DASHEN ZUCIYA

A filin jirgi suka sauka acikin garin Gusau, inda yan’uwa da abokan arziki suka cika dankam don tarban yayan gata, Nuru yashiga damuwa wacce baxai misaltu ba amma duk Wanda yaga bisma da Hamdan saiya gane cewa suna cikin farinciki, nan danan su kayiwa junansu sallama, kowa yatafi inda matsuguninsu yake, anyi murna kwarai daga Duka bangarorin,
Bayan wasu yan kwanaki da dawowarsu Bisma tadamu kwarai saboda rashin ganin Hamdan, Nuru ne ya sauka daga cikin Motarsa ya k’wank’wasa kofar gidansu Bisma zaune take a tsakar gida, mai gadi ya wage kofar gidan “Dan Allah bisma nake nema ko tananan?”
Mai gadi ya juya yace eh bari in sanar da ita,
“Ranki ya Dade kinyi bak’o” cikin zumudi tace “Kace ya shigo” duk a tunaninta Hamdan ne amma sai taga ak’asin hakan,
Nuru tagani yana shigowa da hancin Motarsa lokaci guda taji ranta yayi mugun baci amma saita boye dariya tayi tace “Manyan kasa Ashe Baka manta daniba” Lemo tasa aka kawomai da ruwa.
Dariya Nuru yayi yace “Banda abunki Bisma ai zumunchin mu bamai karewa bane, fatana shine Allah yakara hada kanmu baki daya”
“Tabbas wannan haka yake Nuru banida Wata kawa koh aboki Wanda ya wuce kai, ina iya gayama duk wani sirri nawa batareda naji wani dar acikin zuciyana ba, Sai kuma Hamdan Wanda yak’asance abokin rayuwana bantaba son wani da namiji yadda nakeson Hamdan ba, I really love him amma sai gashi yau Kusan satinmu uku babu Hamdan babu labarinshi koh wayarsa nakira bana samu kuma bansan yaxanyi ba, nasan ba darajata bace inje gidansu da sunan ina nemansa bansan dawani ido zasu kalleni ba”.
Shuru ne yadan ratsa Nuru bakaramin dadi yajiba, yadda yaji Hamdan bai damuda Bisma ba, “My friend hakuri zakiyi zuwa wani lokaci kila dakwai wani Abu so strange daya rikeshi but nasa
[1/31, 7:51 PM] Mummy: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
4⃣
Nasan everything shall be well with him”, kallon Nuru Bisma takeyi yadda duk ya damuda lamarinta yadda yanuna rashin jin Da dinsa akan rashin zuwan Hamdan, sun danyi hirarsu wacce batada maraba data masoya, Sallama sukayi daga bisani ta rakashi har gaban Motarsa, harya fita tana dagamai hannu cikin gida Bisma tashiga tana wasa da yan yatsunta tana wakan christ brown, cikin dakinta tashiga tafada kan gado, wayarta ta dauko ta hau kiran lambar Hamdan amma bata shiga, saidai taji the number you’re trying to call is currently switch off nan ta zabga uban tagumi Wanda ya nuna tana cikin tashin hankali.
Gefe na koma ina tunanin yadda Hamdan yayi barin iska da lamarin Bisma, meyake nufi da itane yana nufin duk love din da sukasha a Florida USA duk ta bogi ce?
Abunda nikaina HUMAIRAH nakasa bawa kaina Amsa kenan, Chatting takeyi Wanda yaxame mata jiki, bata wannan GRP bata wancan saidai yawancin group dinta na matane sannan kuma na novel ne, wani novel ta tsinci kanta da karantawa, Wanda yayi shige da yanayin aikinta Wato NEESMA’A WAH NUSHUUF,
Wannan littafin ba karamin tafiya yayi da imaninta ba,
Karar bell din dakinta taji hakan yasata kashe data, ta mike ta bude kofa, Nabil tagani tsaye yanata dariya Wanda tarasa gane ma’anar hakan batayi kasa gwiwa ba Wajen cewa
“Nabil lafiyanka sai wani dariya kakeyi saikace Wanda akace ga Aljanna shiga?”
Nabil yace
“Aunty Bisma dole inyi farin ciki tunda Allah yasa appointment dinki na aiki yafito shine nace bari inzama mutum na farko daxaiyi miki albishir”
“Naji dadii kwarai nabil amma hakan baxai sani farinciki ba matukar banga Hamdan ba, shine mutum na farko daya karbi ragamar zuciyata, amma tunda muka Dawo yau kusan sati uku bashi ba labarinsa”.
Dukda nabil karamin yarone Wanda shakarunsa bazasu wuce Sha takwas ba, yasan cewa yar’uwarsa tana cikin halin kunci na rashin mosoyinta,
Washe gari suna zaune a katuwar darduma wacce itace tazama kamar dining dinsu anan ake baje kayan abinchi kuma kowa anan yake zama doncin abinchin,
Daddyn sune zaune Bayan sun kammala cin abinchi,
“yabo ya tabbata ga Allah madaukakin tsarki dayasa Bisma ta karkare karatunta, nazama kwararrar likita a fannin maza da mata, har ila yau gashi tasamu aiki a Federal medical center dake garin Gusau, an dauketa a matsayin consultant, yanzu Abu daya yarage mata a Rayuwa shine tafito da mijin aure Wanda shine zaisa tacika mace”.
Yana zuwa nan yayi shuru, Bisma koh tashiga rudani
“mai daddy yake nufi dani toh ni yanzu idan ance infito da miji yazanyi after ol Hamdan ya watsar dani dukda moment din da mukayi spending tare a USA”
Muryan daddy ne yadawo da ita daga tunanin da takeyi, “Bisma yanzu Sha’awara yarage naki kiyi gaggawan fitarda miji don hadaku zanyi dasu Rumaisa da Ikram duk inyi muku aure in huta da surutun mutane”.
[1/31, 7:51 PM] Mummy: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
5⃣
Bata iya amsawa ba saboda, wani haushin kanta da takeji tashi tayi lokacin kowa yabita da kallo, kafin ta karasa daki taji karar wayarta dafe kai Tayi a tunaninta Hamdan ne yake kiranta amma saitaga Akasin haka Nuru ne yaketa kiranta amma takasa ta daga wayarsa saboda abubuwan dake dawainiya da zuciyanta, da shigarta daki ta taradda ikram kwance sai minshari takeyi wani wawan Duka ta daka mata a duwawu tace “Maza ki tashi ke har wani lok’acin bacci gareki toh bari kiji in gayamiki abunda baki sani ba Daddy aure zaiyi mana kuma yace kowacce cikinmu tafito da miji don yagaji da surutun mutane”,
Ai ikram batasan lokacin data nanawa Rumaisa dukaba, tace “maxa kitashi kiji wani sabon Al’amari daddy yace kowaccen mu tafito da miji, Zare ido rumaisa tayi tace kalu inna-nallahi wa’inna ilaihir rajiun, tashi tayi ta zauna daga ita sai half vest,
Ikram tace
“a gaskiya nidai a yanzu saidai Daddy ya zabamun miji Donni ubanwa nake saurara bare akaiga wani zancen aure tab wanga abun Alkhairi haka dame yayi kama?”.
Bisma dake zaune tace “hmm ke ikram saurayinne bakida toh ni wallahi Wallahi inada amma tunda muka zakkuwa kasar nan muka rabu airport shikenan niya babu waya babu sako, ke koda lambarsa nakira bata shiga switch off, kinga damuwata guda kenan,”
Rumaisa da karatun ya kare mata cikin kwakwalwa tace “Nifa bari kuji wani zancen banza zancen wofi chan kasar America saurayin nawa yake acan yake karatu muna masifan son juna amma kwana biyu nima shuru, ikram bakijin wayar damukeyi dashi, wallahi 24 waya mukeyi Donni bani sauraran kowa cikin garin ga mazan garinnan koh yan ataru a lalace”.
Wata safiyar Asabar gari ya daure yayi dind’um, saboda wani gagarumin hadari dake haduwa daga gabas, amma Bisma, Rumaisa da ikram shirin fita sukeyi, basu damu da yanayin garinba lace iri daya sukasa amma kowacce da kalan nata, biki akeyi na yayan Hutu yara masuji da kyau da isa basuda maraba da larabawa Wato zuri’a Wamban Gusau kenan, amma in fedewa mai karatu wani sirri Bayan fari wallahi da dukkan su bola za’ayi dasu dama dama ikram, gasu gajeru Kamar a kife da kwarya.
Fitowa suk’ayi saida suka ratsa tacikin falon Ummi suka gaidata binsu kawai takeda kallo tarasa wacce zata yaba cikin su, tashi tayi ta zagayesu tace “Tabbas dawisu daban yake cikin tsuntsaye, Giwa kenan dole aganku a kyaleku, Tabbas kunyi kyau yadda ake bukata amma kun mata Abu guda” daki tashiga ta dauko Wasu warwaraye, Masu kyau da tsada tace wannan wani sirrine dake karawa mace kyau duk inda tayi sai an kalleta, Bisma tsaye tayi amma ranta yayi masifan sosuwa ganin yadda yan’uwanta sukayi mugun kyau.
[1/31, 7:51 PM] Mummy: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*