KWARATA 4

???? —— 4
Ya uzura min sosai akan naje na bawa Dikko hakuri dan haka na tunkari wurin kai tsaye zuciyana tana min tsake tsaken mugunta iri daban daban.
Cike da bacin rai na isa wurin, kamar yanda na fadawa tsohon nan zanyi haka kuwa nayi, dan ina zuwa na kamo kafar Dikko da zumar na fadar dashi kasa ya karya kashin baya,
Amma ina, dan ina riko kafar shi daya, ya tattakura yakai min halbi da dayan kafar da ban rike ba, hanci baya raina duka lokaci guda jini ya ballemin kamar an yanka kosashshiyar kaza,
Yana halbina ya diro daga saman motar shima ashe yayo dagon muguntar shi yana neman inda zan sauketa ya huta, ganin jini yana bimin baki har yana digowa kasa yasa hankalina ya tashi,
Sosai nayo kan Dikko, yaranshi suna kokarin rikeni yace su barni yanzu zai koyamin hankali yanda idan na ganshi da gudu zan canja hanya.
Daga nesa mutane suka fara bashi hakuri dan babu wanda ya isa yazo kusa dashi, babu wanda ya kalla bare kayi tunanin ko zai saurare ka, kusa dani ya matso sosai, yasa hannuwan sa biyu ya riko min fuska, sai yanzu nakejin halbin da yayi min yake ratsa duk ilahirin cikin kokon kaina, gaba daya jikina ya saki ya koma kamar ba nawa ba,
Sama sama nake ganin Dikko har yanzu bai daina cin cingom in da yakeci ba, saida yayi min kyakkyawan riko sannan ya cire gilashin dake fuskarshi ya kalleni ido cikin ido sannan yayi dan kyakkyawan murmushi, wanda ke nuni da mugunta ta tashi…
Sai mun sake had’ewa an mata…yana fadin haka ya k’uma min kanshi da nawa wuri daya wanda haka yayi sanadiyyar daukewar gani na gaba, amma har zuwa wani lokaci goshina da nashi yana hade wuri daya,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }()); Bai sakeni ba saida ya tabbatar na tafi suma, dan tabe baki yayi tare da dage girarsa ta dama sannan ya sakeni ya zura hannuwansa cikin aljihu ya nufi motarsa dashi da tawagarsa suka bar anguwarmu.
Ni kuma na fadi kasa somammiya, Allah sarki dan uwa mai dadi duk “yan gidanmu basu ji dadin abinda Dikko yayi min ba, sun tausayamin iyakar tausayi gashi babu mai kwandalar da za’a kaini asibiti, saidai aka samo kankara aka rika dandan na min a goshina tunda habo ne nayi,
Abokin Babanmu shi yaji labarin abinda ya faru damu, yana da wani gida na Alhaji Sabo da aka saka a caca ya ciwo gidan, shine ya bada makullin gidan aka kawo mana yace mu bude mu shiga,
Daukata sukayi suka shiga hadani tare da bani kulawa ta musamman, amma duk abinnan saida nayi sati daya kafin na dawk daidai,
Babana har yanzu bai dawo ba kuma bamuji labarinsa ba ko ta waya, kuma har yanzu ban yadda na sake fita ba koda zaure saboda zuwa wannan lokacin bana san ganin Dikko ko inuwarsa,
Gaba daya na jingine islamiya da wata bokon banza, daga tsakar gida sai daki, idan ina tsakar gida naji karar mota ma daki nake komawa,
Satinmu ukku a gidan abokin Babanmu Baba baizo ba, kuma baiyo aike ba, shima kuma wannan gida da muke ciki Dikko ya siyeshi, ba’a gidan kadai ya tsaya ba duk gidan da yasan na hayane a anguwar saida Dikko ya sayeshi duk sun zama mallakinsa, tashin hankali da damuwa kowa ya shiga,
Saida abokin Baba yazo yake fada mana cewa an kama Babanmu yana can an kulleshi saboda ya ranci miliyan biyar din wani abokinsu bai bashi kudin ba, shine ya kaishi wurin hukuma suka tsareshi,
Kowa ya jinjina miliyan biyar saboda babu wanda yasan abinda Baba yayi da kudin nan, shiba gida ba, ba mota ba ba fili ba, haka kawai ya saka kanshi rikicin duniya.
Inna na kalla data zabga tagumi tana d’igar da hawaye, cikin yanayin tausayi nace Inna wai da zaki auri Babana bakuyi binciken halinsa ba kafin auren ku? Banza Inna tayi dani bata bani amsa ba, tsoki nayi tare daci gaba da cewa muma mata muna da matsala yayin da muka hangi tilin dukiya da babbar mota hankalinmu, ganinmu da kuma tunanin mu sukan b’ace , idan aka samu kwadayayyar zuciya sai kuma takai mutum ta baroshi, kamar dai ku duk zuciyoyi ne da kwadayin duniya suka kawo ku nan suka barku, kiyi ta addu’a kema Allah sa ya sakeki ki huta. Kunga mutum da arziki bakusan taya yai ya samu abinsa ba,
Inna dai bata tankamin ba, muka fito domin “yan gidanmu sunce muzo mu tafi wata primary school dake bayan gidanmu mu kwana tunda dare yayi kafin mu samu gidan zama, duk muna tsaye a tsakar gida dan Dikko yace wallahi idan muka kara cikakkun mintina biyar saiya kunna mana wuta,
Cikin kyarmar jiki nacewa Maman Fa’iza “yan uwan Babanmu basu da kirki kowa ya zura masa ido dashi da iyalanshi sai wuta mukesha babu mai roka mana sassabci a rayuwarmu, ansa daya ta bani itace, ai babu ubanda yasa shi aure auren kuma basune suka sa duk yayi cikunnan ku aka haifo ku duniyar ba.
Haka tayi ta surutai marasa dadi na bad’ala da rashin kamun kai har muka fita gidan muka tafi makarantar, koda muka fito motoci sunkai biyar masu zafi tsadaddu masu burgewa da daukar hankali, an haska fitilinsu duka, amma yau babu Dikko dan naji suna magana cewa mai gidansu yayi tafiya baya k’asa amma ya umurcesu da su tabbatar bamu kwana gidan nan ba, idan mun fita mun huta idan bamu fita ba a kunnawa gidan wuta, wannan shine sakon da Dikko ya aiko dashi,
A makarantar mukaci gaba da zama cikin azuzuwa, { Classes } idan dalibai sunzo zamu fita waje idan sun gama suka tafi zamu koma mu zauna, ni na gaji na fadawa matan Babana waisu basu da gidan iyayensu ne ? Wannan wulakanci ai ya isa haka, kowa ta tafi gidan ubanta ta huta mana, ai fa yak’ai yak’ai kamar zamu cinyeni d’anyata saboda tsabar masifa, dole naja d’an bawan Allahna nayi shiru.
Satinmu daya kullum sai an koremu kamar karnuka kuma kullum bama tafiya sai mun dawo, da safe kuma su tura yaransu su shiga bara cikin gari, rayuwa dai wulakantattar rayuwa mafi muni da k’ask’anci, Babana baya da adalci kuma baya da imani hakika zai tadda Allah, domin wannan zalincin yayi yawa.
Ranar da muka cika kwana takwas aka koremu da karfin bala’e mukabar makarantar malaman suka kara da cewa gwamnati bamu ta ginawa makarantar nan ba muje can musan inda zamu zauna amma ba makaranta ba, suka kara jaddada mana idan suka sake ganin wata wallahi sai sun kaita an kulleta wurin “yan sanda,
Nanfa Allah ya bamu sa’a cikin malaman wani ya ji kanmu ya bamu kyautar fili dan mun fada musu matsalar mu, shi kuma ya tausaya mana, saifa suka fara yahani akan fili yayin da kowa ke cewa saidai a siyar da filin a raba kudin aba kowa,
Yayin da wasu ke cewa ayi hakuri a zauna, masu cewa ayi hakuri a zauna sun rinjayi wanda keso asiyar, dan haka dole suka hakura, muka dinguma zuwa fili, bayan munje akayi tamalmala ta malmala aka siyo buhunna dasu aka zagaye gidan ,
Wannan fili dai bazai ansu a wurin Dikko ba, nima ganin mun samu mazauni hankalina ya komawa tunanin Babana,
{{{}}} {{{}}}
Bayan wasu kwanaki,
Rayuwata nakeyi cikin jin dadi, nidai Allah ya taimakeni bana bara saboda kanin inna yana kawo mana dauki da abinci, kunsan idan mace ta koshi tou fa lallai bata da aiki sai iskanci da rashin kunya, toni dana koshi nawa iskancin Dikko kadai yake nema ido rufe, kullum ina bisa hanyar zuwa tsohuwar anguwar mu, haka zan hau napep kamar duka kenan saina tabbatar mun kusa zuwa sai in dire abuna, wasu basajin fita ta wasu kuma suna gani idan suka bini basu kamoni ba saidai suyi min Allah ya isa, nima na fara dauko kadan daga cikin dabi’un Babana.
Yauma direwa nayi, da gudu nasha lungu na shige wani gida, zaure na tsaya saida na huta sannan na tattaro natsuwa na shiga ciki da sallama,
Cikin sakin fuska matar ta ansa min, wuri na samu kasa na zauna ina gaisheta, ta ansa lafiya lau, shiru nayi zuwa wani lokaci nace mata hajiya dan Allah kin iya rubutun wasika ? Murmushi tayi sannan tace niko na iya rubutun wasika, nace tou don Allah kitaima min mijin Yayata ne suka rabu shine yayi mata shegen duka ya raba mata kai da tab’arya tana can asibiti rai hannun Allah, kuma sai rubutun zagi yakeyi yana aikowa gidanmu, shine aka rubutomin ansa na maida mishi kuma takardar ta fadi, ni kuma idan na rubuta sabuwa zai gane rubutu na ne , amma ki taimakamin don Allah, ni na karanta wasikar kuma zan iya fada miki yanda take kiyimin rubutun nakai mishi don Allah……..!
Ba tare da tunanin komai ba tace tou, daki ta shiga ta dauko jakar makaranta, da gani ta yara ce , a ciki ta dauko biro da paper tace min bismillah, duk ba tare da tayi wani dogon binkice ba ko yin nazarin yin hakan me zai haifar daga baya.
Ni ko dadi naji sosai a zuciyata , tunda ni bazan iya rubuta uwar komai ba, amma nayi farin ciki sosai domin dai yau zanci uwar Dikko kafin in fara kashe dawanki dan iska. Bayani na farayi ta fara rubutawa,
Ka fita daga rayuwarmu yayin da ni kuma yanzun nakejin farin cikin shiga taka rayuwar, salon ka yana da matukar burgewa dan marasa tarbiyya, taya zaka fara rashin tarbiyya kuma ka gaji da sauri haka ? Ko kudin sayen gidajen ya kare ne ? To tunda kudin sayen gidaje ya kare nasan zakayi kokari ka samo kudin sayen dokuna, ina mai farin cikin sanar dakai daga yanzu d’innan har zuwa ranar da zaka bar zaman anguwar nan farin ciki zai bar zuciyarka, kuma zaman anguwar nan zai haramta a gareka kamar yanda ka haramta mana zama a cikinta, zanyi ta kashe dokunan ka harsai ciwon zuciya ya kama ka idan ka fasa kai ba d’an Babanka bane…………
Sultana ce, Allah ya bawa mai rabo sa’a, idan kaje Islamiya kace amin……
Mikomin tayi bayan ta kammala rubutawa, godiya nayi mata sannan na fita, nayi tafiya mai dan nisa ina kokarin bi hanyar da zata sadani da tsohuwar anguwarmu na hango Dikko ya sauko daga saman doki……,
Jar riga ce a jikinshi amma ba irin ja d’innan ba ja mai kyan kallo, sai jar hula akanshi irin wacce matasa ke gayu da ita, fesin cap, bakin wando ya saka wanda suke kira 3quater da rufaffin takalmi, sai bulalar da ake dukan doki a hannunshi, daga gani dai daga kilisa suka dawo,
A fili nace shege mai kama da mata, cin cigom kamar tsohuwar karuwa, duk’awa yayi k’asa ya d’auki wani abu wanda ban iya ganewa ba, bayan ya d’auka ya koma saman dokin yayi mishi diddige tare da tsuke bakinshi irin yanda ake kora doki yayi gaba,
Da gudu ya wuce ya wani d’an jirge saman dokin yayi kyau sosai bazan mishi haddasa ba gaskiya, ci gaba nayi da tafiya, kafin in ida isa wurin kuma naga ya wuce da gudu cikin mota kura tabi bayan motar sosai kamar guguwa ta taso.
Hamdala nayi domin na samu damar farko da zan kashe doki d’aya daga cikin dawakan Dikko, saboda nasan wata mugunta d’aya da ake ma doki, ba’a ba doki ruwa idan aka dawo dashi daga yawo, idan aka bashi ruwa a wannan lokacin tou cikinshi k’ullewa yakeyi ya mutu.
Nikaf ina na ciro na saka tare da gyara tafiyata na tun kari gidan kai tsaye, a kofar get in gidan nayi ma mai gadin gidan sallama, ya ansa cikin sakin fuska, nace mishi dama wani mutum ne da jajayen kaya a jikinshi yace in turo mishi kai yana can yana jiranka….. Na nuna mishi hanyar da Dikko ya wuce da hannuna ,
Cikin sauri ya wuceni ya tafi, yana wucewa na shiga cikin gidan, doki d’aya ne kad’ai wato shine dokin da Dikko ya dawo dashi, an d’aureshi a gefe kuma an cika bokiti da ruwa an ajiye shi kuma dokin yana ta bubbud’a hanci yana maida numfashi,
Da sauri na kinkimi bokitin ruwan nakai gaban dokin na ajiye, aiko ina ajiyewa ya duk’ar da kanshi yaci gaba dashan ruwa, a daidai lokacin da mai gadi ya shigo dan yabi hanya baiga Dikko ba ya dawo,
Kay kay kay ba’a bashi ruwa yana k’ok’arin isa dan d’auke ruwan na tareshi tare da cewa anshi yace ka ajiye mishi wannan takardar idan yazo da daddare zai karb’a, bai tsaya ansar takardar ba kuma baimin magana ba ya wuce,
Murmushin nasara nayi daga cikin nik’af ina sannan naje na ijiye masa takardar a saman kujerar da yake zama na wuce abuna.
Kafin ya isa tuni doki ya shanye ruwan dana ajiye mashi, sai dai abinda ba’a rasa ba, cikin tashin hankali ya ciro wayarshi daga cikin aljihu ya fara kiran wayar Dikko,
Mai gida kazo akwai matsala dokin daka dawo dashi yanzu, gashi nan zai mutu, yana fad’in haka ya kashe wayarshi,
Cikin k’ank’anin lokaci Dikko ya iso, a k’ofar gidan yayi parking ya fita da sauri ko murfin motar bai tsaya rufewa ba, lokacin daya shiga cikin gidan tuni dokin ya kwantar da kanshi k’asa yana ta zabura irin na fitar rai.
Meya faru haka ne ? Dikko ya tambayi mai gadin shi ! Cikin daburcewa ya fad’awa Dikko duk yanda mukayi dashi , sannan ya d’ora da cewa ga takardar can daka bata ta kawo ta ajiye, ajiyar zuciya Dikko yayi tare da furta wace ce ita tayimin k’arya ?
‘Daukomin takaddar kila tana da wata manufarta a ciki, d’aukowa yayi yakai mishi, ya warware ya duba, cimimiye takardar Dikko yayi bayan ya gama karantawa ya dink’uleta wuri d’aya sannan ya jinjina kanshi, ya fito da sauri daga cikin gidan,
Wurin motarshi ya tsaya, tare da kaima gaban motar duka sannan yace wallahi cikin k’ank’anin lokaci duk inda “yar iskar yarinyar nan take cikin garin nan ku d’auko min ita, yana fadi haka ya shiga mota yaja fa fafa ya tafi kamar zai tashi sama…….
Har yayi nisa ya dawo, har yanzu mai gadin bai koma cikin gidan ba yana nan tsaye a wurin, yanzu daya dawo bai fito ba ya sauke glashin motar shi sannan yace, ku kawota wurina zan nuna mata nid’in d’and’an Babana ne wallahi wallahi wallahi sai tayi nadamar zuwanta duniya.
Yana fad’in haka ya juya a guje ya tafi, lallai da ganin yanayin shi gaskiya ranshi a b’ace yake, tabbas idan har aka kamoni aka kawai Dikko ni a cikin wannan yanayin lallai Dikko kasheni zaiyi,
Lokaci d’aya jikina ya d’auki kyarma naji fitsari ya kamani sosai, “yan hanjina suka juya ai bansan lokacin dana bar wurin ba, cikin tashin hankali na hau napep na nufi filin gidanmu, tun kafin mu isa na dire nayi gida da gudu……..
Da sallama na shiga, Babana na gani zaune dashi da abokanshi kuma sune suka amsa min sallama, cikin farin ciki ya kalleni tare da cewa daga ina kike Mamana ?
Cikin inda inda na sosa kaina tare da cewa daga gidansu k’awata nake, murmushi Babana yayi tare da mik’ewa yace muje waje muyi magana, naso nayi masa gardama dan gani nakeyi kamar idan na fita zanga Dikko k’ofar gidanmu,
Muna fita na fara tambayar shi ya akayi ya dawo ? Yace min su Bello sukayo belin inshi, akwai wani wasan caca da za’ayi an saka naira miliyan hamsin kin san na kware sosai a wasan caca babu wasan cacar da za’ayi a ci ni saidai ni in ciwo shi yasa ake min hassada.
Gyara tsayuwar shi yayi tare da d’an jan dogon hancinsa, sannan yace Mamana kinsan ba’ayin wasan caca a bashi sai an saka k’addara, bani da k’addara sai kayan sakawata, na saka amma ance ba’asan sutura, tou Bello ya bani shawara wai in sakaki a matsayin k’addarata,
Cikin rashin fahimta nace Baba kamar ya za’a sakani a matsayin k’addara bayn nima banda komai… Murmushi yayi tare da cewa Mamana kenan ai kuwa kece ma mai komai domin keda kanki kece babbar k’addara ta shi yasa na zab’eki a cikin duk “ya “yan hamsin da takwas dana aifa…..
Kiyi hak’uri kawai ki yadda duk wanda yazo ya tambayeki kece k’addarata kawai kice Eh, danni na yadda da kaina babu ubanda ya isa ya ciwo uwata a wasan caca saidai ni inciwo uwarshi wallahi, Mamana ki yadda da Babanki nayi alk’awari baza a samu matsala ba, ki yadda dani kinji Uwar masu gida, ya k’arasa maganar yana mai rik’e duka hannaye na duka biyun yayi kalar tausayi.
Tou Babana idan aka tambayeni zance Eh kawai ko ? Yawwa Eh zaki ce kawai ya wadatar, insha Allah gobe kamar yanzu muna cikin kud’i kuma ga Uwata a tare dani, ya k’arasa maganar cikin farin ciki, murmushi nayi mishi sannan muka koma cikin gida dan in fad’awa su Bello na yadda……….
Allah yasa muyi juma’a lafiya, ubangiji ya sadamu da alkairan dake cikin wannan juma’a mai albarka, mugun ji da mugun gani tsaka mai wuya ubangiji ya tsare daga garesu, Allah ya karemu da jin kunyar duniya da lahira. Am3n,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());