DASHEN ZUCIYA

Zare ido tayi tana “kayi hakuri yaya NURU Allah dagaske maciji nagani shiyasa nake magana” daka mata tsawa yayi yace “Keep quite Yarinya sai zuba saikace wacce komai ya kwance mata” hannunta ya rike GAM ya dinga janta da sauri har cikin Dakin Hajiya su Ashwa kanwar NURU tabisu tana Dariya tace “yau kashinki ya bushe wajen yaya” gwalo takema baitu lokaci daya baitu tace atafau saita rama gwalon da Ashwa tayi mata.
Gaban hajiya ya ajiyeta ya dank’wafar da ita yana “Cewa Hajiya kinga wannan maikama dayan ruwa bataji sai tayi ta sani magana kaman ma da ganda take zuwa inda nak’e hutawa tak’e damuna”.
Hajiya tayi Dariya tace “Ai Baitu tayi mun daidai datak’e saka magana, tunda bakada aiki saina tunani maganinka kenan” NURU yasaki baki yana kallon hajiya itako Baitu bayan hajiya takoma tana mishi gwalo.
NURU yace “Hajiya Wato kin goyi bayan taci gaba da damuna Yarinya bakifi shekara goma sha biyu ba amma ki zaman ma mutane annoba”.
Hajiya tayi carab tace “Banaga annoba ba” ganin ran nuru ya baci baitu ta mike tayi wajenshi tace “Yaya kayi hakuri banida burin ganin ranka a bace nasan cewa Yaya bisma tana sonka sosai batason bacin ranka kayi hakuri bazan sake ba” shuru yayi yana kallonta cikeda kaunar Baitu amma yak’asa sa wata ya mace koda jaririya ce acikin ransa.
“Baitu karki damu kinji na hakura” Dariya hajiya tayi tace “Nuru yakamata ka koma bakin aiki hakan shizai sa damuwarka da tafi gaba daya”
“Hajiya damuwata bazata taba gushewa ba indai akan bisma ne na dinga tunaninta kenan har duniya ta nade, hajiya Nida aure har abada saboda babu wata mace dazata mayemun gurbin matata Bisma Wallahi babu”
Ashwa dake tsaye a bakin kofa tace “Yaya ga baitu wacce zuciyar bisma ke dashe acikin zuciyan ta, nasan zaka samu duk wani farincikin rayuwa a wajenta”
Nuru ya kalli baitu ya kalli hajiya yace “kar kucemun zuciyar bisma ce aka dasawa wannan mai kamada yan ruwa?”
Lokaci daya yafara fita hayyacinsa, tuni suka rude maganinsa aka dauko aka bashi tuni bacci yayi awon gaba dashi.
Wani ajiyan zuciya Baitu tayi tacewa Ashwa “Dan Allah kicema yaya yadaina cemun yar’ruwa aljana fah kenan?”
Hajiya Dan Allah.
Hajiya tace “Baitu karki damu zai daina wata rana ma matata zai dinga cemiki kedai ki k’wantar da hankalinki” kada kai tayi haka aka fara shirin sata a mak’aranta tundaga aji biyar na primary tafara kamar wasa Baitu akwai k’wakwalwa ga fahimta.
[2/21, 8:29 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
3⃣4⃣
Bayan shekara Biyar
Rayuwa takasance mai dadii saidai tsakaninmu da wayanda suka rasu Adu’a, Nuru ne zaune cikin falon gidansu inda yan uwa daga bangaren bisma da bangaren sa suka hadu don gabatar da muhimmiyar magana ciki harda jood’a da ya k’walam iyayen baitu.
Manya kowa ya hadu magana daddy yafara cikin nasiha ga Nuru na cewa yaxama dole NURU kayi hakuri kadauki komai ba komai ba ita Rayuwa dakake gani ta gaji haka kila wataran bani ba hajiya ba Ummi bokowa anan, don haka namiji majiyi karfi irinka bazai zauna zaman gauronci ba dole kanemi mata.
Haka kowa ya amsa da “kwarai dagaske”
NURU jinsu kawai yakeyi amma shi gaba daya babu aure a tsarin shi gani yake idan yayi aure kaman yaci amanar Bisma ne, mahaifin Nuru yace “Kuma dakwai wani Abu da muka Dade muna boyewa saboda kwanciyan hankalinka da daurewar lafiyarka, dak’wai wasiyya da bisma tabari, Wanda yin hakan shizai nunama duniya cewa kaimai tausayine da rikon amana ga wasicci”.
NURU dai yakasa cewa uffan illah iyaka murna dayakeyi, Allah yasa bisma cewa tayi inyi mata Alkawarin bazan sake wani aure bayan itaba dako naji dadii kwarai, Niko Humairah nace tab dakamar wuya gurguwa da auren nesa, daganin fuskan NURU a kage yake dayaji wace irin wasiyya ce.
Gyran murya mahaifin shi yayi yace, “Wato wasiyya ta itace indan na rasu a cire zuciyana Adasawa Baitu, wasiyya ta biyu itace baiyan raina kurike baitu da iyayenta amana sannan Mijina NURU ya auri Baitu a matsayin mata” dam kirjin NURU ya buga inhar mafarki yake yaci ace ya farka baxai taba iya daukan baitu a matsayin makwafin matarsa ba saidai a matsayin kanwa babu wata ya mace daxata maye gurbin Bisma.
Kowa NURU yake kallo an rasa me yake sakawa acikin ransa, “kai muke saurare me zaka iya cewa idan harka aminche toh baza’a jimaba zaa daura muku aure”
NURU hankalinsa ya tashi yace “Abba babu abunda bisma zata nema a duniya bare wasiyya bayan ranta ink’asa amincewa, na aminche”
Yana gama magana ya mike ya fita batareda ya waiga ba, kowa dake falon saida ya tausayawa NURU.
Fitansa keda wuya yaci karo da Baitu tanata karatu, dagani haddarta take bita, jitayi kaman ana kalonta tayi saurin juyowa, da gudu taje ta rungume NURU tace “yaya koda yaushe Alhaji koh hajiya suka kiraka sainaga gaba daya ranka ya baci kome suke gayamaka haka na bacin rai kasanar dani inje in basu hakuri sudaina don banason bacin ranka yaya”.
“Baitu kenan kinada tunani da hangen nesa shiyasa kaifin baseerarki take bani Sha’awa karki damu sunayine wai don insamu kwanciyan hankali jeki cigaba da karatunki yayanki zaije ya huta”.
Juyawa tayi takoma taci gaba da karatunta.
Haka aka watse ansa ranan biki wata biyu, lokacin baitu tasamu hutun makaranta.
NURU kwance yake babu tunanin dabayayi, Baitu tayimun karama a inkirata mata SS 1 fa take bazan taba Dan ganta bisma Da wata mace ba, noo I can’t dukda baitu babu inda tabaro Bisma a cikar kamala amma nooo baitu saidai kiyi hakuri bazaki taba zama mata acikin zuciyana ba saidai kizama mata a wajen zuciyata babu wani hakkinki baitu dazan iya saukarwa.
Baitu ce tsaye a bakin k’ofa duk maganan da NURU yake fada akunnenta suka kare, sallama tayi tana murmushi tace “Yaya kanata magana kai kadai har na shigo bak’asan nashigo ba tunanin me kakeyi kaketa kiran Sunana?”
A rude NURU yace “kawai k’yawawan dabi’unki ne suke burgeni shiyasa kikaxo acikin tunanina”.
Dariya baitu tayi amma tasan ba haka bane, “hajiya tana kiranka yanzu fah basai anjima ba”
Tashi tayi tafita tana wasa da hannunta gaba daya maganganun NURU kawai suke Dawo mata dukda kankantar shekaru tasan abunda yake nufi dakinta ta wuce.
NURU jiyayi zufa yana keto mishi, “banaso baitu tasan irin zaman dazamuyi amma sai gashi maganar danakeyi acikin zuciya harta fito, tashi yayi yashiga Dakin hajiya yayi sallama yanemi guri ya zauna hajiya dake fuskantar NURU tace “Ansa ranan aurenka wata biyu yakamata duk wani shirye shirye afara saboda baitu ta tare acikin gidanta” nuru yakalli hajiya yace “Hajiya duk haka bai tasoba ana iya daura aure ta zauna daku anan kafin zuwa wani lokaci saboda nasa gidan a kasuwa, dazaran ankawo kudin zan fara Sabo a wajen gida DARI” hajiya tace “Lallai nema NURU toh baka isaba matarka Dole koh kanaso koh bakaso ta tare acikin gidanka don haka Tun wuri ka canza Shawara”
Mahaifin NURU da yake kokarin wucewa yajiyo maganganun da hajiya keyi turo kofar yayi gamida yin sallama yace “Hajiya meye na tada hankali tunda haka yazaba mubishi yadda yakeso”
“Amma alhaji taya NURU zai yanke wannan Sha’awaran amma nasan maganinka tashi ka bace mum dagani kuma kayi gaggawan sanarda baitu halinda ake ciki don baxamuyi maka ciki muyi maka goyoba”.
[2/21, 5:19 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*