Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 50

Episode 49 & 50

……….Da asuba daya tadata suyi salla kuka ta dinga masa sosai. Duk sai tausayinta ya lulluɓesa. Shi kansa yasan ya tsaurara mata da yawa, dan dukan

fushinsa na shekarun nan babu ƙwange sai da ya sauke shi tsaf. Bata wani yarda ya taimaka mataba tace zata iya.
   Koda ya haɗa mata ruwa sai ya fita a toilet ɗin ya barta. Zafin ruwan ya sata harar ƙofar tana ƙunkuni ta surkeshi ya koma salaf. A haka ta gyara

jikinta ta fito tana faman sinne kai. Ga dariya ga tausayi duk suna cin Ramadhan lokaci ɗaya. Amma sai ya gimtse dan karya sake tunzurata.
      Da ƙyar ta yarda suka sake komawa barci bayan ta idar da sallar. Acewarsa su ɗan ƙara rage barcin idonsu dan anguwa zasuje. Taura house yake son suje

hutun nan na kwanaki biyar da akai, amma bai sanar mata ba. Dan kuwa bazai yarda amarcin nan ya wucesa bai ɗana gadonsa na Taura house ba.

(Mutumin nan ko????????)

         ★Tun a daren jiya dama ya sanarma ƙanensa yau zasu wuce Taura house hutu gaba ɗayansu. Dan haka da safe ya turama Bilkisu text ta haɗama Raudha

abinda duk tasan zatai amfani da shi su wuce su sai zuwa anjima zasu zo. Murmushi kawai Bilyn tayi. Sai dai kafin su fita tai ƙoƙarin haɗa breakfast ta

ajiye musu. Mama Ladi kuwa ta zauna gadin abincin nan dan kuwa Anne ta kirata tun sanda suka gane Raudha ce ta aika musu takarda akan saka poison a ac ta ce

mata ta dinga saka ido akan kowa na gidan kar’a cutar mata da su Raudha. Duk da tasan bata isa hana zartar da ƙaddarar UBANGIJI akansu ba.

        Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi matuƙa. Akan fuskar gogan nata ta saukesu. Idanunsa a lumshe, ƙyaƙyƙyawar

fuskarsa tayi wani fayau. Duk da haushinsa na murzar da yay mata jiya babu tausayi da takeji haka ta shagala a kallonsa. Itama kanta tasan shiɗin ƙyaƙyƙyawa

ne, ga yanayin jin daɗin rayuwa daya tashi a ciki, bai san wahalar komai ba sai ta karatu. Ahankali takai yatsanta saman girarsa data daɗe tana kwaɗayin

taɓa tsagar wajen da zuciyarta ke bata wanzami yay masa. Sai dai me, koda ta shafa wajen sai taji santsi irin na tabon ciwo. Mamaki ya kamata, a zuciyarta

tace, (Ashe ba tsaga masa akeba tabon ciwo ne) a fili kam mamaki ƙarara ya bayyana gareta da sake girmama sunan UBANGIJI, dan babu mai kallon wajen yace

ciwone. Sosai tsagar ta fita da tsari kamar yimasa akai akan sani. A hankali ta sauke numfashi da maida gashin girar data yamutsa masa ta maidashi ya

kwanta. Tana ƙoƙarin sake janyewa taji an riƙe hanun. Babu shiri tai saurin rumtse ido tana fisgewa amma yaƙi saki. Nasa lumsassun idanun dake cike da barci

ya buɗe a hankali a kanta. Sai kuma ya sumbaci hanun nata daya riƙi ya turashi ƙasan kuncinsa yay filo da shi.  Ɗayan hanunsa kuma ya ɗaura a jikinta saitin

ƙugunta.
     “Good morning sweetheart”.
  Wani bala’in kunyane da yafi na ɗazun da asuba ya lulluɓeta. Tai ƙoƙarin kauda kanta yay azamar tallafosa da hanunsa dake a ƙugunta ya hanata hakan. Cikin

ɗan marairaicewa yace, “Ki amsa min mana Baby luv”.
        Da ƙyar ta iya buɗe baki tace, “Ina kwana”.
      Ahankali ya shafo kanta tun daga sumar gaban goshin har zuwa ƙeya yana ɗan murmushi. “Ya jikin ki? Duk da nima dai ya kamata a tambayeni nawa kodan

yaƙushi da cizon dana sha”.
      Ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Tai ƙoƙarin jan hanunta da yay filo da shi amma ta kasa. “Kibar wani gulma Ustazah, nasan kina son mijinki kar kiyi

sake wata ta ƙwace miki ni”.
      Kanta tai ƙoƙarin sinnewa a jikinsa. Yay murmushi yana riƙeta ya hana hakan. “Gara na faɗa miki gaskiya matsayina na abokinki babban amininki. Bazan

so a miki kishiyaba kina ƙawata ta hanun damar, dan sai na fiki kishi kilama kullum dani zaki dinga cin dabe da ita a gidan ga muna lakaɗa mata duka ko ya

kikace?”.
       Duk yanda taso riƙe dariyarta ta kasa. Ta saki murmushi tana turesa. “Kai Ya Ramadhan….”
      “K nifa bana wani kalar dangi ƙannena sun isheni, inama laifi da muke abota niba yayanki bane”.
   “Toni ai bazan iya faɗar sunanka ba”. Tai maganar tana sake son cusa kanta a ƙirjinsa. Haɓarta ya riƙo ya ɗago fuskar tata da sumbatar laɓɓanta. Cikin

sake ƙanƙan da murya yace, “To basai ki canjamin da wani ba. Amma sam bana son Yayan nan kamar wani zamanin iyaye da kakanni, bayan kuma jiya na gama

turmusheki a gadon na….”
       Dariya ta ɗan ƙyalƙyale da shi tana kaimasa ƙaramin duka a ƙirji. Shima sai ya rungumeta yana murmushi. Zuciyarsa fes da farin ciki.

       Duk yanda taso zamewa kar suyi wanka tare bai bata damarba. Amma kuma taƙi sakin jiki haka ya gama nashi ya barota a bayin. Sanda ta fito yana zaune

yana waya. Dan haka tai wuff ta fice a ɗakin bayan ta saka hijjab.
       Ciwo take ɗanji kaɗan-kaɗan a ƙasanta amma ta daure ta shirya cikin wani material da yay mata ƙyau sosai da fiddo kalar fatarta. Tayi fayau da ita

daka ganta kaga amarya, sai dai fuskar babu walwala sosai ga idonta duk wanda ya kalleta yasan taci kuka. Yunwa takeji amma batajin son cin abinci kuma.

Bakinma ɗaci takeji yana mata kamar mai malaria. Tana fesa turare ya shigo, sanye yake cikin shadda ash color datai bala’in masa ƙyau. Sai maiƙo take da

ɗaukar iadanun mai kallo. Ya murza hula baƙa data fiddo ainahin hasken fatarsa da ƙyallin angwanci. Duk da waya ya shigo yanayi hakan bai hana Raudha shiga

jin kunya ba, ya ƙaraso inda take yana riƙe kwalban turaren da kunya tasata cigaba da fesa ƙasa-ƙasa dan karya tada mata asthma. Ajiyewa yay saman mirror

ɗin ya riƙe hanunsa cikin nata idanunsa a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yakeji kamar ya haɗiyeta. Ga ɗaurin datai ya sake fiddo ƙyanta kamar dai ya

haɗiyetan ya huta kawai. Ita dai kanta a ƙasa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na Dolce & gabbana daya gauraya da burberry brit. shiko yanata

wayarsa da murza yatsun hanunta.
      Tsawon lokaci harta fara gundura da tsaiwar kafin yay sallama da wanda yake maganar wanda ta fahimci kamar akan harkar kasuwanci ne. Saman mirror ya

ɗaura wayar da kamo fuskarta cikin tafukan hanunsa ya sumbaci goshinta, sai kuma ya sakko a hankali ya sumbaci lips ɗinta dake ƙallin lips gloss. Shima ya

duƙo kaɗan yana nuna mata nasa kumatunsa da goshi.
       “Kai Ya Ramad……”
Sai kuma ta kasa karasawa saboda ɗallin daya bama bakinta. “Dole na fara hukunta wannan bakin idan yaya ɗin nan bai fita a cikinsa ba”.
     Hannu tasa ta rufe laɓɓanta da zafi ya maimaye idonta na cika da ƙwalla. Hannunta ya kamo ya zuba mata link ɗinsa da agogonsa hublot dayay mata ƙyau

sosai kalar ash. Batai musu ba, dan koba komai tasan aiki garesa lada ne. Links ɗin ta fara saka masa sannan agogon.
     “Thanks bestie”.
Ya faɗa a hankali idonsa a kanta. Sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen mirror ɗin. “Ƙarasa mu wuce so nake na more gida sosai lokaci nata tafiya”.
       Duk da batasan ina zasu ba cike take da ɗokin tafiyar. Ta ɗauka hijjab da zai shiga da kayanta ta saka tare da haɗa abinda zata iya buƙata a karamar

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button