Al-Ajab

DA ƊUMI ƊUMI: An sace kayan fitar angwanci na wani ango a Kano.

DA ƊUMI ƊUMI: An sace kayan fitar angwanci na wani ango a Kano.

Daga Rufa’i Abdurrazak Bello Rogo.

Ɓarayi sun fasa shagon wani tela, mai suna Ali Isma’il a unguwar Kundila a jihar Kano, inda su ka yi awon-gaba da shaddoji, yadika da sauran kayayyaki.

“Majiyarmu ta jiyo cewa da ga cikin kayayyakin da ɓarayin su ka sace har da set shida na wani ango, mai suna Junaidu Muhammad duk a nan unguwar ta Kundila.

“Wannan lamari ne kwanaki uku kafin ɗaurin auren Junaidu, inda ya shaida wa manema labarai cewa ya kai ɗinkin kayan ne domin fitar angwanci.

“Da ya ke wa da manema labarai, shima telan, ya ce ya tashi da safe ne dai ya tarar an ɓalle shagon na sa an kuma yashe kayayyaki sama da set talatin na kwastomominsa.

“Kaya ne a aka dauka dinkakku da waɗanda ba dinkakku ba. Sun haɗa da shaddoji da yadika. Dinkakku da aka sace sun kai set 16. Wadanda ba dinkakku ba kuma sun kai sama da set 30,” in ji Isma’il.

“Daga ciki, a cewar telan, har da na shi wannan ango da ke shirin kece raini kafin da kuma bayan bikin nasa.

“Sai dai kuma telan ya ce ya ji daɗi sabo da duk kwastomomin da abin ya shafa, har da shi angon, sun ɗauki na damo.

“Yanzu haka dai jami’an tsaro na yankin unguwar sun ce sun fara gudanar da bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button