BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

sai da Meena ta gama kintsa falon sannan Baba Rabi tashiga falon suka sake gaisawa da Hafeez, Baba Rabi tasake da Hafeez sosai sai jansa take da fira, wanda shikuma Hafeez gabad’aya kunya tagama cikasa kasa sakewa yayi da Baba Rabi, bayan sund’anta6a hira sama sama ne Hafeez yaciro kudi Wanda shi Kansa baisan iyakarsa ba yace wa Baba Rabi gashinan tayi tsaraba, dafarko Baba Rabi qin kar6a tayi tace a’a ae Balkisu tayi musu hidima sosai dan haka baxata kar6i kudinsa ba, gabad’aya Hafeez jiyayi daraja da kimar tsohuwar taqaru a idonsa, dakyar dai Hafeez ya samu ya lallama Baba Rabi ta Amshi kudin,….daga bisani Hafeez yace da ita shi xai wuce gda dama yaxo ne dan yayi mata Allah yakiyaye hanya, Baba rabi nan tayi tasa mishi albarka tana mai nuna jindadinta sosai.
Hafeez nafitowa Meena tasa Hijabinta tad’auki wayarta sukayi sallama da Amma, a hanzarce tarufawa Hafeez baya a tare suka fice a gdan.
Gaban Meena sai dukan uku uku yakeyi gabad’aya taqisakewa sai faman takure kanta takeyi.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:50AM, 8/6/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣7⃣
Daga Hafeez har Meena ba Wanda yace da wani uffan haka har suka isa gda, Hafeez nayi parkn Meena tayi sauri tafice a motan, tsuki Hafeez yayi cike da haushinta, a filin gdan Hafeez yayi parkn din motanshi baiko sami damar sakata ma ajiyarta ba, a hanzarce yarufawa Meena baya.
Meena da sauri tabud’e kofan falon sannan tanufi d’akinta, isar take nan takama kofan da niyyar tabud’e sai jitayi Hafeez yace “kee! Tsaya anan Meena ko waigawa takasa tsaye tayi bakin kofar kmr wadda aka shuka.
Hafeez nazuwa a fusace ya manna Meena ajikin Bango, take mata babban yatsanta yayi naqafa da qarfi Meena tasaki Yar qara, Hafeez yace “aikin banxa ashe kina mgn?, Meena ganin Hafeez ya kura mata ido ko kiftawa baiyi yasa tasadda kanta qasa, Hafeez gyad’a kai yayi yace “dakyau hakan Yatabbatar min da cewa baki da gaskiya sannan inaso kifad’a min uban waye yabaki izinin tare mai adai daita har kitsaya dashi kina masa dariya? Meena wacce sai mutsu mutsu takeyi tanason kwace kanta daga riqon da Hafeez yayi ma hannayenta gashi ya taka mata babban d’anyatsa yaqi sakewa, Meena kamar xatayi kuka tace nifa badariya nake mishi ba, kawai tambayarsa nayi anawa xaikain…..kafin Meena taqarasa abinda take son cewa Hafeez yadaka mata tsawa yace ni ba wannan natambayeki ba cewa nayi meyasa kike masa dariya?
Meena tayi rau rau da idonu tace Dan Allah yaya kayi hkri baxan sake ba.
Hafeez yace no ba laifinki bane laifina ne sbd kin raina ni ko? Meena ta girgixa kanta tace “a’a
Hafeez yace okay toh yayane? Wato hakan ma yananufin cewa idan kukaje garin naku haka xakiyi behaving? Kina tare masu abin hawa kina musu dariya? Toh bari kiji inkikasa wasa a tafiyan nan wlh sai nace babu inda zaki, sannan sbd tsaban kinrainani wato nabaki awa biyar akanki dawo gda shine kikayi xamanki sbd tsabar kinnrainani ma shine kike ganin kinfi qarfin kid’aga waya ki kirani kice xaki koma gda.
Meena tace “wlh ba haka bane nadauka kana gurin aikin kane shiyasa nayi tunanin komawa da kaina, a firgice Hafeez yaqara matse ta da bango wnda gabad’ayansu sunajin numfashin juna, Hafeez yamatso da kanshi daf da fuskar Meena yace” an gaya miki cewa aiki na yafiki muhimmanci ne ko kuwa bakisan cewaa..shiru Hafeez yayi ya kasa qarasa abinda yake son cewa.
Sake mata hannu yayi sannan yanuna ta da yatsa yace toh bari kiji ban amince ko da kinyi wannan tafiyan ki ke yawaita hawan motan haya ba ko kice xakisawa mutane gyale, can kuma Hafeez ya kufula yace ke daga yau ma nayi canceln sa gyale a gareki, inkinga kinsa gyale toh daga ke sai nine acikin gdan nan kinajina ko?
Da sauri Meena tace ehh!
Hafeez ya gyara tsayuwansa ya kalli Meena dakyau sannan yace in kunne yaji jiki yatsara, d’akinshi ya wuce yabar Meena tsaye.
Huuhh!! Shine abinda tace kawai tashiga d’akinta
A gajiye takwanta bisa gadonta tadafe goshinta, cikin zuciyarta tace “hmmm Yaya kenan dama nakawo haka araina sbd naga take takenka kwana biyun nan sokake ka hanani wannan tafiyan shiyasa kake tsiro da rigima kala kala nikuwa nasan halinka dan haka a ynxu dai baxan biye maka muyi ta rikici ba, balle kasamu galaban hanani yin wannan tafiyan.
Kiraye kirayen sallahn la’asar din da akeyine yasa Meena tayi hanzarin tashi tanufi toilet tad’auro alwala.
Abangaran Hafeez kuwa wani irin abune yatsaya mishi arai nan yafara jerowa kanshi tambayoyi wai mema yasa nadamu da lamarin wannan yar qauyen ne mema zaisa naji kishinta ohh my god kar fa najawa kaina raini agun wannan bakauyiyar yarinyar (nidai Munay dariya nayi, nace araina babu mai amsa maka wannan tambayoyinaka sai munturo maka JUMAYMA Yar bincike ta bincika mana kai LoL)
Hakanan Hafeez yayi ta faman sintiri cikin d’aki shi kad’ai yarasa abunda ke mishi dad’i domin gabad’aya jiyayi bayason abinda zaisa Meena tayi nisa dashi. Tunani barkatai Hafeez yayi tayi har dai shima yajiyo kiran sallahn yatashi yad’auro alwala yanufa masallaci.
** **
Bayan dawowar Hafeez a masallaci haka kawai ya tsinci kansa da son xaman falo, kasancewar Meena nacikin kitchen, shiyasa ya zauna yana kallon dukk wani shiga da ficenta.
Haka nan Hafeez yayi xaune har Meena tagama kirginta ta jerasu a dinning table ta wucewarta d’akinta domin ta shirya kayan da zata tafiya dasu gobe.
*Washe Gari*
Tunda asubar fari Meena ta tashi kmr yadda tasaba tad’aura abin brkfst ta jerawa Hafeez a dinning area, sannan tashiga toilet ta silla wankanta, tana fitowa tashafa versiline sai powdr Meena bata yarda tayi wata doguwar kwalliya ba domin talura a yan kwanakin nan Hafeez na matuqar nuna kishinsa akanta Wanda ita kuma hakan yan burgeta yana kuma bata tsoro, wata atamfarta tad’auko tasa sannan ta sanya hijabi har gwiwa.
Travelling bag dinta tajawo ixuwa falo, sannan tanufi sashen Hafeez ta kwan kwasa mishi kofa.
Hafeez nacikin d’akinsa yafito a wanka kenan yaji kmr ana buga kofa, jallabiyansa ya jawo yasaka sannan yaje ya bud’e kofan.
Meena yagani tsaye cikin shirinta na tafiya ga kuma nan jakar kayanta a gefe, haka kawai Hafeez ya tsinci kansa da fad’uwar gaba. Jiki a sanyaye hafeez yadubi Meena yace “har kinfito? Meena tace eh! Ina kwana Hafeez yace lpy Lou.
Mamakine Yakama Meena don yau ko ince ynxu taga wani irin canji atattare da Hafeez komai yakeyi tamkar Wanda bashi da lakka ajiki haka nan ya kama jakar Meena yasa a booth din motarshi.
Har gdan Baba Rabi yakaita, Hafeez yashiga sungaisa da Baba Rabin sannan yamusu Allah kiyaye hnya.
Bai wani jima ba a gdan yayi sallama da Baba Rabi, Meena har tayi xamanta domin bata da niyyar mishi Rakiya, sai da Baba Rabi ta doka mata harara sannan ta tashi tabi bayansa.
Xakujini anjima don jin ci gaban lbrin, ynxu banda caji ne. Tnxs oll😘
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:06PM, 8/6/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿