DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣7⃣

Haka aka watse kawayen amarya su Ashwa ana can ana ta hada hada, ya k’walam ce zaune tacewa hajiyan NURU “koh kunsan Baitu ba sunanta na Asali bane” hajiya tace “kai haba duk daukanmu ai sunanta kenan?” Ya k’walam tace “Ah ah sunanta *MUJEEBA JOOD’A*.
Tuni hajiya tasanarma NURU cewa baitu sunanta mujeeba haka aka sanarda kowa sunan Baitu na asali.
Kuma baitu tasan sunanta amma ta boye kai Fulani sai abarsu, NURU ne ke wannan maganan kuma a rayuwarsa yana masifan son sunan don har cewa tayi sunan yarsa tafari mujeeba dansa na biyu mujeebu, washe gari ajayiwa baitu kwaliya nagani na fade haka tadinga shigan kaya iri daban daban, misalin karfe biyu da rabi na rana aka saura aure
*NURU DA AMARYARSA MUJEEBA*.

Dayake bikin bakowa yasani ba shiyasa mutane tsiraru kake gani, mahaifin bisma shiya bada baitu ma mahaifin Nuru, akan sadaki naira dubu hamsin, aka zanyi Adu’oi aka shafa fatiha, abokan ango kausar da hamdan suke kai kawo har aka gama biki.
Washe gari akayi budan kai da yamma Ummi dasu ya k’walam akayita ma baitu fada kamar zasu ari baki, koh Dan kukanda amare keyi baitu batayiba saboda baasan ciwon kaiba baasan zafin rabuwa da iyaye ba haka kowa ya watse.
Gida Yaza mana shuru daga Baitu sai Ashwa sai kamal Wanda ya tasa baitu yana mata tsiya harta kulu tafara kuka, shigowan yaya NURU ne yasa kamal tashi yabar wajen, NURU ya kalli MUJEEBA yace “ke lafya kike kuka kamar wata karamar Yarinya?” Ashwa tace “Ya kamal ne yake tsokananta wai matar yaya NURU”
NURU ya kulu yace “Shine yazama abun kuka? Allah wadaran naka ya lalace” mtwww tsaki yayi ya wuce Dakin hajiya ya gaidata yayi mata ban gajiya.

Hajiya tace “Toh yanzu nauyi ya rataya akanka, dukda muna tare dole kasauke duk wani hakki daya rataya akanka daga sutura Rashin lafya cinta Shanta, dukda muna tare har lokacin daka mulmula ka mulmule kanemi matarka saimu baka kajini koh hantara kyara kar inji kar in gani, kanuna mata so kajata ajiki har tasan meye aure da abunda ya kunsa”.
Nuru shuru yayi yakasa cewa komai saida yadau minti biyar yace “Zanyi yadda kikace insha Allah” haka Alhaji yayimai fada sosai.
Bayan SATI daya da biki MUJEEBA ta shirya tsaf itada Ashwa zasu makaranta dukda sunkusa komawa garin Zaria daxama, skirt ne mujeeba tasa iya gwiwa sai safa ta tuma uban gashi ta kulle tadau Beret tasa duk Wanda yaganta saita bashi sha’awa, sun kammala breakfast kenan, hajiya tace “Mujeeba yimaxa kikira yayanki yakaiku school karku makara” MUJEEBA bataso ba amma babu yadda ta iya da dariyarta ta mike tana tafe taku daidai ta isa kofar sasanshi knocking takeyi tana sallama, haka yafito dagashi sai boxer saurin kauda kanta tayi tace “Mun shirya kaxo ka kaimu school naji ance zakayi musu bayani cewa ni matar aurece”
Wat!!!!!??? Zare ido NURU yayi yace “you must be out of your sences matar aure wakika aura?”.

MUJEEBA ta mishi wani banzan kallo ta juya zata tafi sai wata zuciya tace koma kibashi amsa, juyowa tayi saida gabansa ya fadi “Kaina aura kuma Kaine mijin look Malam idan zaka iya kaimu you better do inkoh ba hakaba munada kafa biyu don ba guragu Allah yayimu ba, banda mistake mezanci dakai look at you” haka tafadi ga turancinta dake dabo, da fillanci.
Tafiyarta tayi NURU ya mutu a tsaye yace zanyi maganinki bazaki taba zama mata acin zuciyana ba saidai a waje bisma ita nakeso kuma da sonta kadai nake Rayuwa.
Kafin yayi brush ya fito su mujeeba har sun tafi adaidaita suka tsare suka kama gabansu, fitowa yayi yashiga folon hajiya yace
“ina suke?” Hajiya ta kallai tace “Banda labarin inda suke kai Wallahi kadaina abunda kakeyi Wallahi Wanda ya mutu ya mutu, kadaina wulakanta Mujeeba don wata rana”………sai tayi shuru arude yafita har yarigasu zuwa makarantan.

Ashwa ce tacewa mujeeba “kinga kaman motar yaya?” Mujeeba ta tabe baki tace “kinga idan kallonsa zaki tsayayi ni banda lokaci mu wuceshi mununamai cewa mu fah manyan yarane” haka suka wuceshi yana mamakin yadda suka jisgashi cikin class suka shiga suka zauna suna karban darasi, aikowa akayi akira mujeeba kowa na class yace babu mujeeba, aka kara dawowa akace MUJEEBA JOOD’A akace babu mujeeba jood’a sai baitu jood’a, NURU yace “Malam itace” haka aka zakulo mujeeba sai office malam, salman yace “itace wannan? NURU ya kalleta yace “Eh Inaso pls kubarta tadinga sa hijab sannan akula banda kallo don naga kusan Duka school din Malamai mazane, haka principal yace toh takoma class saida ta harari NURU kannan ta fice.
Haka NURU yakoma gida da tsananin tunanin nayi kuskure danace baxan tareda mujeeba ba Dana dinga Dana mata gyada a hannu nasan daduk wani iya shege saita rage amma zan tuntubi hajiya inji, don iche Tun yana danye ake tankwara shi don mujeeba takara shekara daya gaba nizata gasawa gyada a hannu.
[2/22, 7:57 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣8⃣

Ni melody dake gefe mezanyi banda dariya nace tabbas NURU ka makara, ichen nan yarigada ya bushe, cikin gida yashiga da mota yayi packing amma kafinya shiga gida Adu’oi kawai yake rerawa acikin zuciyanshi, kitchen ya iske hajiya tana yan gyre gyre saboda hajiya bamaison yar aiki bane tafison tayi aikinta koda zai kaita dare tanayi, “hajiya sannu da aiki”kujera ya dauko ya zauna yace “hajiya gaskiya na canza sha’awara inajin nan zaku tafi kubar mujeeba saboda yan wasu dalilai”hajiya ta ballamai harara tace “kul karka sake kazomun da zancen banza don wallahi koda kukan jini zakayi mujeeba dani zata zauna sai ranan da ka bukaceta don yanzu nasan bakada wata manufa illah ka muzguna mata kar inji”ta juya taci gaba da aikinta haka NURU ya mik’e yanufi dakinsa.

Misalin karfe biyu su mujeeba suka Dawo agajiye ko zama batayiba NURU yashigo yace “ke yimaza ki hadamun abinci kikaimun Daki sannan ki hadamun lemon natural ki matse ki kaimun, haka Baitu ta sakankance da kallonsa tace “wai yaya meyasa bakaso inhuta ne daga dawowa na sai aiki kabari idan cikina ya dauka nayi full charge sai ayi wacce za’ayi idan zaka iya jure yunwa toh ni bazan jureba” Daki ta wuce tabarshi tsaye yana cizon yatsa kuma abincin dabata kai maiba kenan.

A kwana atashi asaran mai rai sunata shirin komawa Zaria, haka sukayita ban kwana da yan’uwa makota Baitu kam har shinkafi aka kaita tayiwa su Ummi da Abba bankwana haka suka kara yimata fada akan kama mutuncin kanta sannan tasan cewa aure ne akanki, iyayen Arziki kenan basuda wani buri illah kizauna lafya hakuri da juriya yi Nayi bari na bari, akasin iyayen banza basuda wata sha’awara saita yana miki kiyimai, daya ajiye riga ki lalube idan bai bakiba Karki dafa kaico duniya ina zaki damu iyaye mu gyara halinmu, Tabbas duk macen dakeson zama zinariya acikin gidanta awajen mijinta saita yi aiki da sha’awarar Arziki, tattausan lafaxi, iya Girki, iya kwaliya, iya kissa da kisisina, iya taku, da wannan kadai kinciri tuta bare kuma akaiga wajen kwanciya.

Haka suka koma Gusau washe gari sai Zaria yaran hajiya Duka dasu aka taho rakiya kamal dashi zasu koma Ashwa itace kawai ta rage musu a gabansu saikuma baitu Wato mujeeba, dazuwansu gida suka katafaren gida nagani na fade, bangare kuda dagani ba bayani na Baitu ne sai wani achan gefe Wanda yasha kayan gabas na iyayensa ne, Hajiya da Alhaji tuni suka fara kukan dadi suna Dada shima NURU albarka suna tuna irin bakar izayan da sukasha a baya da yawon haya da dawainiya da sukayi da NURU wajen ganin Yazama wani Abu a Rayuwa, sai gashi yau sune cikin wannan daular Hajiya tace ARZIKIN YAYA kenan duk macen data haihu karta cire rai, sannan duk macen dabata haihuba ba wani rabo idan yaso zaki haihu saikin haihu saidai idan bakida kwai a duniya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button