Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 36

Episode 36

………..“Ki rantse bakiji daɗi kamar zai kasheki ba? Nasan dai ustazai basa ƙarya Ustaza!”.
Dariyar da tazo mata a bazata ta ƙyalƙyale da ita da sake rufe fuska saboda a yanda yay maganar.
“ALLAH nidai ba ruwana”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa. Sosai yaji sanyi a ransa ganin damuwarta ta kwaranye ta sanadinsa. Bazai iya cewa komai a kanta ba, sai dai bazai so a wulaƙantata ba domin ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wannan karatune daya samu daga kakaninsa tun ƙuruciya. Sannan bayaso Raudha tai tunanin akwai wani banbanci a tsakaninsu dan kawai tana ƴar talakawa….
Duk tunanin da yake idannsa na’a kanta ne. Bazai ɓoyeba cute face nata na matuƙar birgesa tare da sumar kanta data kwanta har saman goshinta sosai. Sannan a ɗan zamansu ya fahimci tanada haƙuri da juriya. Shiko yana son mutum mai waɗan nan halayyar musamman mara riƙo. Yanda ta saki jiki da shi lokaci guda duk da tasan ba haka yake mataba a baya ya masa daɗi matuƙa da sashi nutsuwa gareta.
“An taɓa faɗa miki k ƙyaƙyƙyawa ce?”.
Ya faɗa cinkin suɓutar harshe da ƙan-ƙan da murya yna sake shanye idanunsa suka koma ƙanana.
Wani irin dummm taji a kunenta saboda furucin nasa. Bazata iya jurewa ba, dan haka tai azamar maida kanta ƙasa tana wasa da zanen less ɗin jikinta. A ranta mamakin yanda baijin ko kunyar ƙureta da ido a lokuta makamantan haka takeyi, ta matuƙar tsanar kallo a rayuwarta, sai dai ta rasa dalilin da yasa nashi baya mata zafi ko gundurarta sai dai sakata a wani yanayi da yake yi…….
“Uhhmm?!”.
Ya buƙaci jin ta bakita cikin wani yanayi.
Fahimtar amsa yake buƙata daga gareta ya sata saurin jinjina masa kanta tana murmushi.
Basar da zancen yay ya ɗakko wani yana furzar da numfashi.
“Kuka yana sake raunana raunin mai raunine a duk sanda yake yinsa. A tunaninki kukanne zai iya canja ƙaddararki? Ki zama mai juriya sai ki kasance cikin masu nasara. Ki ɗauki ƙaddara matsayin jarabawa sai zuciyarki ta dawwama a farin ciki. Ki amsa a duk lokacin da aka jehoki da sharri ko alkairi, sai dai zaɓin inda zaki ajiyeshi yana daga karfin imaninki ne. Bana bama mai son ganin kukana dama a duk lokacin da yaso hakan, domin in tabbatar masa da damarsa itace nasarata a yau da gobe na”.
Ya ƙare maganar da miƙewa zaune sosai ya ɗan leƙo fuskarta da hawaye ke sauka saboda nasiharsa ta shigeta. Tissue ɗin daya ɗiba a side drawer nata ya ajiye mata saman cinya yana miƙa mata yatsansa ƙarami.
“Zamu iya zama abokai”.
Yanda yay maganar da abinda ya faɗa ya sata kasa jurewa saida ta ɗago ta kallesa. Idanunsa manya da suka canja launi ya kaɗa mata.
“Ustazah bana son gulma fa, da kika samu ma zaki zama ƙawar shugaban ƙasar NAYA?”. Yay maganar da ɗage gira sama yana ɗan ɓata fuska.
Murmushi tayi da miƙa masa nata yatsan suka ƙulla.
“A rage gulma ƙawata Ustazah”. Yay maganar da juyawa zai fita….

  _“Nagode, ALLAH ya dawwamar da farin ciki da nasara a rayuwarka data ahalainka baki ɗaya, ya cika maka burinka na alkairi”._
  Cak ya tsaya saboda tasirin da  addu'arta yay a dukanin zagayen ɓargonsa zuwa jini. Ya saki wani lalataccen murmushi daya kawata ƙyaƙyƙyawar fuskarsa, sai kuma ya juyo a hankali gaba ɗayansa yana fuskantarta tamkar mai tsoron hakan. Har yanzu tana a yanda ya barta, sai dai hawayene sabbi ke faman mata gudu a kumatu. A hankali ya tako ya dawo zuwa gareta. Saukar numfashinsa a kanta ya sata ɗagowa da sauri, ƙoƙarin jan jikinta tai baya saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo haɓarta ya sake kai fuskarsa gab da tata. A hankali ya ɗan hura mata iska a saman idanunta data rumtse, sai kuma yay sama kaɗan ya ɗora tausasan laɓɓansa saman goshinta. Harga ALLAH jitai kamar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya, dan kuwa a bazata taji saukar laɓansa saman goshin nata, cikin yanayin kasala ya sake sakar mata kiss a goshi idanusa a lumshe kamar yanda ta ƙara matse nata tanajin kamar ta saki fitsari kawai ta huta.
 “I like you my Friend”.

Ya faɗa a kunnenta cikin wata irin muryar raɗa batare da yasan sanda kalmar ta suɓuto daga ƙirjinsa zuwa harshen ba. Kamar yanda kalmar ta suɓuto masa batare da ya shirya ba haka tari ya subucema Raudha har yawu na sarƙe ta. Sosai jikinta ke tsuma yanzu kam har mai kallonta zai iya ganin hakan. Ramadhan da tuni ya kai ga ƙofa batare da ya juyo ba saboda abinda zuciyarsa ke ayyana masa ya furta, “Kisha ruwa”. Cikin tattausar muryarsa sannan ya fice ko waiwayenta baiyi ba.
Raudha da tari ke neman halaka mata numfashi, dan har ya fara fisga kamar Asthma ɗinta zai tashi ta silmiyo a gadon zuwa fridge, bama tasan a yanda ta ɗakko ruwan ba ta ɓalle murfin kawai ta kafa a baki. Yanda take shansa yana wuce mata a maƙoshi da gudun tsiya haka hawaye ke rige-rigen sakkowa da ga idanunta zuwa fuska. Tas ta shanye ruwan, ta zube ƙasa ita da robar tana maida numfashi.
Sai da taja kusan mintuna biyar a wajen tana kokawa da zuciya da tunaninta kafin hankalinta ya ɗan fara dawowa jikinta. “I like you”. Ta maimaita kalmar daya faɗa a saman laɓɓanta batare da zuciyarta ta amince da sakata a irin gurbin da takejin wasu na ambata ba ga abokan rayuwarsu.
“Tabbas ba haka bane, tashi nada banbanci da tasu”.
Ta sake faɗa a zahiri cikin yarda da kai, dan sam bata yarda da abinda ɗayan sashen zuciyarta ke tabbatar mata ba. Saboda son kauda hakan ma sai ta miƙe ta faɗa toilet kawai maybe idan ta sakarma kanta ruwa zatafi dawowa a hayyacinta fiye da haka.
A wani ɓangaren kuwa mamakinsa take matuƙa. Ina ɗaɗɗaure fuskar tashi ta tafi ne da shan ƙamshi?. Kalaman Anne suka shiga dawo mata a safiyar da za’a kawota nan government house. Ameenatu nasan zaki iya fuskantar ƙalubale kala-kala a cikin auren nan har ga Ramadhan dake amsa sunan miji gareki. Sai dai ina fatan ki zama mai haƙuri da juriya wataran zaki cimma nasarori. Bar ganinsa haka yana wannan ɗaure-ɗauren fuskar da tsumewa yanada sauƙin kai sosai musamman ga abinda yake so. Ɗan karan surutune da shi sannan yana dariya fiye da zatonki. Sai dai bazaki san duk waɗan nan abubuwanba sai kin zama jaruma sannan mace. Kar kiji nace mace ki zurfafa tunani. Mata da yawa sukan koma muna mata a wasu lokutan a gidan aure koma a waje. Amma duk macen data amsa sunanta MACE zaki sameta jaruma sannan duk tsanani bata raki. Mai haƙuri, mai juriya, mai tiƙe sirri, mai bama mijinta farin ciki, mai mantawa da duk wani ɓacin rai bayan ya fuskanceta koda a baya ya cutar da ita, mai kula da tarbiyyar ƴaƴanta dama duk wanda zai kasance a ƙarƙashinta koda ma’aikacin gidanta ne. Karkiyi sakaci da yima mijinki addu’a idan yay miki alkairi koda na murmushi ne, karkuma kiji shakkar bashi shawara ko sauke fushinsa koda bazai fahimceki a lokacin ba koya saurareki. Domin mata dayawa tsoron baza’a fahimcesu ko baza’a ɗauka shawarsu ba kesa watsar da miji idan yana cikin wani hali koda sun fahimci hakan. Wannan ba dai-dai bane ba. Bashi shawara koda baya ganin kimarki, wlhy Ameenatu wataran da kansa zaizo miki da damuwarsa domin yasan a wajenkine kawai zai samu mafita. kuma inhar kikaima miji shawara ta farko ya dace akanta ya kuma fita a damuwa, shima bazai ƙara yarda ya ganki cikin ƙunci bai ƙoƙari ganin ya fiddaki ba koda ace shine ya sakaki sai ya damu ya dawo yana lallashinki da son maye gurbin ɓacin ranki da farin ciki……
Ƙwallane suka cika mata ido, dan kuwa tabbas taga haka, ta kuma yarda da batun Anne. Dan tana ƙyautata zaton canjinsa nada alaƙa da abinda ya faru ranar. Fatanta ALLAH dai yasa ya ɗore.

(Uhm su Meeno aiki ya fara ci za’a mallake ɗan gimbiya Su’adah🤥😏🤕🚶🏻).

_★★★★__

Su Lubnah sun sauka a ɗakin kusa da ita, sai dai saɓanin wancan lokaci ɗaki guda aka haɗesu yanzu. Sosai Raudha ta sake kame kanta da ga garesu, dan taci alwashin zata kiyaye gargaɗin Maah. Sai dai bazata sake bada fuska gasu Muneera suci zarafinta ba duk da kuwa sun girmeta.
To Alhmdllhi, tattarasu datai ta watsar ya taimaka mata matuƙa wajen saka shakkarta a zukatansu. Dan bama ta yarda ta fito inda suke balle su ganta. Ɗakinta kuwa da sun so dinga binta har ciki suyi mata cin kashi, gargaɗin da Ramadhan yay musu ya sakasu kame kansu dan sun san halinsa. Idan ransa ya ɓaci ya kama mutum ya ɓalla ya ɓalla banza babu mai ce masa baiyi dai-dai ba.

Bayan kwanaki uku da zuwansu data kama monday bayan sallar isha’i Raudha na ɗakinta kwance a gado cikin dauriyar ciwon mara data ɗan fara ji sama-sama telephone na ɗakinta tai tsuwwa alamar kira. Ɗagawa tai da tunain Mama Ladi ce ko Mama Tambaya ko Kuku. Dan sune kawai ke kiran layin idan tayi baƙi ko suna sonjin abinda zata ci ko take buƙata.
“Assalamu alaikum”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button