
Dan liti yace nikam meye matsala ta da
da duk abin da kalissafo,
Taimako na fa kuka nema bani nanemi auren ba, balle yabani sha’awa, indan tanine kasa ranka a inwa banida matsala da hakan,
Nidama karake yadawo sati daya alhaji danni takuramin za ayi, har sati uku ”
A’a yihakuri dan liti, yakai sati ukun kar jama’a sugane, to shikenan Allah yabamu sa’a, alhaji yace amin,
Yabama dan liti kudi yace yasamu na kashewa, dan liti yayi godiya,
Har sunrabu alhaji usman yashiga motar shi shikuma, dan liti yana tsare abin hawa, alhaji yadanna mishi horn, yadawo yace ai namanta dan liti yaufa saura sati daya ta fita idda,
Yan kazauna cikin shiri, nikuma nanda kwana biyar, zankawo maka kayan da zaka rinka zuwa, wurinta dashi,yace to alhaji, Allah yakaimu yace amin.
Alhaji usman yana zuwa, gida yakira baby j yayi mata bayanin yadda sukayi da dan liti, dafarko bata yarda ba, tace ita bazata iya auren kowa ba inba shiba,
Alhaji usman yahau washe hakora, yaji shifa akeso haka dai yata lallashi har ta amince ”
A yau ne jamila tafita idda, a yau dinne dai alhaji usman yashirya ma dan liti, haduwa da baby j.
Karfe takwas na dare, alhaji uaman yayi parking kofar gidan su baby j, yakira ta awaya cewa suna waje shida dan liti ”
Dama tayi wankanta taci ado, dama su jamila ba ayi makeup dinba ma ya akakare, balle kuma anyi, tashiga dakin inna dan tafada mata wani yazo nemanta awaje,
Tasameta zaune kan sallaya tana karatun kur’ani, tazauna seda takai aya tashafa, sannan tace inna wanine yake sallam dani awaje, to jamila kuma har yasan yau kika gama idda
Jamila tace eh Inna tawurin maryam yabiyu shiyasa yasan nagama din, to Allah Yasa mudace, tace amin inna kije amma karki dade fa, insha Allah bazan jima ba,
Koda jamila tafito taga batasan alhaji usman da wannan motan ba, tana karasowa, yabude mota yafito ya wani hade rai, yace baby j saboda nace miki wani zezo wurinki ne,shine kikasha makeup haka?
Hnmmmm ni har akwai wanda ya isa inyimai kwalliya, sama da kai, kawai fa dan kacemin tare zakozo ne shiyasa nayi,
yauwa baby j tawa, tare fa muke da dan liti din, bazan iya barinshi yazo shi kadai bane, Shiyasa nadauko shi muzo tare ayi hiran tare dani”
Dan bazan iya bari yaro dan yanjini yatsaya min dakeba, zuciya ta zata buga, Jamila tayi murmushi tace karka damu karubuta ka ajiye, Jamila takace.
Waiyo nikaina wlh har kinsa naji wani sanyin dadi a raina, dole inmiki kyauta, bari inmiki transfer yanzu kuwa, take yamata kuwa dubu dari uku, tayi godiya yace to bari inbarki dashi yanzu nasamu kwarin guwiwa,
Tafiya gida, dan liti yafito alhaji yace karfa kadade, kawai basaja ne abun dan dai aganku tare ne, kawai.
Dan liti yace badamu wa insha Allah,
To ga dan liti ga baby j…………..
Muje zuwa
Yar mutan Kagara
*AUREN* *KISAN* *WUTA*
*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*
*PAGE* *11* */* *12*
Koda alhaji usman yatafi, yarake subiyu wani irin kalo Jamila takwashe dan liti dashi, tace amma kai kam anyi mayan son kudi, saboda kwadayi abun duniya shiyasa kana yaronka dakai,
Ka abince aure na na sati uku, hnmmmm yanzuma intambaye ka, kasan me akecewa in anje tadi?
Dan liti dayayi tsaye yana kallonta, yagirgiza mata Kai alaman besani ba, tace kaga illan talaka ko ga kwadayi ga dakikanci, dan liti shi dai yazuba mata ido yana kallonta,
Tace to ina jinka bakazo zance bane?
To fadi inajinka, dan liti dai yana tsaye yanade hannunshi a girji, yana mata wani irin kallo , wanda koni yar mutan Kagara, banace nasan fasaran wannan kalon ba”
Haka jamila taci gaba da fada mishi magan ganun duk daya mata dadi, shi dai nashi ido,
Jamila tace kadai san badade wa zanyi ba inmukayi aure ko, yace eh nasani tace nifa sati ukun da alhaji yadiba, yamin yawa gaskiya,
Dame zaka rikeni nasan duk alhaji usman dindai shi zeyima komai, Kai saboda talauci shiyasa kayarda da auren kisan wuta ko?
Dan liti yace a’a kawai dai, alhaji usman ne yanemi alfarma, kuma ya cancacci inmasa ne, shiyasa nayar da,
Suna chin haka saiko ga malam, tai mishi sannu da zuwa, dan liti yaduka har kasa yagai sheshi, ai malam yaji dadi,ya amsa mishi cikin mutunci da jindadin gai suwan da yayi mai,
Sabani wasu samari, basaba iyayen budurwa girmansu, kuma malam farat daya yaji yana son yaro, yakwanta mishi, tana ganin malam yashige tajuya tana shigewa gida, tana cikin tafi ne tace zaka iya tafiya,
Sai wani lokacin shi dai dan liti dakallo yabita, abun ma dariya yaba shi, yajuya yatafi
Dan liti besha wuyaba wurin neman auren, jamila saboda daga malam har inna, Sun yaba da tarbiyan shi da nagarta, ga kuma natsuwa,
Koda malam yanemin dan liti yaturo magaba tansa, dan liti baban abokin sa musa yasama, yafada mishi yadda sukayi da malam,
Malam tanko yace to madalla abu yayi kyau, Allah yasanya alkhairi, dan liti yace amin, dan liti yace ammafa abba bazawara ce, masha Allah, kakoyi koyi da ma’aikin Allah,
Hakan yayi kyau, kuma nizan jagoranci al amarin, zamu je tare da kannaina, insha Allah, dan liti yayi godiya,
Biki dai yakan kama, ansa rana sati biyu masu zuwa, kuma malam tanko baban musa, shine waliyin ango,
Alhaji usman yagama komai yayima jamila setin akwati hankare da kaya, yayima dan liti shima seti goma, na fitan biki,
Yakuma ba dan liti gidan da zasu zauna, chiki da parlon da toilet dakuma kitchen, yakuma chema su malam karsuyi komai, shizeyi mata duk abunda iyaye kema yaransu,
Sukayi godiya.
To ranadai bata karya sai dai uwar diya taji kunya, a yau ne dubban jama’a suka sheda daurin auren dan liti da jamila, akan tsadaki naira dubu goma,
Dubu goman ma alhaji usman ne yace ga dubu goman, yabayar saboda iyayenta sunsan ango beda kudi, wankin mota yakeyi kawai, karsuzo suchiga wani tunane shiyasa yabada dubu goma,
Ankai amarya gidanta, kowa yatafi tunda bazawara ce, koda tarake ita kadai bata damuba, hasalima tafison hakan saboda suna makale da juna da alhaji usman a waya,
Yana kara jadda damata, karta yarda yace zeyi wani abu da ita, ita kuma in yafadi hakan sai taji ranta yabaci,
Tace mishi ita ko mazan sunkare mezatayi da wannan yaron, ai ba abunda ze iya yimata, in tafadi haka shikuma alhaji Usman sai yaji wani sanyi dadi,
Basubar waya ba har taji shigowan dan liti, tace gaba dawayar ta hankalinta kwance,
Shikuma yayi kaman besan meta keyiba, sai da suka gaji dankansu sannan suka hakura,
Ta tashi tashiga toilet tayi wanka ta dauro alwalla, koda tafito humra kawai tashifa tasaka dogowan riga tayi sallah,
Ta idar tanaciki karatu kur’ani taji wanyan dan liti yana ringing a parlon, tagane da alhaji yake wayan, saboda taji yana cewa insha Allah bazan kusanci taba har mucika sati ukun,
Alkawari na dauka, to madala alhaji ka kwantar da hankalin ka ba abunda zefaru,
Haka rayuwa yata tafiya, duk cefanen da dan liti zeyi ahaka zai lalace, jamila bazata girkaba, sai dai tafita tasayo abunda zataci, tunda kullum alhaji usman cikin tura mata kudi yake,