yayi mata kawai saita firgita , Dady yace tou waye yace ana firgita mace ? Me na faɗa maka akan mace tun auren ka da Sadiyya ? Tunda baka san ta ka sawaƙe mata ta kama gabanta kafin ka jawomin tashin hankali , Dady ba haka bane , tare shi Dady yayi cewa ka rufe min baki ya faɗa cikin faɗa yana ci gaba da cewa ka saki yarinyar nan , haba Da…. , cikin hayani Dady yace bana san maganarka ka bani takaddar sakinta har sai yaushe zan huta da halinka Babana…….? Hawaye ya zubo daga idon Dikko yace Dady ni banayin saki , sai kayishi Babana sai ka saki yarinyar nan bazan bari ka kashe yarinyar mutane ba , yanzu da , da tsautsayi shi kenan maganar nan bazai rufe ba yana can yana zagawa a gari ka kashe matarka , dama na Sadiyya har yanzu surutu bai tsaya ba akan ka tsafe yarinyar mutane banda hauka kuma zakaje da gangan ka jefo yarinyar mutane kai sarkin zuciya itama ta mutu ka zama matsafin kenan ko…………….?

      Shiru Dikko yayi kanshi yana kallon ƙasa lokaci bayan lokaci yana buɗe bakinshi kaɗan yana jan iska cikin ɓacin rai , Dady kuma ganin Dikko yana kuka yasa ya sassauta maganarshi yana cewa ni ne kaɗai na isa na faɗa maka gaskiya komin rashin daɗinta bana san abinda kake yi kaji ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi , kallon Dady Dikko yayi sannan yace kaima mahaukaci kake cemin ko Dady ? Baban naka ne mahaukaci ko ? Ya faɗa yana ɗora kanshi a kafaɗar Dady yana kuka , tunda kacemin mahaukaci kowa ma zaice ni mahauka ci ne.

      Bakajin magana Babana nace bana san halin nan bazaka bari ba ya kake so inyi ? Kayi haƙuri Dady na bari bazan sake firgita ta ba , idan na sake ji kuma fa ? Sai kayi min faɗa ya ƙarasa yana kallon idon mahaifinshi cikin soyayya , murmushi Dady yayi shima Dikkon murmushi yayi tare da rumgume Dady yana dariya…….. Aka daina zancen saki.

      Daga wurin Dady wurin Momy ya wuce duk sallamar da yayi bata ansa ba daga ita har “yan uwanshi kuma babu wanda ya kalleshi , Rabiya sai haɗe rai takeyi tana hararar bango , cikin rashin jin daɗi Dikko yace Momy meya faru ? Fuuuu ta tashi tayi ciki suma suka tashi suka bi bayanta , cikin yanayin damuwa Dikko yabi bayanta tana zaune a gefen gado sai ɓata rai take , wurinta yaje ya duƙa gabanta ya riƙe hannunta cikin lallashi yace baki lafiya ? Cikin faɗa tace lafiyata qalau , tou me yayi zafi haka ? Ya faɗa yana tsareta da ido , ban sani ba tunda kaje ka haɗani da ubanka kai ɗan zinari , me nace masa Momy ? Kace masa ni bana sanka , Rabiya tace Momy ji har kin manta kina masa magana shi yasa yake iskancin daya ga dama , cikin ɓacin rai ya leƙa ta gefen Momy inda Rabiya take zaune yace ki fita hanyata kafin in kwantar dake , Momy tace kwantar da ita Iliya ɗan mai ƙarfi , ƙannenshi ya kalla tare da cewa da Allah ku fita kuba mutane wuri , tashi sukayi suka fita wurin ya rage daga Dikko sai Momy sai yayyenshi , Rabiya tace to ka kwantar dani mara kunya , bai kalleta ba yace Momy me nayi miki ? Dikkon ne mai laifi a wurinki ? Haba Mamana waye zai haɗani dake ? Cikin sansanyar murya tace Dadynku ne yayi min wulaƙanci a gaban kishiya abin baimin daɗi ba , Rabiya tace ki kyale shi Momy ai duk shine munafukin , dunƙule hannunshi yayi tare dakai zamiya taja baya da sauri yace zan…… Riƙeshi Momy tayi tace ya isa ta faɗa tare da miƙewa taja hannunshi suka fita waje ,

      Wurin motarshi suka tsaya tana masa magana wai yanzu ya daina santa a gaban idonshi ake mata iskanci a gidan nan yana kallo bayayin komai , yace Momy tou yanzu kuma me akayi miki wanda nayi shiru ? Ɗan ɓata rai tayi cikin rashin san zaman lafiya tace yanzu ba a gabanshi Bilki taje take faffaɗa mata maganganu marasa daɗi ba shine yayi shiru { abiyar zamanta } Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri babu yadda za’ayi ta faɗa miki maganganu kedai ki bari a zauna lafiya , sai kice anyi miki laifi kullum inyi ta hauka har an fara cemin mahaukaci , tou Dikko ƙarya nakeyi ta juya zata koma ciki da ɓacin rai tana gunguni , da sauri yasha gabanta yace shikenan zan mata magana , dariya tayi irin ta ƙasaitaccin mata , duƙawa Dikko yayi ta dafa kanshi tana cewa Allah yayi maka albarka , amin ya faɗa ta koma cikin ɗaki ,

     A gajiye ya koma mota ya kifa fuskarshi a saman sitiyari shidai baisan abinda yasa gidansu akeyin bahaggon zama ba , sai zafin kishi da nuna “yan ubanci “yan wancan ɗakin basa san “yan wancan ɗakin , kowa ɗan ɗakinsu ya sani kuma shi yake so , sai kuma wani babban shirme idan ana faɗan kishi sai kowa ya shigar ma mahaifiyarshi wai me yasa mata sukeyin haka ? Shifa a tunaninshi matar uba uwa ce , ita kuma “ya “yan mijinta kamar itace ta haifa , gaskiya gaba ɗaya babu kyautawa su kuma wanda iyayensu basa gidan an ɗauki masifar duniya an ɗora akansu ga masifar aiki ga aike² kamar ba “ya “yan Dady ba sunayin wata irin rayuwa kamar “yan aiki kuma a hanasu ganin Dady saidai shi idan yana nan yake musu jagoranci zuwa wurin Dadyn , kuma shima Dadyn ya kamata idan baya nan ya dawo yaga kowa suma ya nemesu tunda ai yasan ya haife su , haka ya siyama kowa sabuwar mota amma duk wanda babu uwarshi a gidan babu rabonta , dole shine ya siya musu motocin da suke hawa Momy kuwa tace ina wuta ta jefa Dikko tayi tashin hankali saida aka kai ruwa rana suke hawan motoci , su Momy basa tunanin idan Dady ya sakesu ko suka mutu suka bar nasu “ya “ya wace irin rayuwa zasuyi ? Ya kamata a riƙa adalci a rayuwar “ya “yan da basa tare da iyayensu a gidan miji dan babu wanda yasan abinda gobe zatayi haka kuma babu wanda yasan maci tuwo sai miya ta ƙare , shi kuma yayi bakin ƙoƙarinshi wurin ganin Momy ta jawo yaran jikinta tana basu kulawa tarbiyya da tsaro kamar yadda take ba nata “ya “yan amma tace sam bata ƙaunar ɗan kishiya , tsoki yayi a dai² lokacin da text in Umar ya shigo Al ‘ Ameen ya shiga gidan gwamnati yanzu , dan yadda yasa aka sakawa duk wani motsin Sultana ido a baya haka yasa a sakawa Al ‘ Ameen…..

       Yana tashin mota wani text in ya shigo amma yanzu ba Umar bane Al ‘ Ameen ya shigo yana ɗakin Aunty , kai tsaye wurin Dikko ya nufa da gudun tashin hankali ɓacin rai yana hawa , tunda motarshi ta tsaya gaba ɗayansu sukayo waje hada Al ‘ Ameen da matar Dady ita tana cewa wannan wane irin iskancin tuƙi ne zaka zo ka tashi hankalin mutane , wani irin kallo Dikko yayi mata sannan ya kalli Al ‘ Ameen yace me kazo yi nan ne ? Shiru yayi baiyi magana ba , fitowa yayi daga cikin motar ya taka ƙafarshi ta baya ya dafa murfin motar da hannun damarshi na haggun kuma riƙe a ƙugunshi yace da kai nake me kazo yi nan ne ? Aike na tayi , zuwa ina ? A daburce yace ca ca can….. Ya nuna da hannunshi , har yaushe aka fara aiken ni ban sani ba ? Yanzu ne mai gida , tou ya akayi ka shiga ɗakinta ? Kai Dikko bana san iskanci ni zan aiki yaro kazo kana mishi tambayoyi , hannun daya dafa murfin mota ya ɗaga mata ba tare daya kalleta ba yace hajiya ba dake nake ba yanayin fushi yana gaf ki kama gabanki ko kimin shiru , sakin murfin yayi ya matsa kusa da ita ya riƙe ƙugu yace ai nima a cikin matan na tashi kuma duk wani makirci na iya kuma duk a wurinku na koya ki bari kafin in gigita miki tunani , wurin Al ‘ Ameen ya koma ya riƙe wuyanshi amma bai matse ba yace tunda kake ka taɓa ganin wani mai aikinta yaje ɗakin Momy ? 

     Kafin Al ‘ Ameen yayi magana ta ɗaga murya tana salati cikin kuka wai ita Dikko ya daka ? Ta shiga 3 ta lalace , Dikko yace tou tunda sharrin kike so bari ki tara man mutane idan Dady yazo zance Al ‘ Ameen na kama ɗakinki , ta ɗage baki bata ƙara ihun ba kuma bata rufe bakinta cikin tashin hankali ta kalli Dikko tace ummmmmm , murmushi Dikko da gefen bakinshi yace ummmm a dai² lokacin da yayi ma kan Al ‘ Ameen kyakkyawan riƙo da duka hannayenshi ya buga shi da bango yayi mishi fashin kwakwa , amma ba fashewa yayi biyu ba , take a wurin Al ‘ Ameen ya ɗauke , dariya Dikko yayi ya kalli matar Dady har yanzu bata rufe bakinta ba , but ya buɗe ya jefe Al ‘ Ameen ya rufe yaja motar da gudu ya barɓaɗeta da hayaƙi bata matsa ba tana tsaye wurin , Goruba yakai Al ‘ Ameen ya cire wayar jikinshi ya nufi asibiti dan dare yayi.

       Satina 3 a asibiti bayan nasha doguwar wahala dan bayan an haska ƙwalwata likitoci sun tabbatar da jini ya shiga brain ina saida akayi min borrhole surgery kuma kullum Dikko ne yake jinyata komai shi yakeyi min yana bani haƙuri akan abinda ya faru bazai ƙara ba , amma na daka kaina ƙasa bazan komai zama dashi ba.

        Inna kuwa Dikko ya kirata ya faɗa mata banda lafiya tace Allah ya sawaƙe itama tasha fama da rashin lafiyar wai tayi ɓarin ciki , da yace mata gani cewa tayi tana gaisheni itama zata dawo kwanan nan , 

      Dikko kuwa ya ƙufule akan duk wanda baizo ganin Sultana ba shima saiya rama , zama dai cikin mata yasa shima ya iya tsegumi da irin halinsu ,

      Bayan an gama kai magunguna a mota da dai abinda ya kamata yace muje , fashewa nayi da kuka ni bazan zauna ba , haba An mata wai meye kikeyi haka don Allah ? Nifa gaskiya bana sanka saika sakeni da , da ƙarar kwana dana mutu an fara kiran marigayi Sultana , yi haƙuri bazan ƙara ba , nidai bazan zauna dakai ba mahaukaci , ba komai idan ma kince mahaukacin ne ai banji wani damuwa ba na yadda ni mahaukaci ne kiyi haƙuri dan girman Allah An mata , nifa bana zama dakai saika sakeni , daka min tsawa yayi tare da cewa anƙi a sakekin kuma tunda ke yarinya ce ta tashi mu tafi bara ki sake magana kiga yadda zanyi dake dan kiga ina lallaɓaki kike tunanin na warke ? Tou ina nan yadda kika sanni tun farko ban canja ba sai abinda yayi gaba ya ƙarasa maganar yana min kallon da bana so.

    Naji tsoro amma saina kalli ƙasa na sake cewa saika sakeni , zama yayi kusa dani yace An mata kalli ya nunamin cikin ƙwayar idonshi da kallonshi mai ɓatar da damuwa yace yanzu ko dan albarkacin wannan bazanci ba ? Haba ƙaramar yarinyar Dikko cikin sigar lallashi ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da rungumoni jikinshi ,

A wahalce na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka , dafe ƙeyata yayi da hannunshi yace ai na sani kiji natsuwa daga jikina An mata yayi maganar yana jawo numfashi daga cikin cikinshi saiya ɗan riƙeshi a ƙirjinshi kamar shashsheka haka da ɗan sauri² mai tayar da tsikar jiki cikin salo mai tada hankali , shiru nayi ban sake ko motsi ba na ƙara lafewa a jikinshi , murmushi yayi a zuciyarshi yace haba An mata ina zaki tafi kibar mahaukaci ? Ai muna tare harsai hauka ya ƙare.

      Saida ya tabbatar ya ladabtar da jikina ya fara ƙoƙarin sakina , ƙara riƙeshi nayi ina kuka , me ne ne kuma ? Ba komai na bashi ansa , tou sakeni , anƙi a sakenka na faɗa da irin ansar daya bani aa farko ina ƙara lafewa a jikinshi kamar ƙadangare ya lafe jikin bango idan yaga mage , murmushi Dikko yayi cewa tou tashi muje gida sai ki rufe ƙofa ga makullinma tun yanzu ya bani a dai² lokacin daya ɗagoni yana kallona yace kinga sai muci karenmu ba babbaka ko……? Ya ƙarasa yana ɓata fuska a sakace , Murmushi nayi banyi magana ba ina kallonshi , yace yawwa jarumata muje ya ƙarasa maganar yana saukoni daga saman gadon….

     Ashiru ne ya ɗaukemu , dani da Dikko muna baya kuma tunda muka baro ɗakin har yanzu bai sake magana ba sai haɗe rai yakeyi kamar bai sanni ba , ko magana nayi mishi saidai yayi min wani irin gittaccen kallo , ni na kasa gane inda ya dosa wani irin birkitaccen hali yake dashi yanzu mutum anjima ba mutum ba , tsoki nayi ban sake magana har muka isa goruba road , ajiyemu Ashiru yayi ya tafi da motar ledar magungunan ya bani wai inje ciki yana zuwa kuma inyi wanka….

      Banyi magana ba na shige , na daɗe sosai har nayi wanka na fito bai shigo ba , jikin madubi na matsa ina duƙar da kaina inda akayi min aiki , taƙaitaccen murmushi nayi tare da komawa da baya na zauna saman gado ina kallon kaina a madubi nace ina Amisty ? Kizo kiga ranar da nake faɗa tazo ,

      Nace miki naji a jikina zan rasa wani babban abu mai muhinmanci a rayuwata , ni kuma zan shiga wani babban tashin hankali wanda bansan ranar zuwanshi ba , ashe abinda zan rasa ba komai bane sai Babana , tashin hankali kuma ashe shine wannan na taɓa kaina yau itace ranar wayyo gani anyi min aiki cikin kai niba mahaukaciya , fashewa nayi da kuka gaskiya rayuwata ta cika tsalle² a dai² lokacin nan ya shigo yana cewa kin fara ko ? Kedai kika sani An mata kiyi duk abinda kikaji kina iyawa , da gudu na tashi naje na rungume Dikko cikin kuka nace wai me yasa rayuwa take tsanantawa ne ? Ba tare daya riƙeni ba yace An mata duk yadda rayuwa ta baki kawai ki ansa , ya ƙarasa maganar yana jana zuwa gaban gado ya zaunar dani , wayata ya ciro daga aljihunshi Hafsa ke kirana , shine ya ɗauki wayar yace ya akayi ne ? Bayan wani lokaci yace lafiya , kila gaisheshi tayi nadaiji yace lafiya , …….., tana bacci , …….. Wane wuri ne ? …….. Tou bata da lafiya idan ta samu sauƙi zan kaita yana faɗin haka ya tsinke kiran !

     Ajiye wayar yayi da nashi ya ɗauki kofi zai fita , tun kafin ya fita cikin kuka nace bazan sha ba , baiyi magana ba ya dawo ya ajiye kofin a inda yake ya nufi toilet , kuka naci gaba da yi ina maimaita bana sha kuma bazan sake sha ba mugunta kawai , har ya fito wanka ban dai tsegumi ba , ko inda nake bai kalla ba yaci gaba da huɗɗar gabanshi , ganin zai saka kaya nace nayi wankan na faɗa a tsiwace , tou ina ruwana da wankanki , ai kaine kace nayi wanka , rigarshi yake ƙoƙarin sakawa yana cewa tou ki kwanta kiyi bacci idan kuma kina zuwa tashi mu tafi G R A zanje Jiddah bata da lafiya , banyi magana ba na tafi inda ya ajiye kofin na ɗauka nace zansha , ai babu ya ƙare ki saka kayanki kawai mu tafi , yi haƙuri , a , a , dan Allah Dikko ai nace babu ya ƙarasa maganar yana kallona , na bari , zaki sha ne ? Ey tou jeki ibo ya faɗa yana cire rigar daya saka tare da cewa dandai baki lafiya amma yau dasai nayi miki rowa ƙaramar yarinya dake , murmushi nayi tare da juyawa na murza ƙuguna cikin salon jan hankali da neman faɗa , murmushi yayi ya biyo bayana yace bakijin magana ko An mata ? Nima yadda naga yana ɗaga gira nayi nace kai ka koyamin rashin jin ai…

     Ah ni ƙarya kikemin , tare dashi mukaje wurin firij ni na riƙe kofin ya zuba yana kallona yace An mata nan gaba kodai nine zan riƙa riƙe makulli , hmmm idan ya ƙare bana sake siyowa inba haka idan kika kamani a ɗaki saina ci ƙaniyata yayi maganar yana riƙoni jikinshi bayan ya maida “yar jarkar a firij , ɗaga hannuna nayi da niyar shafa gemunshi amma saina ɗorashi a goshinshi , dan shima haka yakeyi baya yadda mace ta gane abinda yake tada mishi hankali a jikinta kuma ko yana kwance da mace yana warwarewa yana saiti baya surutu shiru yakeyi sai wani munafikin kukan kissa mai tsayawa a rai da tada hankali idan ka tunoshi , kome nake abun yana yawan zuwamin a rai , idan na tuno abun sai hankalina ya tashi sai naji maganar Dikko ko na ganshi ko naji ni a jikinshi nake samun natsuwa , Hmmm Dikko duniya , amma ban sani ba ko ni ɗaya yake ma haka ……?

    Saifa na taɓo dan haka na ɗan basar na taho da hannu ina kawowa saitin bakinshi ya sumbaci hannun muah yana sauke wani irin nishi , tsikar jikina ta tashi yarrrrr da sauri na shanye maganin nace ngode , murmushi yayi ya jani zuwa ɗaki….. An danbace cikin tsari da sabon salo ba irin wancan ba…

       Sai bayan isha’e muka isa G R A kuma an sauke bene anyi ma palo gyara na bada mamaki idan baka san wurin ba zaka rantse bene bai taɓa zama a wurin ba a cikin sati 3 , binshi nayi har ɗakin Jiddah ina ƙara kallon palon , ɗakin cike yake da mutane da “yan uwan Jiddah da mahaifiyar Dikko da danginshi , sai wata mai kama da maman Dikkon kila itace maman Jiddah , wani irin kallon tsana Momy ta bini dashi har naji babu daɗi jikina ya fara ƙyarma , kusa da Dikko na zauna idona ya cika da hawaye kuma har yanzu jikina bai daina ƙyarma ba dan ni a halin yanzu bana so nayi wani abu da zaisa nayi nisa da Dikko wallahi bana iya rabuwa dashi , cikin rawar murya nace Momy ina yini ɗauke kanta tayi bata ansa ba , kallona Dikko yayi yace me ne ne kike kuka ? Dakel na haɗiye yawun bakina nace ba komai , kallon Momy yayi sannan ya sake kallona , tana ganin Dikko ya kalloni ta nunamin saita kasheni , da sauri na ɗauke idona na gaishe da Maman Jiddah , itama ɗayan mara wayan ɗauke kanta tayi in banda rashin wayau abiyar zaman ɗiyarta aida da wayau ko ba daɗi tayi ta “yan bariki tace lafiya lau Sultana badai wayau “yan mata sunma makaɗi tusa…..

       Duk basar dani sukayi sukaci gaba da firarsu ita Maman Jiddah babu ɗan kawaicin nan irin na sarakuta da Dikko ta saki baki sai ɓarin maganganu takeyi na rashin lissafi a gaban Dikko abinda na fahimta wurinta Jiddah ta gado surutun tsiya kamar akku , ita kuma Maman Dikko bata da yawan magana kuma bata cika dariya ba tana da natsuwa sosai tanayin magana cikin aji da kamun kai amma bata da mutunci “yar masifa ce wato mafaɗaciya su kuma su Dikko a wurin uwarsu suka gaji rashin mutunci , suna da sakin layi idan mutum ya shiga jikinsu dole zai raina su dan basu da sirri ga Mardiyya amma sai sakin layi suke suna maganganu…….

      Dikko kuwa bayan ya gaisa dasu Momy wurin Jiddah ya koma yana ta jera mata sannu haushi abin ya bani kuma na ƙufule har a wuya ji munafurci ɗazun nan yake nuna ba wata bayan ni amma yanzu yaga Jiddah harya manta da Sultanar banza , kallon Jiddah nayi sai wani kwarkwasa takeyi tana kashe mishi ido shi kuma yabita da kallo , komi ya sameta ? Oho ma banza , miƙewa nayi na fita dan abune nasu na “yan uwa ni kuma a cikinsu bare ce ba “yar uwa ba dan haka na tattaro mutunci na nabar ɗakin ,

    Palo na dawo na zauna , shiru² ba Dikko ba inuwarshi har 9:13pm gajiya nayi na kirashi a waya , ya akayi ? Ya tambayeni bayan ya ɗauka , bacci nakeji , kashe wayar yayi ya fito saida yazo inda nake zaune yace ai na ɗauka kin tafi kin kwanta , jeki ki kwanta fita zanyi yayi maganar yana miƙomin wayoyinshi , cikin ɓacin rai nace ai dama dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , yarinya kenan idan kinga dama tashi muje , nifa bana kwana gidan nan a ina ma zan kwana tunda an rushe ɗakin na ? Bai bani ansa ba yace tou naji baki kwana tashi kije Ashiru ya maida ki goruba , ai ni tsoro nakeji saidai mu tafi tare idan nayi bacci kaje inda zaka je , duk in fasa abinda zanyi sai kinyi bacci kammar sakaran namiji ? Ke zaki koyamin yadda zanyi rayuwa ma kenan ko ? Idan kinga dama ki bishi ni kinga tafiyata kuma karki zubar min da wayoyi yayi gaba abunshi…………



02/12/2019 ????????



*JAMILA MUSA…* ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button