Comment on DOCTOR ESHA Page 41 to 50 by Unknown

Tsakiyar cake din kuwa 7 ne Mai dauke da candle a ciki( Kai gaskiya Mai cake din ta kware) .
Pooja ta share hawaye tana ta shafa cake din a hankali tace” Sadik mummyka na matukar sonka, tana tsoro abunda zai rabaku ne kawai, but very soon nasa komai zai zo mata da sauki” ta Kara bin parlor da kallo decoration din ya gama haduwa, harda number ballon Mai dauke da seven da aka kafashi a tsakiyar aluminum balloons dake gefe parlor, gefe guda Kuma Happy Birthday Sadik akasa da flowers na zangaye da rubutu, ga white bulbs da akasa a gida gabadaya sai ya bada wani yanayi Mai annashiwa, Kai guri birthday yagama haduwa, Pooja ta nemi guri ta zauna tana bin yara da ke ta wasa su da kallo, can Arundh ta shigo da guduta ta Sha wanka tayi kyau gashi kana yasha gyara, Pooja ta kirata tana tambayarta Ina su sadik? Ta Bata amsa da cewa taje Airport dauka brother nata”
Da Hindi tace” mummy surprise birthday ne fa aka hada ma sadik, mummy guri ya mi kyau”
Pooja tayi murmushi tace” nasani saura kifada Mai da baki ki na surutu na”
Arudh ta rufe baki tana dariya…
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
Essha ne ke tuki a hankali harta iso Airports din, tana fitowa sai waige waige take tana neman Amir, can ta hangoshi zaune ya makala earpience a kunne, sai danne waya yake hankalishi a kwance, Batama ganeshi ba, sanda ta Kara murza Ido da kyau, Amir yazama wani handsome guy, da sauri ta karasa wajashi ta bashi bugu Wasa a kafada tana murmushi. Amir naji a tabashi ya Mike a zabure, Yana ganita yafara zuba murmushi cike da tsokana yace” kaga manya ba, Doctor Essha, sis kiga yanda kikara kyau, wow sis bamaraki da indiyawa ma”
Taja mishi kunne tana murmushi tace” haryanzu baka canza bako, tsokanar na”
Yayi murmushi yace”sis Ina fa zan canza, gaskiya sis we really miss you, daddy yace nafada Miki gobe, gobe na ba sai jibi ba, ki koma gida, kiga zamu koma tare kenan”
Essha daji haka jikita yayi sanyi, ba haka tasoba, ama dole tabin umarni Daddy, tafison ako yaushe ta riga farata mishi..
Amir ya katse mata zance zuci ta da ” where is my son? Yau ne birthday shi ko?
Tayi murmushi ta kada Kai ..
Yace” toh Ina yake?
” Kai amir sauri Mai kake, yana gida nannyshi tana shiryashi,muje na daukoshi “
Yayi murmushi yace” to muje sis ko Doctor zance”
Bata bashi amsa ba tayi gaba da jakashi Yana biye da’ita , suna isa baki motar ta kunna motar ta bude ta bude ma Amir ya shiga , itama ta shiga, suna Bari Airports sai gida ummulkulsum nanny sadik, suna zuwa suka tarar sai fitina yake mata, yayi kyau jiki shi sanye da black jeans trouser da jeans jacket itama baki, gashi kana yasha gyara, he looks cute. Yasa nannyshi a gaba Wai sai ta hada mishi Khirr( sweet ne da indiyawa ke hadishi da shinkafa da sugar) ya damaita lallai shi Khirr yakeson ci.
Tace” toh Sadik bara na hada ma”
Basu ma lura da shigowar su Essha ba, sanda takara doka wani sallama , nanny tayi sauri amsawa tana murmushi ta musu barka da zuwa tayi hanya kitchen.
Sadik na daga Kai yaga Uncle Amir tsaye Yana mishi murmushi da gudu yaje ya rugumeshi, Amir ya tsaya yana kalloshi girma yaro yabashi mamaki, Essha gani kallo da amir yake ma Sadik ne yasa ta zargu duk ta rikece a tunanita, yagane wani Abu ne , da sauri ta yi gyara murya kamar Mara gaskiya da turanci Tace
” Sadik yau ga uncle Amir”
Sadik ya Mike daga jiki uncle shi yakali fuskar shi ya na Mai murmushi yace” Namaste uncle”
Amir bai amsaba sai bin sadik yake da kallo, yaro ya burgeshi, Kuma yashiga ranshi sosai. Sadik gani bai amsaba bane sai yasa hannu ya waving a fuskar Amir.
Amir ya dagoshi Yana murmushi yace” my boy yakake?
Sadik bin baki Amir uncle nashi kawai yake da kallo yanda yaga ya furta yakake , shi dai yaji my boy ama yakake dine bai ganeba..
Amir ya Bata fuskar ya kalli Essha yace” badai haryanzu Sadik baiji hausa ba?
Ta gyada mishi Kai.
Yace” lallai sis ke da daddy ne, gobe akwai drama, sis ki duba fa , ko yakake din ma baisani ba, wlh muna da ja aiki.
Shifa fa yaro fa, da yare da yatashi dashi nefa yake rikewa har girma, yanzu inmukoma Nigeria, misali ya shiga mix din yara da basaji turanci balle asa wani yare Hindi, kiga Sam basai ji dadi har ya sakeba, gobe Allah yakaimu, Zaki hadu da Daddy, ni baruwana, Allah yasoki ma zaiyi tafiya yau, sai Sunday zai dawo. kila ma boy ko gaisuwa baiya da hausa ba”
Ya dubi Sadik yace” hey greet me with Your mum’s language”
Sadik sai Ina Ina yake yanason ya tuna gaisuwa da mummyshi ta koyamai da hausa ama yakasa sai “En… En ” yake tacewa har ya ba Amir dariya..
Amir ya rugumeshi Yana dariya yace” Don’t worry boy, nasan ba laifika bane, is ur mum’s fault, da Bata koya maba, Kar kadamu Autar mummy da grandpa zasu koyama, Dani zankoma school, mummy ka Kuma. Tasan ma ranta fada sai Tasha shi guri daddy , dun wanan rubutace”
Essha ta baka Mai harara ta nemi guri ta zauna..
Yayi murmushi yace” oho dai ni dai bazan dukuba”
Essha tayi dariya tace” Allah Amir ka rainani”
Yace” Allah sis acire maganar wasa fada zakishs aguri Daddy, balle yanzu da muka koma uke gabadaya ba kamar lafia bane, zai Dan Sha wuya kafi yasamu friends dun kisa baya ji yaresu Suma basa ji nashi, kiga ko shine da Sha wuya, Anya ma yasa wasu abubuwa aka kasashi kuwa?
Tace” gashi gaban ka tambeyeshi”
Yace” okay tom, boy bara nafara ma Dana India, what is the name of your prime minister ? Nasan Wana zaka sani”
Sadik yayi murmushi yace” *NARENDRA MODI*”
“Toh Who is the current president of Nigeria? Amir ya sake jefo Mai wani tambayar
Sadik ya sake saki wani murmushi Yana su sa Kai can yace” *President *MOhammadou Bu’aali* “
Daga Essha har Amir duk suka fashe Mai da dariya, sadik ya Tsaya shiru Yana ya tabe fuskar Kamar zaiyi kuka, gani haka Amir ya dakata ya rugumeshi yace” No boy don’t cry, u tried, that’s the correct answer”
Sadik yadago yace” really?
Amir yabashi amsa da “yes boy”
Sadik yace” then why are you laughing? Ya fada kamar zaiyi kuka. ….
Amir yace” am laughing at your pronouciation, it’s Muhammadu Buhari, not Mohammadou Bu’aali, give me five ”
Yayi murmushi ya Mika mishi hannu suka tafa…
Amir yasa hannu a dimple na Sadik yace” sis Allah boy Kama yake min da wani, kamarsu ma har ta baci “
Essha daji haka ta Mike da sauri a tsorace murya na rawa tace” Amir jiramu ake, abun na hada ma sadik baso yasani, tashi muje sauri nake” tayi haka ne da ta kawar da zance, kafi su Mike ma hartayi waje, jikita har Yana Bari, Amir zaiya tsareta da tamboyoyi tasashi Sarai.
Tanaji murya sadik na sallama nannyshi, Yana mata godiya Khirr da ta hadamai, tana kallosu suka fito Amir rike da hannushi, daya hannu kuwa food flask ne ya rike na Khirr da nannyshi ta zuba Mai.
Suna shiga ta tada motar sai gida, Tana Gama parking sadik ya bude ya sauka da saurishi Yana kwala ma Arudhati Kira tazo taga uncle Amir.
Essha da sauri itama ta sauka tabin bayashi tace” wait Kar kashiga Ina zuwa”
Taja Amir suka shiga ciki tabarshi a tsaye, suna shiga suka tarar da yara da manya acika sosai harda colleague nata naguri aiki, yara dukasu sanye suke da birthday cap na pj masks, Pooja ta karaso tace” Ina sadik Dr?
Essha tace” surprise party ne basan yasani”