DASHEN ZUCIYA

*******
Bisma ce kwance akan kafar Nuru suna sha’aninsu suna hirar soyayya, tajamai gemu yaja mata hanci, labari suke suna dariya duk Wanda yagansu yasan cewa ma’aurata ne masu cikeda wadatar zuciya, karfe 12:00pm daidai ne Bisma ta tashi tace “my husband bari inshiga kitchen inyi mana lunch kasan anjima munada manyan baki kasan yan gidanku xasuzo yakamata mu kammala komai in time” kallon ta yayi ya sunkuceta sai kitchen, tare suka fara aikin har suka gama anan bisma tagane cewa mijin nata is a nutritionist duk wani abun Gina jiki yasanshi saboda wata makarantar cooking and pastries dasukayi attending Lokacin suna kasar America, haka yayita kai abinchin dinning wayarta ce tayi kara lokaci guda nuru ya matsa kusa Bisma dake kitchen tace “my kadauka pls am busy ryt here”
Haka NURU ya amsa yace “Hello”
Daga dayan bangaren yaji ance “Doctor here is an emergency and we seriously need your help” sai aka kashe wayan NURU yashiga kitchen ya kalleta yace “baby your help is needed at the hospital Call din danayi receiving kenan”.
Dagowa tayi ta karewa Nuru kallo taga kaman ransa baiso ba, “tsame hannunta tayi tsam daga gyran fruit din datake tace “Honey lafya naga duk ranka ya baci nasan is a mistake sunsan cewa hutun one month aka bani kuma am not the doctor on duty pls saki ranka bari na kira dean din asibitin inji daga bakinsa, falo ta wuce komai na jikinta kadawa yakeyi nuru kallonta kawai yakeyi yarasa meyasa komai na bisma yake burgeshi ta dauki wayar ta zauna ta kira number nan sukayi magana akabata hakuri akace taci gaba da Honeymoon dinta.
Mikewa tayi taje ta janyo hannunsa tace, “you are a blessing to me and you are my world darling I can be a full wife without your support my dear I need you support towards my profession I need to help the needy as wel the sick people pls” tafadi suna shak’ar numfashin juna.
Rungumeta yayi kwarai a kirjinsa tace “karki damu bazan barkiba my love you mean the world to me bana fatan kirigani mutuwa nafiso rana daya ta rikemu mutafi chan muzama mata da miji a aljanna, abunda banaso shine yadda kike damun kanki da karatu kinsan cewa bawa yana bukatar Hutu ina sonki bisma idan nace miki your are the breath I breathe pls kice kin yarda” yafadi tareda zura mata harshensa a kunne lokaci guda tayi wani ihu ta tashi tana yimai chakulkuli, tuni suka fara zagaye acikin wada taccen falon su.
Nuru Kullun kara sonta yakeyi saboda kula datake nunamai, haka suka tashi sukayi wanka tare hatta abincin tare sukeci kwano daya chokali daya kofin shan ruwan su dayane, haka suka fito daga wanka suka fara shiri haka Nuru ya zage yana shafa mata mai itama haka tayi mai hatta kwalliya yace shizai mata haka ya chab’a mata kwalliya dukda bata mata fuska yayi amma haka tace “my Wallahi baka iya kwalliya ba amma kasan me” nuru tace “Ah saikin fadi”
Tace “Am proud of my husband zan iya zuwa gaban kowa in tsaya da wannan kwalliyan saboda ba kudi na biyaba miji na yayimun”.
K’washewa NURU yayi da dariya tashi tayi ta fito mishi da kaya ta shirya shi tsaf, itama haka yaciro mata kaya masu kyau da tsada haka taci dauri falo suka koma suna tsumayen bakin su, da NURU ya kalli Bisma saiya kece da dariya ita kuma tawani poze,
Suna cikin guje gujene sukaji ana knocking Bisma tana nizan bude nuru yana shizai bude abun mamaki suna budewa sukaga mahaifiyar Nuru itada yan’uwansa da yan’uwa tuni kunya ta lullube Bisma tayi bayan kofa tana musu sannu da zuwa.
NURU yace “hajiya wai kunyarki takeji”
Mahaifiyar nuru tace “meye na kunya don kina wasa da mijinki ai wannan ya nunamun cewa Nuru yana cikin kwanciyan hankali kuma Allah zaiyi miki albarka gaba daya aikace Amin suna shigowa.
Bayan sun zaunane bisma tashiga kitchen takira Hamdan yazo shima ya tayata daukan kayan ciye ciye aka daura musu akan center table, kallon Bisma sukeyi irin kwalliyan datayi innar Nuru tace Bisma halan dai mai gidanne yayi miki wannan kwalliyan ai tuni suka bushe da dariya, bayan sun gamane aka yiwa su hajiya iso zuwa dining amma Sam sukace a kasa zasu Zauna haka aka shimfida musu tabarma aka kawo musu kayan abinci.
Suma sukasa a kwano daya hajiya tace ma Bisma “ga chokali kici abinchin dashi,” NURU yace “hajiya da chokali daya mukecin abinchi saboda karawa zuciya yadda so da zumunchi”
Hajiya tace “kwarai kayi dabara harka tunamun da baya Allah yayiwa annabi daraja” akace amin Bayan sun kammlane akayimusu fada sunji dadii kwarai daga bisani sukace zasu tafi haka bisma ta kwashi Wasu a motarta NURU ya kwashi Wasu, amma saida sukayi tsiya bisma tana ita zata dauki hajiya Nuru yana shizai dauka daga karshe dai NURU yaci girma.
Bisma bakaramin guri tasamu a dangin nuruba, saboda irin shedar dasuke mata, ga Albarkan iyaye gana iyayen miji gana miji sannan dadin da dawa gana jama’an gari dole Bisma tayi farin jini saboda dadi Bisma saida tayi kukan dadi.
[2/12, 3:45 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
2⃣4⃣
_*This page goes to you ILILEE am sending my Condolence???? due to the lost of our beloved and Dearing Grandpa, May Allah have mercy on him, may Allah make his final abode to be Aljanna FIRDAUSI Amin*_????????
*RIGAR GEIDE*
*********
Ya k’walam ce zaune tana kullewa Baitu K’oren nono da fura tana kaiwa kasuwan datake ci duk ranan Asibi, yarinyace son kowa kin Wanda yarasa, saboda kyawunta zan iya cewa Kamar yar India amma saidai cikas guda tana dauke da lalurar ciwon zuciya, dazaran ciwon yatashin mata sai tayi kaman bazata rayuba dayawa yan garin suna masifan sonta amma Yarinya ce Mara hayaniya, wacce bata damu da rayuwan mutane ba.
Baitu! Baitu!! Baitu!!!
Kiyi maza kifito mana lok’aci yana k’urewa, haka tafito tana tafiya cikeda natsuwa ta dauki k’waryar nono takama hanya sai kasuwa, Jood’a yana tsaye Wato mahaifinta shida wani abokinsa dake zuwa daga birni, ta gaidasu ta wuce.
Bayan wucewar Baitu ne bakonnan yace “Jood’a wai har yanzu yarinyarnan tana fama da wannan ciwon?”
Jood’a yace “kwarai kuwa amma kwana biyu ciwon bai tashiba, kasan dazaran ranta ya baci shikenan zamu rasa gane kanta”.
Bakon ya jinjina kai yace “Toh tabbas yakamata kudinga zuwa birni ganin likita saboda wannan ciwon nata yana bukatar kulawa na musamman, sannan daganin kwararrun likitoci”
“Kwarai maganarka haka take zamuje insha Allah” haka sukayi Sallama ya wuce.
Kamar yadda Baitu ta saba dawowa da wuri haka ta dawo amma daganinta batada lafya sosai haka ya k’walam ta amshi Koren nonon gaba daya ta saida bamu koh barbede, haka ta nemi guri ta zauna tana numfarfashi tana cije baki, Baitu tayi karfin hali tace “Ya k’walam ina cikin wani yanayi inajin ciwona zai tashi”…….
kafinta gama magana ta fadi a sume.
Cikin tashin hankali ya k’walam da Jood’a suka Mike suna kuka haka, ya goyata har bakin titi gashi yakai kimanin kilometres daya daga kauyensu zuwa bakin titi, saboda kula da sukeson bawa yar Tasu k’waya daya, sun isa bakin titi duk motar dasuka tsayar sai taki tsayawa hankalinsu ya dad’a tashi, da kyar suka samu wani mai akori kura ya daukeso akan kudi naira Dari biyar zuwa garin Gusau, ya k’walam kuka kawai takeyi abun saiyaba mai karatu tausayi.