DASHEN ZUCIYA

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
3⃣5⃣
Haka NURU ya fice jiki ba kwari, ransa yake cewa ashe kam za’a mutu inhar shizai sanarda Baitu cewa zasuyi aure Allah shi kyauta, jiyayi ana gudu Ashwa ce tabiyo baitu na gudu, kawai tsayawa yayi yana kallon yadda baitu ke tsalle kaman wata biri, Ashwa ta kasa kamata yana tsaye ta shigeta OC dinshi duk yana kallon ikon Allah, da Ashwa ta gaji ta tsaya tana haki tace gaskiya ke Baitu Kamar Dan biri, dole kici inter-Sport idan mun koma school.
NURU yace duk kuzo nan, haka suke tahowa kaman wayanda ruwa ya cinye a gabansa suka tsugunna, kowacce idonta yayi kwal kwal zatayi kuka, “Kuna ganin har yanzu Ku yarane koh, kuna ganin tsalennan dakukeyi baxai haifar muku da matsala ba toh Wallahi Ku kuka dakanku randa za’a kaiku Dakin aurenku mijinku ya muku wulakancimaza Ku wuce marasa abunyi” baitu ce karshen tashi tuni yasa mata kafa ta fadi rijib a kasa gashi tasamu wani Hutu tayi wata hamshakiya kibar ta saita boye nonuwan dake dafe a kirjinta hakan yasa kowa ke mata kallon kwaila.
Idan kika sake guje guje saina ballaki, sakara kawai sannan idan kina yawo ba dankwali, ba gyale saina miki illah, wannan fuskar dakike takama da kinada kyau saina saba miki kamanni mai kamada yar ruwa kawai bacemun”.
Da gudu Baitu ta shiga Daki tana kuka, hajiya ce tazo wucewa ta jikin dakin baitu taji sautin kuka, bata tsaya ba ta fada ciki rumgumo baitu tayi taji temperature din jikinta ya hau, ga masassara datakeyi kamar bazata kai labariba a rude hajiya ya fito tana kwalawa NURU kira amma ina baimasan tanayi ba yafada kogin tunani tsundum, dadamai duka tayi tace “Saika tashi muje asibiti baitu ba lafya sai rawan Dari takeyi”.
Cikin sauri ya mike mukullin mota ya dauko, cik yadauki Baitu gata da shegen nauyi hajiya tashiga cikin motar itama suka wuce asibiti, private sukake nan akayi mata gwaje gwaje, aka sanar dasu cewa Tabbas tana tattare Da damuwa, acikin zuciyanta kuma ga zazzabin cizon sauro dake dumunta, hajiya ta razana k’warai don bataso taji ance wani Abu zuciya don baitu bataji da dadi ba.
Baitu dai gata kwance sai bacci takeyi, baitu sai yar lukuta ce, mai fadin fuska hancin nata kamar, biro ga idanuwanta farare kal, Dan bakinta kamar an tsaga mata duk Wanda yaga Baitu Wallahi ba namijiba hatta mace saita kalleta.
Haka likita ya rubuta musu magani suka koma gida, bayan baitu taji saukine hajiya ta tsareta da zafafan tambayoyi, saboda bataso NURU yayi laifi tace babu komai kila ba gaskiya Likita yafada muku ba, Ashwa dake gefe tanacin indomie tace “Hajiya Wallahi itada yayane karya take miki, duk yadda Baitu take kyaftawa Ashwa ido saida ta tona.
Hajiya ta mik’e a fusace, tayi sasan NURU tace “Sannu Tabbatacce Kaji tsoron Allah ka tuna baitu amana ce ga gareka baikamata kadinga bata mata raiba kasan lalurarta ta ciwon zuciya, kuma katuna yau saura kwana ashirin da biyu bikinku dukda ba tarewa zatayi ba dole ka kula da ita a matsayin matarka, inhar na isa dakai”
Shidai NURU abun yafi karfinshi, washe gari tunda sanyin safe ya fita aiki, bashi yadawo ba sai misalin karfe goma na dare dayake gwamna bayanan shiyasa komai yazo musu da sauki yau, amma NURU yazo musu da wani albishir Wanda saida kowa ya girgiza, ya siya musu gida a garin Zaria acikin KABAMA can yakeso su koma, mahaifin Nuru yaji dadii k’warai, sannan yasama ma mahaifin shi shaguna Wanda zai dinga siye da siyarwa, a FULFULDE PLAZA, abun gwanin ban sha’awa, haka suka kwana da murna.
Amma abun mamaki NURU yaga Ashwa yaga kamal amma baiga Baitu ba hankalinsa ya tashi amma saiya nuna kamar bai damuba, nidai Humairah nace NURU dama kadaina na Fulani kaso Baitu tunda Wanda ya mutu baya dawowa,
*Koya kuka gani masu karatu*??????????????
[2/21, 7:21 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
3⃣6⃣
Haka NURU yaci gaba da harkokinsa amma yakasa sanarda Baitu cewa aurensu ake shirin yi nan bada jimawa ba, hajiya ce zaune cikin farfajiyar gidan inda yaranta mata masu aure wani gida suka kawo mata ziyara itada hajiya wacce akafi sani da Rabi, farace amma ba Sol ba, Ta auri Alhaji Usman Wanda akafi sani da ZUNNU-RAYN, Tun tana yar shekara sha uku haka tazo gidansa tazuba yaya har shida, batasan meye kishiya ba, bare yayanta Susan yan uba ba.
Baitu ce tazo wucewa ta gaidasu tana washe baki, mommy tace “Dadina da baitu ak’wai aukin dariya komai nata yana burgeni babu inda tabar Bisma, Shiyasa na labari ya iskeni cewa yaya NURU zai aureta hajiya bakiji wani irin mugun dadii danaji ba” hajiya tace “Uhumm kukenan daku kasan inda ke muku ciwo banda NURU gaba daya bayata yarinyarnan nidai fatana karya wulakanta yar mutane muji kunya”.
“Hajiya kenan banda abunki ai inace zata tare a gidanta ne?”
Hajiya tace “Meeeeeh inji akuya ai cewa yayi tazauna damu Wato tayi mishi kan kanta toh zanyi maganinshi saiyazo dakanshi yace bani matata mutafi kannan Baitu zata koma” Ni’ima tace “Hajiya Wallahi haka za’ayi Wato yaganta Yarinya bata cika mutum ba to koh saiya yara”.
Kowa dai acikin k’anninsa basuji dadii ba, shiyasa kowacce ta tofa albarkacin bakinta….. Haka sukayi hira harnawani lokaci harsuka gaji da jiran nuru kowacce mijinta yazo ya dauketa, baitu tashiga damuwa k’warai saboda zancen datakeji na aurenta da NURU yaxama dole insamu hajiya insan abunda ake ciki.
Washe gari Baitu ta shirya tsaf zasu wuce makaranta hajiya ta kalleta tace “ke ina zuwa?” Baitu ta kalli hajiya cikin Rashin fahimta “Hajiya mak’aranta zani mana”
“kizauna yau ya k’walam zatazo saboda shirye shiryen aurenki”.
Baitu tasaki baki tace “hajiya wai waye zaiyi aure naji Anata zancen aure? Lallai Ashe munada shan biki baitu tafara murna duk tana sane takeyi don ya zuwa yanzu tasan komai, Hajiya ta zaunar da ita tace “Kece zakiyi aure zaki auri yaya nuru dafatan kina sonsa?”
Baitu ta kwabe fuska tace “nida yaya baya sona komai nayi ban iyaba nidai gaskiya saidai a chanza mun wani bashiba”
Tafara buga kafa tana kuka haka hajiya ta lallasheta ta kwantar mata da hankali harta aminche”.
*SAURA SATI BIYU BIKI*
***********
Hajiya ta hado akwatina dagani na fade, ya k’walam kuwa tadanyi tanadi, gashi an asace musu shanaye inba hakaba sa guda ake yankawo a biki, haka iyayen bisma sunyi abun azo agani inta kama ayi gulma kayane nagani na fade saidai kash basusan cewa baitu bazata tareba amma duk bata baci ba haka aka ajiyesu inda bazasu lalace ba, Ummi tana masifan son NURU shiyasa bata mantawa dashi kusan koda yaushe saiya kai musu ziyara sannan ga kyauta dukda ba mabuk’ata bane, hajiya taji dadi tace “Haka akeson mutum yayi kyauta ta dama ba tareda Hagunsa yasani ba fatana Allah yayima wannan yaro albarka.
*KWANA UKU BIKI*
*********
Dayake ba wani taro za’ayi ba, Amma baitu taji gyra sai kunga kawayen baitu yan kuci kubamu wasu koh irgan dangi basu faraba, baitu tasha gyra iya gyra mommy da ni’ima sunyi kokarin yin mata komai, haka aka shirya k’asaitaccen walima acikin gida, Ango NURU in Baku labari yaki sanarda kowa sai wayanda sukeda link da gidansu, su hamdan da kausar sune kan gaba, haka aka shirya walima babu nuru, baitu bata damuba itada kawayenta sai hira suke suna dariya waaxin da akayi musu yashigesu kwarai, ba akan komai bane sai biyayyan aure Sanin kima da darajan miji yan’uwan miji, tsarekai daga fadawa halaka.
[2/22, 8:19 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*