COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

[8/19, 10:54 AM] Zarahh: ???????? COLONEL UBAIDULLAH????????
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????


Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????


Ya Allah kabani ikon farawa lpy na kuma gama lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

________________________

page°°°1&2

9JA,BARRACKS ABUJA

Tsaye yake daga shi sai 3quarter mai ratsin tambarin sojoji a jiki, sai farar T-shart and p-cap shi ma na sojoji.

Dogo ne amma baza kace masa dogo sosai ba ,yana da ɗan fadin fuska daidai wa daida ,sannan baza kace masa fari ba, za dai ka iya saka shi a layin chocolate color
Yana da gashin baki wanda ya kewaye masa baki wanda hakan ba ƙaramin kyau ya qara masa ba, duk da idonsa sanye yake da black shadow,but yana da ƙananan ido kmr na yan’chinese , yana da faɗaɗɗan ƙirji irin na gwarazan maza jarumai saɗaukai.

Duk ya zuba hannayen sa a aljihu, yana tsaye fuskar sa babu alamun fara’a domin shi ko da smiling ne bai cika yiba infact baya ma yi balle kuma dariya bcox baya daukar raini a barracks, bama iyakar barracks ba ,a koma ina ne baya daukar raini, duk da sojoji ne amma da yawan ana shakkar sa.

Iska ne ke ƙadawa awajan domin a garden din barracks din yake tsaye.

Bakin sa ne ke moving ahankali saika Lura da kyau kafin ka fahimce ashe waya yakeyi but da airpieces a kunnan sa.

Bisa alama kuma da mahaifiyarsa yake wayar domin yadda yake wayar cike da natsuwa.

Mama tace.

UBAIDULLAH ina fatan dai komai lafiya?”

Sai da ya numfasa ya hura iska kafin ya ce

” eh mama lafiya lau fatan kuma kuna nan lafiya? Ina su sister’s ?”

Mama tace.

” lafiyarmu lau hafiza ta je gidan yayarku ummu,na aiketa ,ita kuma na’ila wai taje karban aron littafi agidan su kawarta.”

“Mtsww!!! wlh mama na’ila bata jin magana at oll,na hanata zuwa yawo amma bataji, wani irin littafi da rana haka?”

Mama tace.

” indai na’ila ce sai dai mu dinga taya ta da adduah Allah ubangiji ya shiryeta.”

Ya amsa da ameen
Hira suke dan tabawa na tsakanin uwa da ɗanta.

mama tace.

“Ubaidullah yaushe zaka zo ka gan mu ne kam munyi, kewarka sosai wlh.”

” Karki damu mama zanzo a next week weekend In sha Allah.”

mama tace.

” Allah ya kaimu” suka ci gaba da hira,
Ji yayi anyi hugging dinsa ta baya azafafe ya juyo domin yaji kamshin turarenta
Kashe wayar yayi yana cewa I will call u back mama luv you!!

Sa ke fuskantar ta yayi yana tamke fuska , ita kuma tana murmushi sanye take da kakin sojoji itama sai murmushi take masa, tasa hannu zata shafi fuskarsa ya buge hannun, sannan ahankali ya bude mouth dinsa lyk mai koyan mgn yace.

“waike RUMAISA how many times zan fada miki ki dai na haɗa jikin ki da nawa?”

Smiling tayi tace.

” first lieutenant Ubaidullah I will never tried to say I love u duk fadin barracks din nan oll ladies din DA suke rububin suna sonka karya su keyi! ni ce masoyiyar ka Wanda nake maka true love, plss I beg u Ubaidullah ka so ni ko da kaɗan ne “

ta ƙarasa tana so ta shige jikinsa ya bankaɗe ta ya wuce yana jan dogon tsaki ,rumaisa kuma tayi kwafa ta juya domin indai wannan wulaƙancin Ubaidullah din nan ta saba shan sa.

Ahanya kafin ya isa dakinsa ya hadu da close friend dinsa infact garinsu daya tare suka taso burinsu ɗaya arean su ma ɗaya.

ZAIDU yace.

” Ubaidullah tun dazu nake neman ka ban ganka ba ina ka shiga?”

A kasalance yace.

” ina garden barrack ne menene?.

” No dama stall sergeant David ne yazo neman ka akan mgnr meeting din da za a gudanar anjima a babbar filin taro na murtala barracks shine lieutenant general yace. A fada maka kai da commander Ku shirya domin taron ma yana da nasaba da mu dan gsky naji ƙishin ƙishin akan cewa zabe za ayi domin tura jama’ai izuwa bordern Niger domin kama yan’ta’adda.”

“To kai Zaidu a bakin wa kaji ?”

“Na dai fara ji a bakin sergeant first class A,M kasan halinsa maybe shima ji yayi.”

Ubaidullah yace .

“ok amma K,B yasan da mgnr ?.

Zaidu yace.

” eh dazu ma mun hadu dashi na fada masa kaine kawai baka sani ba.”

Ba tare yayi mgn ba ya jinjina kai kawai.

Duk inda ya gitta sai an kallesa amma ya tsare gida dan Ubaidullahi akwai tsare gida, su na tafiya suna dan taba hira har suka isa part dinsu.

Suna shiga parlour suka sa mu Raihana kwance a 3seter sanye take da wandon sojoji da black T-shart kanta ko p-cap din ma babu, balle kuma dan kwalli ko veil”

Ubaidullah yayi tsaki yace.

” ke kuma fa? oya tashi ki fita kafin raina yabaci ya fada yana mata nuni da kofar waje.”

ahankali Raihana ta miƙe tana taku harta zo daf dashi domin numfashin su har yana sarkewa waje daya tace.

” i will,but ina so kasani wlh wlh bazan taba barin ka ba Ubaidullah, ta juya ta fice.”

Zaidu ya kwashe da dry yace.

” wlh ladies din yanzu duk sun gama kwarkwancewa kalli fa yadda suke rushing akan ka?”

Tsaki Ubaidullah yayi ya shige bathroom domin yayi fresh’up.

Bayan ya fito ya shirya, ya ɗauki doguwar jallabiyya ya saka,
yadan kwanta.

Ya lumshe ido yana tuno rayuwar baya , haƙiƙa yanzu komai yana so ya zamo masa tarihi,sai kuma babban burin sa, na gaba.

Bacci ma yake ji amma bazai iyaba dan haka ya tashi zaune.

Kallon sa.

” Zaidu yayi,lafiya kuwa Ubaidullah?.

“Mtsww wlh Zaidu ina yawan tuno baya ne.”

“Bai kamata ka dinga tuna baya ba Ubaidullah,ka fuskanci gaba kawai,a rayuwar ka komai ya wuce, tunda a karshe Allah ya cika maka burin ka na zama jami’in soja, wanda kuma ake alfahari dashi.”

Numfasawa yayi.

” Zaidu kasan ina da buri sosai a rayuwa ta, but bana so na dawo dasu mama barracks din nan,cox ka kalli abinda ladies ke min mama ba za ta ji dadi ba, ba ma zata jure ba.”

“Haka ne kuma ,to amma ya zakayi?”

“Abinda nima ban gama yanke shawara ba kenan.”

Tattaunawa suka cigaba dayi.

K,B ne yayi sallama ya shigo da sauri har yana tuntube,
Zaidu yace lafiya kuwa K,B?

“Ina kuwa lafiya, ga Raihana da Zeey can su na dambe wlh ina tausayawa Raihana dan babu abun da zata ɗauka, a jikin Zeey, yarinyar da ko wasu mazan tsoronta sukeyi, balle kuma Raihana.”

Dryn mugunta Zaidu ya hauyi, yace.

“Ubaidullah tashi muje mu gani,kai Zeey bata da hakuri,am sure Raihana ce bata da gaskiya, cewar Zaidu.”

Duba agogon sa Ubaidullah yayi,yaga har to 4, yace.

” i don’t have time for this stupid ladies, Ku shirya mu tafi meeting.”

Shiryawa sukayi cikin kakin su na sojoji ,suka fito su na taku a hankali, wanda na Ubaidullah ya sha banban da nasu.

Commander suka sa mu sannan suka ɗun guma murtala barracks.

•••••••••••••••••••

Duk inda ka wulla idon ka baza ka iya banbance waye da waye awajan ba.

Sojoji ne birjik ta ko ina da ina.

Nan aka nemi da a buɗe, taro da adduah ,major usman shine wanda ya buɗewa musulmai nasu,sai major jonh shine ya buɗewa christian nasu,
Kafin, aka fara gabatar da meeting.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button