Labarai

Wani uba ya kashe ‘yarsa yar shekara 20 bayan ta cafkar masa mazakuta

Wani uba ya kashe ‘yarsa yar shekara 20 bayan ta cafkar masa mazakuta

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wani  mai suna Sunday Etukudo bisa zargin kashe ‘yarsa ‘yar shekara 20 mai suna Ofonmbuk Sunday, kan rashin fahimtar juna a cikin iyali.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko Macdon, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Uyo, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa marigayiyar tasa ta rike mazakutarsa  ne a lokacin da aka samu sabani, inda ya kuma yi amfani da sanda ya bugi kai.

Bayan aikata laifin, Mista Etukudo ya binne ‘yar a gidansa da ke kauyen Omum Unyiam a karamar hukumar Etim Ekpo a jihar domin ya boye lefinsa

Daga bisani huku.ar yan sanda ta zakulo gawar don gudanr da bincike.
Related Articles

Leave a Reply

Back to top button