DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

GUSAU
************
Don nikaina saida nayi kuka saboda yadda idanunta suka kakkafe, cikin asibitin FMC suka shiga babu Wanda ya kallesu duk Wanda ya k’walam tagani da farin kaya saita ruga da gudu tana neman taimako amma babu Wanda yakeda tausayi cikinsu, kwatsam saiga Bisma tafe take tana amsa waya dagani da NURU take waya saboda shima ya koma bakin aikinsa, tuni ya k’walam ta ruga tace “Baiwar Allah kayimun agaji yarona ba lafya gashi chan kwance bayako motsi”

Bisma ta kalleta tabata tausayi tace “Baba kidaina kuka muje” inda Bisma taga jikin yarinyar taga yadda aka barta k’wance a kasa taji ranta yayi dubu ya baci ta kwalawa nurses din kira tace “Abunda bazan lamuntaba kenan wulak’anta patient akan wannan carelessness din zan iya barin wannan asibitin akan haka, maza ku dauketa kukaita kan gado”
Haka suka dauketa ranga ranga, “Bisma tace baba kiyi hakuri zaa dubata kuma duk yadda ake ciki zakuji sakamako”.

Haka ya k’walam ta rungume hannu shiko jood’a rikeda sandarsa, abun duniya ya isheshi, “Ya Allah Kaine gatana ka bawa yarona lafya kaba Baitu lafya”
Cikin Dakin Bisma ce tsaye tana bincike akanta ansata acikin na’ura mai kwakwalwa, tuni ta nuna cewa zuciyarta ce ke cikin matsa nancin yanayi.

Bisma hankalinta ya tashi ta juya tacewa nurses din “Yarinyarnan tana cikin mawuyacin hali, batasan me duniya take ciki ba, tabbas zuciyarta tana buk’atan ayimata aiki kila musamu nasara.

Tashi tayi tafita tana fita ya k’walam tayi saurin cewa “likita lafya naga ka fito rai babu dadii karkace mun Baitu ta mutu”
Bisma ta dago idonta jawur tace “kubiyoni Office” haka jood’a yabi Doctor Bisma aguje, har cikin office zama tayi nima nabisu hoton Bisma da NURU ne akan tebur dinta sunyi masifar kyau kaman larabawa, Doctor Bisma tace “Gaskiya sai anyi mata aiki saboda zuciyarta gab take da daina aiki saboda ciwon dayaci zuciyanta”.

Cikin tashin hankali Jood’a yace “likita nawa akeda bukata” Bisma taga idan tace mishi naira dubu dari da hamsin ake nema ina zasu sameshi?
Tace “Malam kudinku naira dubu darine kacal”.

Jood’a yace “Toh likita zani gida inga yadda za’ayi Zan samo likita Baitu itace kadai yata a duniya banida kamarta baitu mai ladabi ne da biyayya Baitu bai taba batamum raiba likita karya mutu likita” haka ya k’walam itama take kuka tana ji aranta Baitu bazata Rayuba.
[2/14, 7:57 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

2⃣5⃣

Haka jood’a ya kama hanyan zuwa rigar Giede don saida wasu k’adarori nasu, da isarsa rigar su ya tadda babu shanu babu kowa cikin rigar dagani barayin shanu sunyi awon gaba dasu, jood’a yashiga matsanancin hali inda ya duba gabas da yamma kudu da arewa babu dabbobinsu koh daya karshe ma an k’ona musu gari koh kukan tsuntsaye bakaji illah iyaka hucin zafi dayake tashi, ihu kawai yakeyi babu salati babu komai dayake suna cikeda tsantsar jahilci, haka jood’a ya koma cikin birni cikeda tashin hankali, yaje yake sanarda ya k’walam abunda yake faruwa gaskiya sun shiga cikin tashin hankali, “Yanzu ya zamuyi? Yanzu ina zamu sa kanmu dabbobinmu sune rayuwanmu, yanzu ina zamu samu kudin ayiwa Baitu aiki nasan cewa baitu mutuwa zatayi matukar muka kasa samun kudin da za’ayi mata aiki bara zanfita jood’a rayuwar Baitu tafi komai mahimmanci a rayuwa”

Haka suka baxama cikin gari Neman taimako amma babu maison taimaka musu, kofar gidan wani Alhaji ya k’walam ta tsaya ganin zai shiga da Motarsa tace “bawon Allah taimako nake nema yata batada lafya tana kwanshe a asibiti kuma aiki za’ayi mishi a zuciya Dan Allah ka taimakeni yadda Allah ya taimakeka, Alhajin nan ya kalleta sama da kasa ya hankadata gefe yace “Aikin bazan no koh zan baki kudi bazan bayarba jiki wata bakauya dake aini yan mata Nike bawa kudi subani abun dadii”
Wasu yan’matane sukazo wucewa susu shida kowacce daganinta kasan cewa tasha kudi ta koshi komawa sukayi da baya yayinda yaci gaba da cewa “maza kibarmun kofar gida kafin insa a daukeki cik” haka ya k’walam ya mike tana kuka zuciyarta cikeda tsanar wannan bawon Allah, “meyasa Wasu basuda imane maiyasa wasu sukadau talaka Mara yanci maiyasa mai kudi yakejin kyashin yiwa talaka Alkhairi nagari kadanne acikin duniyannan amma wata rana kaima saika nema wajen wani tunda ka wulantani”.

Yan’matan nan su shida daya tayi gaba wajenshi tana kwarkwasa tana fari da ido lokaci daya hatsabibin Mutuminnan yaji bazai bari wannan kyakkyawan yarinyar ya wuceshi ba, kallonta yayi yace “Lafya baby me kikeda bukata yanzu mushiga cikin gida inyi miki” Yumna tace “Menakeso banda kai inji kana abunda bora mata samu wajen mijinta inji ina Sosa maka tsakiyar kai” tafadi tareda Jan gaban rigarsa, tuni ta wuceda imaninsa, yayi horn mai gadi ya bude mishi kofa haka yaba sauran yan matan shigowa amma sai suka boye, mai gadi yace “wai yau Alhaji zaici banza har mata shida inama zai mikomun uku nima indan maida mugun yawu” nidai Humairah saboda dariya saida na durkusa.
Suna shiga ciki da yumna sauran suka kama mai gadi suka daure shi tamau, biyu suka tsaya tsaron mai gadi sauran suka shiga ciki, Alhaji tuni yacire kayan jikinsa daga shi sai dan kamfai Wanda akafi sani da boxer, ya ajiye uban tumbi kaman mai cikin wata Tara “motso kusa mana baby yana cikin faden haka sauran ukun suka shigo daya daga cikinsu da bindiga, lokaci guda yaji mugun tsoro Kabira tace “Irinku mukeso azzalumai Wanda matan banza ne kecin kudinku matanku suna chan kun barsu da yunwa koda kanzan tuwo toh yau sai asirinka ya tonu haka Shantel ta kwabe kaya dayake cikinsu itace kabila koh ince crista.

Daga ita sai bra sai pant haka Ubaida tafara daukansu hoto kuma sukasa shi dole saiyayi dariya alamun yana holewa ya ya’iya haka yadinga bashe baki bayan sun kammala ne, Aisha tace “ji yadda ka wulakanta wannan baiwar Allah Allah kadai yasan halinda yarta take ciki amma ka kasa taimaka mata toh yau kashinka ya bushe,
Haka suka umurce shi daya basu kudi sannan ya rubuta musu check na naira miliyan shida haka suka daureshi suka dauki brief case dinsa suka kara gaba sannan sunyi alkawarin saisun tonamai Asiri yumna kadai zai iya ganewa acikinsu itama tasan abunda ta taka shiyasa bata rufe fuskarta.

Tuni sukabar gidan tareda wayoyiinsa suna cikin tafiya suka hadu da ya k’walam a karshen layi tana kuka tana share hawaye haka sukadau kudi naira dubu Dari da hamsin suka bata suka wuce tundaga ranan sukabar garin Gusau zuwa wani garin, haka ya k’walam tadinga jin dadii tana murna taba shimusu albarka haka takoma asibiti da karfinta tuni aka fara shirin aiki nanda kwana uku, haka jood’a yadawo ransa babu dadi, saiyaga ya k’walam tanata dariya zama yayi yaga tanacin abinchi yace “Ina kika samu abinci munata lafiyan baitu?” Nanta bashi labari shima yabata labarin irin wulakancin dayasha wajen masu hannu da shuni Wasu har cewa sukai sai sunyi lalata dashi sannan zasu bashi kudi shikuma bazai iya sabawa mahaliccinshi ba.
[2/14, 8:13 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button