DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Ya k’walam ta zare ido cikin ridewa tace “likita acire zuciyana asawa baitu ta rayu dan Allah, itace kadai ta ragemun cikin yaya goma Dana Haifa yarana wabi sukeyi, mai zai hana acire nawa asamata ita Yarinya ce nikuma tsufa yazo” jood’a yakasa cewa uffan Saima jingina dayayi da bango tana salati wannan wace irin jarabawa ce Allah ya daura mana Allah kabamu ikon cin wannan jarabawan” amin ni Humairah nace.

Anfito da baitu Bayan awa uku, idonta a bude tana Dariya tace cikin muryan Mara lafya, inna “Kinga naji sauki Fatana in warke inci gaba dakai miki fura kasuwa da nono inje rafi in debo miki ruwa inje daji inyo miki itace, takoma ga mahaifinta baffa kaima in ba bisashe ruwa in share maka Daki banaso Ku wahala dayawa a duniya, Bisma da sauran likitoci suka tsaya suna kallon baseerah irinta baitu, Bisma tayi Dariya tace
“nikuma ne za’ayi mun?”

Baitu tace “Adu’a itace a tsakanina dake Adda, Kinyi iya kokarin ganin kin ceto rayuwata lokacin danake Neman taimako, Allah ubangiji yasa kigama da duniya lafya, irinku kadanne a duniya Halinki nagari zai biki har zuwa karshen rayuwarki, Insha Allah karshenki mai kyauce likita”.

Tuni Bisma tafara kuka maicin rai bata taba jin wani yanayi irinna yanzun ba, Jitayi ana share mata kwallan da kyallen handkerchief kuma kamshin turaren mijinta taji, yana cewa “Ki kasance jaruma bamai saurin kukaba yin hakan zaiyi saurin k’arya zuciyar Mara lafya, Bisma kemai nasara ce sannan ki godewa Allah da ma’aikinsa, mijinki yana yabonki duniya tana yabon aiyukan Alkhairinki ai kin gama da duniya lafya saidai muce Allah ya kyauta ta karshenmu.

Bisma ta juyo tana kuka tana Dariya tarasa murna takeyi koh bacin rai, Kallon Baitu tayi tace “mijina koh wace uwa tana burin Rayuwa da yayanta tabbas inajin zafin da uwa takeji Lokacin da takeyi yayanta Adu’a bayan ransu, koh a yanayin ciwo uwa tana hana kanta bacci saboda ta kulada rayuwar yayanta, uwata tana kincin abinci taba yayanta dukdan yaranta su rayu, lokacin da uwa taji kukan danta koh a ina zuciyarta kuna take, meyasa yaran baxasu rayu sujikan iyayensu ba mai yasa yaya suke fand’arewa iyayensu, meyasa yaya suke ciwa iyayensu zarafi a bainar jama’a kaico da Wanda baya tausayin iyayensa kaico ga Wanda yakasa bawa iyayensa kwanciyan hankali”

Kukane yaci karfin ya taci gaba da cewa, da ace yayanmu aka daurawa nauyin iyaye Wallahi Wallahi damu iyaye mun shiga uku da yawancinmu bamu raye, don dayawa yaya bazasu Goya iyayensu ba, ba zasu kici suba iyayensu ba Allah ka bawa duk wata uwa karfin zuciya wajen hakuri damu yaya” kowa yace Amin.

Nan kowa ya watse Bisma tace “kubata abumai ruwa Mara zafi zuwa gobe kila anjima abokin aikina zaizo gobe bazan zo ba, ta kalli baitu tace Allah yabaki lafya kinji,
Baitu tayi saurin cewa “Likita yaushe zan bar wannan asibitin mukoma rigarmu nayi kewan gida kwarai?”
Nuru ta kalli yarinyar ta burgesgi Bisma tace “My king tambaya takeyi?”
Nuru yace
“kece da bada amsa ai”.

Bisma tace “Insha Allah nan bada jimawa ba zaki bar Asibitin kije kitaya inna da baffa aiki”
Murna a wajen baitu baya misaltuwa Bisma tace “Kada Ku yarda wani Abu ya bata mata rai kuyi kok”arin sata Dariya sannan ta dawwana acikin farinciki” suka amsa da toh.

Rayuwa mai dadi haka nuru suka koma gida suka ajiye motarsu, waya suka samu daga wajen ruma cewa Dan Allah Bisma tazo yan uwan Hamdan zasu kasheta, bisma tace “Sunyi kadan my king muje mota tashiga shidai bita yayi suka fada cikin mota sai gidan su Hamdan da isarsu cikin zafin nama bisma ta fada falo sunyi mata ligi ligi ga ciwon ta yak’ara tsananta ga karamin ciki ai kwance suka tadda Ruma kelaye cikin jini wani kara bisma ta fasa tace “kun kasheta cikin jinin ta fada tana jigjiga Ruma amma batakoh numfashi, ka yan’uwan Hamdan tsaye suna huci tuni NURU yakira Hamdan yakira gida Shinkafi yasanar dasu.
Bisma wani kukan kura tayi ta shakesu tace matukar Ruma ta mutu sainaga bayan danginku Wallahi saikun talauce don kara daganan har kotun manta Sabo saimunje saku ta watsar dasu asibiti suka kwasheta sukakai abokan aikin bisma su suka tsaya akanta saboda wani irin matsanancin ciwon kai ke damunta sai jiri take gani hamdan yashigo asibiti kaman mahaukacin zaki ana sanar dashi cewa cikin da Ruma take dauke dashi ya fita jingina yayi jikin bango yace “Haka Allah yaso sake Ruma Allah ubangiji kaba ruma lafya kabamu masu amfani”

Kowa saida yaga kokarin Hamdan a yadda ya shigo cikin asibiti a hargitse lokaci daya yayi tawakkali ga Allah ya yarda shike badawa ya amsa a Lokacin dayaso.
Inda nuru yake rungumeta da Bisma ne tana kuka yace “Kiyi hakuri bisma Allah shike komai a yadda yaso”
“Dakata kadau mataki koh koh indauka a hannuna?” Cikin rudu hamdan yace
[2/16, 2:44 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

2⃣9⃣

“Na kira su hajiya na sanar dasu amma batace dani komai ba nakira alhaji na fadamai shima shuru yayi ya kashe wayar kinsan irin zaman da akeyi na doya da manja” Bisma ta dafe kai tace
“ai case bata kareba yanzu zan sanarda hukuma ayi mai tarariya” Hamdan ya rude waya kawai bisma ta dauka takira Acp Bello ta sanar dashi batareda bata lokaci ba suka isa gidan su hamdan.
Hamdan ya kalli NURU yace “Dan Allah kasa baki kar a kama kannina”.

NURU yace “Kanaso kacemun kafison kanninka akan ran matarka? Oh Hamdan banga laifin yan’uwanka ba Dan sunzo sun Daki Ruma da goyon bayanka kuma kaima saika fuskanci hukuma” tsaki nuru yayi yaja hannun matarsa suka shiga inda Ruma take Yadda ta koma abun tausayi cikin yan lokaci ta rame takoma Kamar bulala, bacci suka tarar tanayi yan gida duksun hallaro da wayanda zasuyi jinya, bisma kuwa zuciyarta ce ke tashi bayan sun gaisa ne Ummi ta umurci bisma dataje gida don taga kaman yar tata takamu.

Haka Nuru ya rike hannun bisma har gida, ya bude mata murfin mota ya dauketa cik har cikin gida sannan ya ajiyeta, kofin tea ya hado mata mai zafi tasha gaba daya ya amoyo mishi ajiki sai kakari takeyi haka, nuru dukya rude yarasa mezai fara yiwa bisma, gashi Da gashi sai ita a gida, abin ne gwanin tausayi.
Tissue ya samo ya goge mata baki tareda yimata sannu koh magana bata iyawa, daukanta yayi cik zuwa toilet ya gyra mata jiki shima ya gyra nashi, suka shiga Daki ya taimaka mata tasa kaya harda sweeter saboda sanyi datakeji haka ya daura ta bisa gado ya lullubeta da bargo.

Fita yayi falo ya fara kwashe aman datayi ya gyra koh ina yasa air freshener Dakin ya dau kamshi, sallama yaji yace Am coming budewan Da zaiyi yaga abokinsa Faisal yace “Abokina lafya naganka haka a hargitse?” Cewan abokin NURU.

Nuru yace “dole ka ganni haka my princess ce ba lafya amai tayi shine na kwashe nake gyara wajen”
“Lallai nema abokina kazama mijin tace mace kake yiwa yik’i haka ina aini baxan iyaba tab Wallahi kabi a hankali koh an jikama kasha”
NURU ransa yayi mugun baci yarasa abunda ke masa dadi arai yace “Dakata Faisal banason maganar sha shanci me kake nufi toh bari kaji Wallahi akan bisma babu abunda bazanyi ba yadda kake ganina yanzu kitchen zan shiga abunda takeso shizan dafa mata”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button