Daga karshe, Shugaban Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa Mulki a zaɓen 2023

Da aka tambaye shi kan haka bayan kammala Sallar Idi a Abuja, Buhari yace zai miƙa mulki ga duk wanda yan Najeriya suka zaɓa.
Ya kuma kara da kalubalantar manyan hafsoshin tsaro su bi yan ta’adda har inda suke su kawar da su daga doron duniya.
Abuja – Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara matsowa kusa, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake magana kan mutumin da zai gaje shi bayan wa’adinsa ya ƙare.
Daily Trust ta rahoto cewa a shekarar da ta gabata lokacin da ya zanta da wata kafar Talabijin a Najeriya, shugaba Buhari ya ce bai damu da ko waye zai gaji kujerarsa ba.
Daga bisani kuma shugaban ya ce duk da yana da wanda yake son ya gaje shi a zuciyarsa, amma ba ya son ya bayyana wa duniya shi saboda, “da yuwuwar a kawar da shi idan ya faɗa.”
Sai ɗai da yake jawabi bayan kammala Sallar Idin ƙaramar Sallah a Barikin Mambila dake Abuja, Buhari ya jaddada jajircewar da gwamnatinsa ke yi na tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.
Da aka tambaye shi kan wanda yake son ya miƙa wa mulki a 2023, Shugaba Buhari ya ce: “Mutumin da yan Najeriya suka zaɓa.”
Bayan haka shugaba Buhari ya ƙalubalanci hafsoshin tsaro da dukkan hukumomin tsaron ƙasar nan su bi yan ta’adda har maɓoya su kawar da su daga duniya.
Buhari ya jaddada manufar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya.
Ya ƙara da cewa wajibi a tabbatar da tsaron manoma yayin da suke gab da komawa gona, domin ceto ɓangaren samar da abincin ƙasar nan.
Daga Hausa Legit
[ad_2]