DASHEN ZUCIYA

Faisal yayi sarere, daman shi halinsa kenan mazigi ne makwangari, haka yakebi yake lalata auren abokansa amma dayake nuru yasan abunda yakeyi ya sakar mai da gwiwa, “Toh mijin hajiya ni nayinan sai anjima ka gaisheta idan ta farfado, Nuru saboda haushi bai iya cewa komai ba.
Nuru yashiga kitchen ya dafa musu abincin daza suci, bayan ya kammala yashiga mater bedroom dinsa ya tada bisma cikin dabara harta soma bude idanunta, murmushi tayi ta sakkoh riketa yayi saboda bayaso wani Abu ya sameta brush tayi sannan ta dauko abunyin test na ciki don duk symptoms din da takeji namai ciki ne.
Ilai haka tayi test din cikin ikon Allah yanuna Jan danja, dukda NURU baisan abunda yake nufiba amma saiyaga bisma tana murmushi shima saiya fara, juyowa tayi ta rungume shi hartana jin bugawan zuciyarsa, tace “My king da a asibiti muke da wasune zasu tayamu murna amma dayake likita ce da kanta ina maka albishir da cewa ina dauke da juna biyu Wato danmu nidakai”.
Wani ihun dadi NURU yayi yace “Wasu sun rasa gashi mu mun samu, don haka dole muyiwa annabi salati” haka sukayi NURU yaci gaba da shafan cikin haka bisma tadinga fama yau lafya gobe ciwo dukda bawani kwantar da ita yakeba, bayan kwana biyu aka sallami ruma amma sai akai shinkafi da ita saboda sai anyiwa tufkar hanci.
Baitu ce kwance bayan SATI ciwo yakici yaki cinyewa, bisma tace “Baitu dole ayimiki dashen zuciya gida” takoma da damuwan halinda Baitu take ciki NURU yace “princess gaskiya ki rage tunani akan patient dinnan wai ita kadaice kike dubawa? Haba gaskiya ki kula saboda lafiyarki data abunda ke cikinki, ko kuma ki ajiye aiki har saikin haihu”.
Cikin rudu da tashin hankali, Bisma tace
“My king katuna Alkawarin dakayimun akan cewa zaka tsaya tsayin daka ganin na comma nasara akan aikina amma meye na canza raayi katuna rai zan ce ta”
“BISMA dakata akanki da abunda ke cikinki bakida abunda zakice mini saboda dole kidaina zurfafa tunani”
Bisma tace karka damu my king ana dasa mata zuciya shikenan zan dauki Hutu pls kasaki ranka.
[2/18, 7:23 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
3⃣0⃣
_*This goes to basira one of our gigantic FAN Am here by saying my big condolence to you for the lost of our beloved brother may Allah forgive him may Aljanna firdausi be his final abode AMIN*_????????
Wani murmushi tasaki tareda komawa kusa dashi ta kwanta amma gaba daya zuciyarta tana wajen baitu datake fama da ciwo k’warai Wanda Bisma tarasa dalilin hakan, bayan sun kwanta bacci ne BISMA ta lallaba ta mike tafara jero salloli tana yima baitu Adu’a wacce Allah yabata iko, Shiko NURU wani
Bacci yakeyi.
NURU yana zaune a kujera bisma tazo ta wuceshi tana murmushi nuru tana daga mata hannu cigaba yayi da karanta jaridarsa, bayan fitarta ne yaji karar waya tuni ya dauka ganin lambar bisma hello shine abun da yafara cewa Wanda yakira yace kazo wajen DANGASKE NIG LMTD wata motace tayi hatsari kuma inajin matar dake ciki ta rasu cikin rudewa nuru yace whatt!!!!!!!
W firgice ta mike yana salati juyawan daxaiyi yagansa adaki bisma kwance kusa dashi, tanata bacci cikin kwanciyan hankali.
Wani numfashi yasaki ya koma ya k’wanta yana mai ajiyar zuciya, amma kuma tsoro fal da fargaba acikin zuciyarshi.
Ba NURU kadai ba hatta ni humairah saida zuciyana ta karaya.
Da asuban farko Bisma ta tashi taga nuru zaune ya nade hannu cikin gaggawa ta matsa kusa dashi tana “NURU lafya kake? Dan Allah lafya dagani bakayi bacci ba dubi yadda idanunka suka kumbura sannan sukayi ja pls my dear husband tell me wat is the problem?”
NURU ya dago sai jitayi hawaye suna zuba kamar daman jira suke tayi magana.
Bisma ta kara rudewa “Ga gayamun abunda ke damunka Dan Allah”
NURU ya fashe da kuka yana cewa “Bisma karki barni bazan rayu ba kece mahadin zuciyana bisma don go and leave me I know definitely am gone too” itadai bisma a rude take tarasa dalilin dayasa NURU wayannan kalaman gamida zubda hawaye.
NURU yace “Nayi mafarki Bisma mai tsantsar rikitarwa, idan kikaji tilas zakiyi kokawa amma nabarwa zuciyana banaso kiji abunda zai tada miki da hankali” bisma ta rikemai wuya tace “you most tell me wat is happening” tana jijjigashi tana kuka.
NURU yace “Nayi mafarki Allah ya dauki rayuwarki shiyasa kikaga ina kuka don tabbas da ace ba mafarki bane bisma wallahi da tuni na biki na kashe kaina bisma inacikin matsanancin tashin hankali”.
Bisma tayi wani ajiyar zuciya tace “Amma ka tadamun da hankali Wallahi, inace mutuwa akayi ka kasa gayamun, Wato kanaso kacemun tsoron mutuwa kakeyi? Toh Kasani “Kullu nafsin za’ikatul maut” dukkan mai rai mamacine kuma idan lokaci yayi babu makawa duk soyayyar dake a tsakanina dakai Kasani Allah daya haliccemu yafika sona kuma ina maraba da mutuwa akoda yaushe”.
Zare ido NURU yayi yana k’ara sautin kukan sa Wanda nikaina saida nakara karaya da kalaman bakin Bisma, nikaina saida na goge wasu hawaye.
“Bisma kiyi fatan mu mutu rana daya karki tafi kibarni lokacin danake matukar son mu rayu da juna Kituna kina dauke da farincikin rayuwanmu, nidake bisma rana daya zamu rasu”
Bisma tayi Dariya tace “Kamanta yadda mutuwa take raba d’a da mahaifa haka take raba masoya, ma’aurata, abokai harda aminai NURU ba’a mutuwa sai lok’aci yayi idan Lok’acin ka baiyi ba zaka zauna daram a duniya Fatana Allah yasa mucika da Kalmar shahada”
Amin yace yana karewa bisma kallo mikewa tayi ta dauro alwala tace “Mai tsoron mutuwa tashi maza kayi sallah kar tazo ta riskeka yanzu don arana mutuwa tana ziyartar kowani gida sau saba’in taga waye akan layi”.
NURU yace “pls chapter close naga kinaso kimaida abun wasa” haka sukayi sallah kowa yafara shirin tafiya wajen neman halalinsa
Bayan sun gama cin abinchi ta mike tace “Nina tafi pls karufe koh ina kila bazan Dawo ba” NURU yakara kallon Bisma yace “madam zolayan ya isa haka”
Haka tafita tana Dariya amma wani kallo takeyi wa NURU, fitanta keda wuya NURU yakirata yace “Amma shine kika kasa shan maganinki koh kuma kindauko gashi kan dinning”
Oh barina Dawo insha haka bisma ta Dawo cikin gaggawa tasha maganin ta kalli NURU tace “Hankalinka ya kwanta barima kaga inzauna” guri ta nema tafara kiran Ummi tana sanarda ita halinda baitu take ciki sannan ta tambayi lafiyar Ruma kusan yan’uwa saida takira ta mike tace “Na wuce” NURU yace “Allah ya kaiki lafya”.
Fitarda keda wuya nuru yakara kiranta yana cewa ki kulamun da kanki yana mata hiran soyayya sai Dariya takeyi, wani kara yaji Wanda lokaci Guda yadaina jin maganan Bisma yayi maganan duniya amma shuru kakeji, tuni ni humairah zuciyata ta tsinke na lallaba na ajiye wayata don ingarzaya ganin abunda ke faruwa.
[2/19, 3:39 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
3⃣1⃣
Cikin rud’ewa Nuru da boxer da yar vest ya fita mukullin mota kawai ya iya dauka, cikin sauri gaba daya jiri yakeji yana tunanin Tabbas Bisma ba lafya wani Abu so strange ya faru da ita daidai DAMJI yaga cin chirundon mutane saiya hango motar Bisma duk ta mokad’e ai da gudu yayi cikin mutane da mota bai saniba, fitowa yayi yaga bisma kwance shabe shabe cikin jini.