DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Gaba daya kamanninta sun canza, numfashinta dai dai yake fita, abun gwanin ban tsoro, “Bisma Ashe yau mafarki na zai zama gaskiya Ashe wannan ranan zatazo kaico duniya ni NURU inazan dosa?” Chicciban Bisma yayi zuwa mota kafin sukai ya sullube shima yafadi asume tuni Road safety, suka iso sukayi Kansu tareda jami’an tsaro Wato yan sanda Asibiti sukayi dasu FMC inda Bisma take aiki.

Cikin asibiti, emergency aka shiga da Bisma inda likitoci da dama suka shiga rudani ganin ma’aikaciyarsu cikin mawuyacin hali, NURU kuwa ruwa aka yayyafamai yana fizga abarshi yaje yaga matarsa amma likitoci rirrikeshi sukeyi.

Emergency ward
Da kyar numfashin Bisma yadawo gaba daya dangi duk an sanar dasu asibiti yacika damkam ba masaka tsinke Ummi kuwa Adu’a kawai takeyi amma yadda ake sanarda ita halinda Bisma ke ciki tasan cewa sai abunda Allah yayi.
Nisawa bisma tayi ta bude idanunta inda sukayi jawur amma wani murmushi takeyi mai cikeda ciwo tace akira mata Ummi da hajiya da maifinta Dana NURU.

Cikin kankanin lokaci aka kirasu suka shigo, halinda Sukaga Bisma aciki ya firgitasu, jini yake fita ta hanci tabaki ta kunne amma da kyar aka samu na baki ya tsaya, kanta yabugu yayi suntum kaman gungumen dutse.

Kallonsu tayi tana Dariya tace “Iyayena kuyafemun iya lok’acin dazan diba kenan a duniya Ummi hajiya ngd ngd kwarai amma ayanzu inajin dani da abunda nake dauke dashi a cikina zamubar duniya, amma Inaso kuyimun alkawari guda daya” tuni iyayen suka russuna gareta suna kuka kidaina faden wannan maganan Adu’a yakamata kiyi muyi baki daya.

Daddy yace “kudaina mata kuka Adu’a tafi bukata a halinda take ciki, bisma takara wani murmushi tace “daddy kuyimun alkawari zakuyi abunda nakeso, bayan raina daddy inaso ayi gaggawan cire zuciyana adasawa Baitu saboda tana matukar bukatar ta, sannan Inaso NURU ya auri baitu ya riketa amatsayin mata kuma amana ce nabashi”

Cikin Rashin fahimta daddy yace “Wacece kuma baitu? Yazaayi a dasawa mutum zuciya? Kuma na matacce?
Daddy ya kalli Bisma yace bazaki mutu ba insha Allah”.

Daddy kenan mutuwa tazama dole akan kowane bawa Fatana kuci gaba dayimun Adu’a bayan raina” tana gama magana aka umurcesu dasu fita koh minti biyar basuyi da fitaba jini yakara ballewa ta hanci ta baki, likitoci sunyi iya kokarinsu Amma fah abun yaci tura haka Bisma ta dinga salati ga ubangijinta har lokacin da rai yayi halinsa, ni Humairah nashiga tashin hankali bani kadaiba duk wani masoyin Bisma babu Wanda yafado mun arai sai NURU.

Haka likitoci suka shiga tiyata aka cire zuciyar Bisma akasawa Baitu, lokacin NURU yasamu ya balle babu Wanda ya iya kamashi cikin inda bisma take yashiga yaga an lullube mata fuska da wani kyallen asibiti, wani shaka ya kaiwa likita saida mutane fin ashirin suka kwaceshi, “Likita ka kashemun mata you have made a big mistake arayuwarka wallahi Shari’a dani dakai har abada, bisma wake up pls this is not the right time to go wat abt our baby shikenan”
Surutai yakeyi marasa kan gado haka kowa cikin dangi yake kuka garin shinkafi yacika damkam, ya k’walam kuwa surutai kawai takeyi har saida aka kaita inda akesa masu tabin hankali saboda mutuwar ta girgiza kowa harda ni Humairah Bashir Melody.

Dakin mijinta aka maidata akayi mata duk wani abunda ya kamata ayiwa mutum musulmi mumini, Wato sutura gidajen radio haka aketa sanarda rasuwar Bisma, haka mutane daga shinkafi sukayi zuga zuwa janaza mutanen Dana gani saida kaina suka juya.

Harka shirya Bisma jini yana zuba gawani murmushi afuskanta kaman tayi magana, NURU dai yana asibiti amma cewa yake abarshi yaje yaga bisma, amma ina saboda halin dayake ciki.

Fitan likita keda wuya NURU ya girgide, duk wani Abu na Dakin ya fita ya tare mai mashin sai unguwarsu, yana shiga unguwar ana fito da gawar Bisma wani kukan kura yayi ya amshe makaran tuni yafara kwanceta amma akayi NAMIJIN kokarin daukeshi yana ihu abar mai bisma bata mutuba.

Haka akayi mata sallah sai makabarta haka aka kaita makwancinta tareda Adu’oi daga bakunan iyaye masoya da abokan arzuka, haka aka kai NURU asibiti inda yake amsan kulawa daga kwararru, amma nuru yazama tamkar rakumi da akala ba umm ba um um, yakoma tamkar Kurma rana daya NURU yazama tamkar kara haka yaci gaba da zama a asibiti har tsawon kwana bakwai
[2/20, 7:05 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣2⃣

Baitu kuma tana samun kulawa daga wajen likitoci kwararru, har daga makotan asibitoci saboda itace mace ta farko da aka taba yiwa DASHEN ZUCIYA harta samu kanta batareda wani mishkila ba, ya k’walam kuwa tafita hayyacinta saboda mutuwar Bisma ta girgizata bayan ta Dawo hayyacinta ne aka nuna mata inda Baitu take k’wance tayi murnan ganinta amma sai kuka yake Neman cin karfinta.

Tuni likitoci suka fitar da ita saboda baitu bata bukatan komai a yanzu face kwanciyan hankali, haka iyayen bisma suke jigila da Baitu daga abinchi zuwa magani jood’a kuwa yanachan dashi ake amsan gaisuwa, Nuru ne zaune akan Gadon asibiti hajiya tana yimai nasiha amma kaman badashi take magana ba kallonta kawai yakeyi kaman yau yasaba ganinta.

Haka likita ya sallamesu amma da sharadin kar a maidashi gidanshi saboda gudun kada ya tuna abunda ya rasa wato bisma, hakan yana iya haifar da matsalan dabaza’a iya magancewa ba, haka hajiya ta amsa dato.
Direba ne yazo ya dauke su suka wuce gida inda hajiya take kokarin sashi yin sallah Adu’oi dacin abinci.

Bayan kwana bakwaine gida aka watse aka koma shinkafi amma Ummi batabar Garin Gusau ba saboda baitu datake amana a wajensu, haka Ummi da hajiya Nuru suketa jigila akan baitu harta warke tasamu kanta cikin koshin lafya.

Ladabin da baitu takeyi musu shine ya dasa kyakkyawan alaka acikin zuciyoyin hajiyan nuru da Ummi mahaifiyar Bisma, haka ya k’walam da jood’a sukabi Ummi bisa sharadin Alhaji, ita kuma baitu aka barta gidansu nuru, saboda hakarsu tacinma ruwa na hada NURU da baitu aure.
[2/20, 7:59 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣3⃣

An shafe lokuta da dama mutuwar bisma tafara gushewa kowa yakoma walwalarsa kamar da amma kowa yasan cewa Anyi musu babban gibi Wanda suke burin samun wacce zata maye musu gurbin Bisma…… Ya k’walam dai tana gidansu Ummi inda take taimaka musu da aikace aikace haka jood’a mahaifin Baitu yakasance shikuma mai gadi Wanda kowa yake matukar alfahari dashi sau dayawa Nabil yakan kaimishi ziyara inda yake bashi labarai masu kayatarwa, haka mahaifin bisma ke kuladasu, saboda yadda bisma tabar duniya da burin faranta musu rai.

Nuru ne zaune cikin Dan k’aramin garden inda baitu ke tsaye a bakin famfo tana wasa da ruwa, kallonta nuru yakeyi amma gaba daya ba ita yake tunani ba matarsa kawai yake tunawa, wani Abu tagani yana motsi cikin ruwa dagudu tayi inda NURU tana ihu yaya zo kaga maciji yana tafiya acikin ruwa, ihunta ne yadawo dashi daga kogin daya Lula.

A firgice ya dago tareda wurga mata wani mugun kallo yace “Waike Baitu meyasa gaba daya rayuwarki a wasa zata kare kinsaba da zaman kauye uwa ba kwaba koh? Toh zanyi maganinki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button