BUZUWA

*_Mutanan kirki watau yan BUZUWA fans kuna can cikin zuciya ta Allah yabar zumunci nagode sosai_*
*_fans dina na Facebook kuma ina godiya a gareku Allah yabar so da kauna_*
????6⃣
*Ta* saki ajiyar zuciya har ta fitoh fili.
“Yasir ka yi tunani mai kyau,
zan so MARYAM ta zama mata a gareka
in da ace mutuniyar kirki ce ko dan saboda zumunci ya k’ara k’arfi sosai
sai dai MARYAM halayyarta bata da kyau Wanda duk namijin da ya aureta zai yi kuka nan gaba saboda bazata tab’a bada tarbiyar data daceba ga yayanta ba”
“Yasir ina so ka fitoh da Matar Aure nan da 2 weeks in ba hakaba ba
ba abin da zai hanaka auran MARYAM dan nasan tana fada ma mahaifiyarta
daddy ka zai amince,
ka sani ba abin da daddy ka k’anwar shi zata nema ya hana ta,
inaso nan da two weeks ka nemo mata dan ai magana da iyayan ta in ba hakaba kuma,uhmm Allah yasa wake dai”
sunkuyar da kai yasir yayi “yace insha Allah mommy na gode Allah ya kara lafiya da nisan,kwana”
“Ameen mommy” tace
” tashi kaje Allah ya maka albarka ya baka macce ta garin”
“Ameen ya Allah momy”
yana fitoh,wa daga wajan mommy
kicibus su kayi da little da Yusrah
Little tace “sannu ya Yasir yana murmushi yace “yawwa my little” suna k’okarin shiga k’ofar da zata sa da ka da mommy
little na gaba Yusrah na baya rik’o hijab din Yusrah yayi wanda little ita tuni ta shige.
had’a fuska yayi kamar bai tab’a dariya ba sai da ya janyo ta ta dawo gaban shi suna face din juna.
“ke bari kiji wallahi duk wani k’ananan iskancin ki kisan Wanda zaki dinga mawa bani ba saboda tsabar kin rainani kin ganni ko gaishe ni ba ki yi ba, bari in fad’a miki koh da wasa karki kuskura ki k’ara kwaso mana Mara sa kunya samarin ki irin ki, gidan nan in ba haka ba zan hada dake dasu in karkarya ku saboda baki da kunya,
k’waya nawa kike da har zaki tsaya da saurayi yaushe mama taga manke miki k……”
da tsawa tace “dakata malam ya isheka dan naga abin naka bana k’are bane,
ka gama in wuce ?
sannan gida daka ke maganar samari,na suna zuwa saurayin daya ke gareni Abbas ko kuma in ce maka mijina,ma
baka da ikon kahanani kawoshi saboda ba gidan ka bane
gida na daddy ne in da ace daddy ne yace kar nakara kawo wani sai in aiki da fadan, shi ballema nasan ba zaice ba Dan shi mutumun kirkine sanan da kake cemin kwaya nawa nake da had zan tsaya da samari bar raina Allura karfe ce kum”….
“dalla dakata malama daman rashin kunya taki harta kai kice ni ba mutumun kirki ba ne saboda tsabar kin raina ni”
mtssss taja tsaki zata wuce jan yota yayi da karfi ranshi gaba daya ya gama macewa “kinyi kadan Ina magana ki kelleni ki wuce ke bari kiji ba make ba har yanzun ba’a haifi yarinyar da zata min haka ba
in kuwa Ina magana ki ka k’ara kuskuran wucewa in ranki yayi dubu sai na bata shi magana samari karki fasa kawo su Allah yaba mai rabu sa’a mara kunyar banza
kowa yasan baba da mama su mutanan kirkine aman ke,kam kin fitah da ban bamusan Ina kika koyo wanan mugayan hallayar taki ba”
wani uban tsaki taja tace “in ka gama ka wuce kaga tafiyata” tai wucewar ta tabar shi sake da baki in banda kallon inda tabi ba abin daye sai kace wani wawa ta kusan shiga wajan momy su kayi kicibas da mommy
“a’ a Yusrah Ummi daman tace tara kuke sai gashi baki shigo ba” “eh mommy na koma na dauko waya nane shi yasa” “ok” ta gaishe da mommy ta shige ciki mommy ce ta hango Yasir
“Yasir daman baka fita ba”
“eh momy naje dauko a bune a dak’i na shi yasa” “ok sai na dawo mommy” ” a dawo lafiya dan albarka Allah ya tsare”.
Kai na gaji wlh da na muku typing da yawa
Muje next page
By y’ar mutanan KD
????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????
*_BUZUWA_*
????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH_*
*_????KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*????
“`{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} “`
*EDITED*
*BY*
*MARYAN AHMAD PAKI*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
“`Allahumma ajirni minna narr! Allahumma ajirni min Azabil qabr! Allahumma inni as As’aluka min Jannatul Firdaus , Allahumma inni As’alukal fawza fil Jannah wan-naja’atu mina-narr. Bi Rahmatika ya Arhamarrahimin ya rabbil Alamin. Amin“`
????7⃣
“Allah yasa momy” yayi gaba “Allah ya taimake ki mommy ta fitoh da na gwada miki ke k’aramar mara kunya ce” ya fitah yana b’ab’atu a zuciyar shi, yana fitah sukayi kicib’us da ABK da yake k’okarin
shiga da mota.
tsayawa yayi ABK ya fitoh “maza sai ina haka a kafa nasan dai ba nisa kayi ba” had’a rai ya k’ara yi “lafiya mutumin? ABK ya jefa mishi tambaya “ai daga ganina ba sai an fad’a ba Kasan ba lafiya” yasir ya ba amsa”waya tab’a min kai ne?”
“ai ka san duk gidan nan wace take b’ata min rai yanzun” oh maza ka dinga sama ranka hakuri ka daina b’ata ranka a kan wanan bai war Allah ita fah ba tasan ma kana yi ba”
“ai zata sani duk sanda ta ganta a karye ne”
ABK ya zaro ido “yasir kasan me kake fada kuwa yarinyar mutane zaka karya?”
” sai me dan na karya wanan mara kunya”
“har kamar ni zan dinga mata magana tana banza dani daga k’arshe ma wucewar tayi ta kalleni saboda tsabar ta raina ni” ya fada da mutukar hassala sai kace yanzun tai mishi abin”, ABK yace “sorry abokina ka dinga sama ranka sallama a kanta sanan ka sani abin da hak’uri bai baka ba tsiya baza ta baka ba dan Allah ka dinga zama mai hakuri da kai zuciya nesa”
“ABK kasan me yafi b’ata min rai yanda tafitoh gatse gatse take fad’an min baza ta daina kulla wanan yaron ba harda cemin mijin ta, Allah ji nake kamar ta cakamin wuka saboda tsabar bak’in cikin yanda ta dage take fad’an min magana” dariya ABK yake yi “abokina sorry ya fad’a yana wata dariyar shak’iyanci “yanzun dai ina ka nufa? “Yasir yace gidan ne naji yamin zafi shi yasa na fitoh shan iska dan ban san ina ma zan nufa ba gaba daya yarinyar nan ta chaja min kai ” Allah ya sawak’e” ABK ya fada “ni bari in k’arasa ciki daga nan in gaishe da mommy ”
“OK sai ka fitoh”
ya matsa yaba ABK hanya ya wuce shi kuma ya zauna a kofar gidan dan shan iska in ji shi
A b’angaran MARYAM ranta a matuk’ar b’ace ta shigo gidan ba sallama koh da daman ba d’abi’arta bace yin sallama kafin ta shiga waje ba kusa da uwar taje ta zauna sai wuci take kamar wata kububuwa “lafiya MARYAM?uwar ta jefa mata tambaya “har kin dawo daga gidan yayan?”
a fusace tace “eh mana me idon ki ya nuna miki” “haba mama kibar mutum yaji da abin da ya dame shi aman kin sani gaba sai wasu tambayoyi kike min”
murya a taushashe sai kace itace yar ” Yasir din baki same shi bane?
“na same shi mana amnan koh kallon arziki be min ba
nayi mishi bayani kwana kin baya akan yanda soyayyar shi take wahalar dani aman yaki amsan tayin soyayya da nami shi a yanda na lura dashi koh ganina ba yasan yi ya fada” hawaye na zubuwa a fuskar ta “MARYAM a kan yasir kike kuka? Ki barni dashi zanje na sami yayana na mishi bayani halin da ake ciki dan bazan je ba inaji ina gani ya kashemin ke ba abanza ba wlh yayi kadan kuma nasan harda wanan munafukar uwar tashi ta dinga Abu simi_ simi sai kace wata mutuniyar kirki” basa shiri da mommy shiyasa ko da yaushe hajiya A’i take ganin laifin mommy da abin da ta aikata da wanda batai ba duk itace
ajiyar zuciya MARYAM tayi “mama ba za ai haka ba, ba daddy da zaki fad’an mawa ai yazama dole Yasir ya soni kuma ya aureni in aka bi ta wajan dadi ya soni mu kayi aure bazan sami kullawar da nake fatan samuba a wajan shi sanan ba zai taba sona ba ni kuma nayi wa kaina Alkawari dole Yasir ya soni kuma ya k’aunace ni ba boka ba Malam dan so na ke in kafa babbar masarauta a zuciyar shi yanda sai ya koma yana kallon matan duniya basu da babbanci da maza sai ni kad’ai zan zama tauraruwa a gare shi” (anya MARYAM baki makara ba)
Murmushi mama ta saki yan magana ” hausawa sun yi gaskiya da a ka ce magaji mafiyi wanan maganar gaskiya ce ” shi ya sa har kullum nake Alfahari dake y’ata dan nasan zaki iya abin da tafi haka”
Mama gode ina so in je fati Amman na kwana ne” “Allah ya kaimu”
????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????