DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Kafin abude gidan saida akayi Adu’oi sannan suka shiga ciki, aljannar duniya idan baka mutuba baka gama ganin abun duniya ba, baitu kuwa washe baki kawai takeyi sai jin dadi takeyi, Ashwa kuwa takasa zaune takasa tsaye haka sukayi settle washe gari duka suka koma saidai NURU yananan don saiyaga komai ya kan kama na gameda shagunan alhaji, harda masuyi musu hidima suka samu dayake Nuru yanada abokai a Zaria musamman a dogarawa, kayan abinci haka yasiyo musu kamar baisan zafin kudiba, hajiya tace “Kai nuru irin wannan siyayya kaman ba’a buhariyya? ”
Nuru yayi dariya yace “Hajiya inda kudi suke Wallahi Sunanan talaka shike shan wuya hajiya abun sai godiyan Allah kinji” Baitu ta kalli NURU tace “Tace yaya shikenan mun daina zuwa school haddanmu shikenan ta tafi?”Nuru yayi mata wani irin kallo tuni ta natsu.

Haka yakammala komai hatta makaranta saida yasasu aka sama musu direba, Alhaji Yakama Sana’a kannan yabar garin Zaria, koh waigen Baitu baiyiba ya wuce Baitu tace “Aikin banza harara aduhu Kaine da sannu baniba, kayi a banza nima na huta da kyara da zagi duk kai kadai”tsaki tayi ta shige ciki haka suke hira da Ashwa, hirarsu bata wuce na yadda ake soyayya, wata kawa sukayi ma’abociya karatun littafan Hausa, haka suke bata kudi tana siyo musu a boye tunda basuda waya, nan Baitu wadda akafi sani a yanzu da mujeeba tafara course kala kala, littafin Zainab dahiru wauwo tafara karantawa subul da baka, Wanda ya chaza mata kwa kwalwa daganan, tafara karanta littafan RAHMATU HASSAN ZARIA, Daganan baitu tafara jin shauk’in kasancewa tareda mijinta “Ashwa Ashe haka so yake Tabbas akwai dadi Zanso ace nima ina cikin wannan yanayin da yaya nuru amma taya zanyi don ganin nasamu guri acikin zuciyanshi?”Ashwa tace “kibari zan samo miki lambar Humairah wacce nasan duk Abunda zata fada miki akan yadda zaki sace zuciyarshi saikinyi mamaki”.

Kubiyoni kuji yadda baitu zata sace zuciyan NURU sannan abun tambaya anan shine NURU dawuya ya aminche koh kuma ta tafi da imaninsa bayan yana soyayya da matacciya????
[2/23, 2:20 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

3⃣9⃣

Kusan karatun littafin Hausa ya zame musu jiki, karatun bokon har nema yake ya bace musu saboda tsananin karatun Hausa, a Kullun Baitu kara koyan fasahohi takeyi naban mamaki da Al’ajabi, an shafe kwanaki babu NURU babu labarinsa k’watsam yasa ranan zuwa Zaria don gaidasu hajiya don badon mujeeba zaizo ba saboda a cewarsa bata cikin tsarin rayuwarsa, hajiya take sanarda su Ashwa da mujeeba cewa yaya NURU yana nan tafe jibi haka Ashwa da mujeeba Suka shiga Daki don shawarta yadda lamarin zai kasance.

Lambar Humairah suka kira bugu daya biyu ta dauka, cikin muryan natsuwa da kamala sallama tafara daga bisani ta buk’aci jin suwaye ke magana, saboda son da takema mutane yasa duk Wanda yakirata don Neman shawara koh taimako take basu dukkan Attention dinta, Ashwa ce tace “barka dai malama Humairah nasan zakiyi matukar mamaki, sabbin kanni kikayi suna bukatar taimakonki idan har ba matsala”?

Humairah ta nisa “Kufadi matsalar Ku Allah yasa inada mafita” haka suka zayyana mata komai daga farko har karshe, nan Humairah ta fara bata shawara ta farko tace “abunda zaki farayi shine kije saloon ayimiki gyran gashi, sannan kiyi kunshi nagani na fade sannan, kiyi mai special abinci sannan kisa kaya Wanda babu raini kiyi kwaliya kaman wacce zata gasar kyawawa, kifeshe jikinki da turare masu kamshi be nuru ba hatta Rossy duk girman kansa dole yaji wani Abu acikin ransa, sannan Karki sake ki nuna kina murnan zuwanshi yadda kika saba haka zakici gaba da shaaninki, ina gaya miki idan bai tafi dake acikin zuciyaba saiya Dawo dake”.

Haka MUJEEBA tayi farin cikin wannan shawaran sannan sukayi mata godiya suka kashe wayan tafi sukayi sukayi shewa Ashwa tace “Yar’uwa dole mu mike saboda yanzu namiji yanasonki yakika k’are bare bayaso”Mujeeba tace ganemin hanya, wajen hajiya suka nufa suka gayamata duk bukatunsu ta aminche, kudi ta mika musu Wanda zai ishesu suka wuce SHANTEL Saloon dake tudun wada direba yakaisu yajirasu daganan suka wuce kasuwa kayan Queens cake suka siyo harda na icing, kayan hade hade na fried rice chicken soup and the rest.

Gida suka wuce Ashwa tana kallon irin tsaruwan da Mujeeba tayi tace “Matar yaya kinga irin kyau da sheki dakikeyi tabbas sweet sixteen yana tasiri akanki baby kiyi komai ba komai Saima gobe”Mujeeba tayi dariya wacce take kara fito da kyawunta tace “Sweet Ashwa you will never understand yadda nakejin mijina acikin raina bantaba Sanin cewa haka aure yakeda tarin niima da ladaba saidana k’aranta *Matar So* Wallahi sainaji duniya tanamun dadii tabbas aure yayi komai kikayi lada ne acikin gidanki amma kinga bariki babu abunda mace zata tsinta sai walakanci sannan ba godi bare nagode, sannan lada saidai kiji labari a makota makotan ma Ma’auratan juna”.

Shewa sukayi suka shiga gida hajiya taji dadin ganin Mujeeba yadda tayi kamar wata sarauniya, washe gari Tun Asuba suka tashi da aiki, Ashwa ranta baiso ba Amma batada yadda zatayi saboda shakuwar da sukayi da juna suyi fada su shirya, hajiya tanata mamakin Mujeeba tace “Tunda mujeeba taji mijinta zaizo naga duk ta canza Allah yasa NURU ya yaba lokacin zaiji magana”kitchen tashiga tana duba aikin da sukeyi cikin natsuwa da tsafta cikin kankanin lokaci suka kammala aka jera komai inda yakamata, Daki suka shiga suka shek’a wanka amma ita Ashwa batayi wani kwaliya ba amma duk Wanda yaga Mujeeba baxai sake cemata baitu ba wata atampha tasa mai ruwan kore, komai nata too match, turaruka ta dauko daga humra zuwa kulacca turarukan Kamshi na waje carribein shine Wanda tafi k’auna haka tasa takalmi Kore.

Horn sukaji Ashwa ce tayi saurin lek’awa tace “Beb he is here waw can’t you see how you’re looking, hmmm Epitome of beauty kenan ”Dariya sukayi Mujeeba ce tayi sarin fita koh gyale babu sai takalmi dake sanye a kafanta.
[2/23, 7:10 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

4⃣0⃣

Bada niyyan bude kofa taje ba amma jin ana kwankwasa kofa tace “Yes am coming ”bude kofan tayi lokaci guda ta juya tana tafiya cikin salo nidai anan har cewa nayi irga tafiyan takeyi NURU tsaye yayi yana kallon kirar da Allah yayiwa wannan baiwar da mamaki sai cewa yayi
“koh ina hajiya tasamo wannan yarinyar datake Neman rikita mutane gosh meyasa haka wannan ai salon Asa mutum cikin halaka ne”
Itadai tafiyarta tayi ganin yadade bai shigoba yasa mujeeba juyowa tace
“You are welcome pls come in an have a set”tafadi tana nunamai kujera.

Gabansa ne yayi mugun fadi yace “Tab Ashe yau danayi abun kunya karamar Yarinya ta rainani”sallama yayi hajiya tafito cikin zumudin ganin danta tana mishi marbabin, itako Ashwa tsale tayi ta haye kan NURU tana mishi sannu da zuwa, hajiya ta kyalla ido taga Mujeeba bata falon kwala mata kira tayi Mujeeba! Mujeeba!! Mujeeba!!!.
Daga k’uryan Daki ta amsa Ashe wasu kaya aka canzo, Hajiya tace “Waw wannan kwaliya haka nasan na tarban mai gidanne Ku dauki jakkansa kushiga dashi dakinsa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button