DASHEN ZUCIYA

Wani irin kunya ya lullube Mujeeba amma saita basar tana murmurshi Ciki suka shiga da jaka itada Ashwa suka kece da Dariya
“Yar’Uwa kinga wani irin kallo da yaya yake miki yadda kikasan yaga bak’uwar fuska tabbas shawaran Humairah ta karbu,
Hajiya data gaji da jiransu ta k’wala musu kira da gudu suka fito cikin isa Mujeeba ke tafiya, “Kuyi maza Dan Allah Ku kawo mishi abinchi mutum ya shawo tafiya ace Baku bashi abinchi mujeeba aikinki ne maza ”.
Mujeeba tayi far da ido tace bismillah muje dinning, tafiya take yana biye da ita saboda tsabar kallo harsaida yaci tuntube kaman zai fadi mujeeba tayi saurin tareshi tace
“Kayi a hankali mijina kar jiwa kanka rauni don bansan yadda zanji in naga jini yana zuba daga jikinka ba” NURU kasa magana yayi saboda tsabar dadin murya mujeeba ga iya salon magana kaman bisma.
Zama yayi tafara bude abinchi tana serving saboda kamshi saida miyansa ya tsinke don har zuba yaso yayi Niko mezanyi banda Dariya nace NURU ka kusa zuwa hannu.
Bayan tagama serving dinshi ta zauna itama tasa abincin kusa dashi ta koma tace
“mijina yakamata kabari inbaka abinchin a baki saboda na hutassheka kaga ka gaji, jiyayi bazai iya share mujeeba ba yace “Mujeeba Dan Allah Kidaina irin wannan magana tana rudani abinci kuma kiyi hakuri zanci da kaina”
Yak’ara kai loma daya na farfesun kayan cikin rago.
“Mujeeba wannan irin kwaliya haka kaman zaki gasan kyawawa, dafatan ba haka kike fitaba”?
Mujeeba tace
“Haka nake fita don har sabon saurayi nayi sunansa Umar Wallahi yaya baka ganshi ba son kowa kin Wanda yarasa, gashi da shegen kishin tsiya basan yadda zaiji ba Dan na sanar dashi cewa inada aure”.
Abinci NURU yakeci amma gaba daya maganganun mujeeba sun ruda mishi ciki, jiyayi cikinsa ya murda inajin saida NURU yashiga toilet yafi a irga itakoh mujeeba da gangan tayi wannan maganan saboda tagane cewa yafara sonta kokuwa har yanzu?
Tashi tayi tabar falon Daki ta koma ta haye gado tana tsale tana murna Ashwa ce tashigo tace
“Ke gayamun yadda film din yayi ending? ”
Mujeeba ta rungume Ashwa tace
“Ashwa Aunty Humairah tayi a Rayuwa dole in shelantawa matan duniya cewa she is the best batada wani buri saina ganin ta gyra zaman aure da rayuwar cikin auren, Ashwa am speechless duk ranan da yaya NURU yafurta cewa yana sona Wallahi sainayiwa Humairah kyautar ban mamaki”
Gaskiya ne Mujeeba tabbas Allah zai sakawa Humairah da Alkhairi.
NURU kuwa Gwanin ban tausayi lokaci daya ya fige hajiya tafito tana tambayan sa lafya yake sanarda ita cewa cikinsa ne ya burge haka ta kawo mishi plygin ta hada mishi ruwan gishiri da Sugar, zama yayi yana fuskanta hajiya maganan mujeeba tana damunsa harya kasa jurewa zuciyarsa yace
“Hajiya yanzu a matsayin mujeeba na matar aure bai kamata tana irin wannan k’walliyan tana fitaba, sannan hartana kula samari wayanda ba muharramanta ba kuma tasan cewa Nike aurenta amma take irin wannan? Gaskiya tare zamu koma Gusau saboda indinga samata ido sosai”.
[2/24, 9:00 AM] Melody????????♀????: *DASHEN* ????
???? *ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
4⃣1⃣
*Ina Kara jaddada godiya na ga masoya wannan novel saboda kaunar dakuke mishi ngd kwarai Allah yabar zumunchi Adu’arku gareni Tabbas tana tasiri Allah yakaremu da karewarsa, ya Allah karka barmu da iyawan mu ya Allah*AMIN???????? LYSM MY FANS????????
Hajiya ta wani harareshi tace
“lallai wuyanka yayi kauri ka dubi tsabar idona kace zaka tafi da ita saboda kadinga sa mata ido, Toh ni me nake samata kafa ko katare? Tambaya nake kayi shuru?”
NURU yayi shuru yarasa abunda zaice ga cikinshi sai kara murdawa yakeyi.
“Ai mu ba tarbiya muke koya mata ba kai kadai kasan yadda zaka bata tarbiya toh koda mujeeba zata tare ba yanzu ba kuma saida aminche warta shashashan banza shashashan wofi lokacin da’akace atare me kace sai yanzu zakazo da kumfan baki wai zaku tafi Gusau kutai kebbi gaban Gusau saida kaga yarinya tayi dumimi tazama mace kayi gaggawan canza shaawara”.
NURU yace “hajiya Wallahi samari take kulawa kuma kinsan bayi bane matar aure ta kula samari” “Ta kula din ai cewa kayi kaifa baka sonta toh mexakayi da ita bayan kana soyayya da matacciya Wallahi Kasani Wanda ya mutu baya dawowa, Sannan abunda babban ya hango yaro ko yahau Dutsen Mambila bazai hango ba” hajiya na gama magana saika Alhaji yadawo saga kasuwa yayi farincikin ganin dansa amma saiyaga kaman baya cikin walwala, haka suka gaida yace
“Nuru lafya naganka kaman mai jinya? Koh dai…… Hajiya ta katse da cewa “Matarsa yakeso abarshi yatafi da ita shine ya tsareni yanamun wa’azi waishi kabiru Gombe na gayamai ba yanzu ba Sannan idan ka gaji da zaman kadaici kayo aure kanada daman yin mata hudu harda k’wark’wara idan kaso amma addini hudu yace namiji yayi”.
Mahaifin NURU yace “Hmm yaro kenan Kanaso kace yanzu kafara son mujeeba ne? Idan harka fara sonta kamata yayi kasanar da ita hakan kila hakan yasa ta Aminche ta bika”
Budan bakin NURU yace “Ni gaskiya Alhaji har yanzu banjin mujeeba araina Amma ayimun adalci mutafi tare acan kila ma saba har naji inasonta ”
“Aikin banza Ashe da sauranka amma bari akira mujeeba aji idan tanason binka shikenan idan kuma tace Ah ah Wallahi kai kadai zaka koma”.
Haka Hajiya ta kira mujeeba, ta zaunar da ita tace
“Mijinki gashi yace zaku tafi tare” mujeeba tayi saurin dagokai tace “Hajiya babu inda zani inanan abunda basona yakeyiba salon mutafi ya dinga muzgunamun bakwa kusa ai nikam babu inda zani” tashi tayi dagudu tayi cikin daki tana shiga ta kece da dariya tace kadan kafara gani indai mujeeba ce duk ranar daka furta kanasona ranan nikuma zan tabbatar maka da irinson danake maka.
Ashwa tace “kinyimun daidai Wato yaga komai yaji ya rude kuma yana fulako baxai ita cewa yanason matarsa ba lallai Girman kai rawanin tsiya ai Karki kuskura kikai kanki wata rana ayimiki gori” NURU yashiga tashin hankali kwarai iyayensa sunki bashi Goyon baya haka yakoma yana Dana Sanin zuwansa.
Kusan tsawon kwanakin dayayi haka yadinga shak’an bakin cikin Mujeeba don wata rana gyale a hannu take rikewa tafita Sannan ta bazo gashi nan har Gadon baya, Sannan wasu kaya take sawa masu tada hankali ga iya kwaliya da magana fita zasuyi itada Ashwa amma itace tafara gaba, wani sak’o ya boye ganin tana tahowa ya janyota sai akan jinkinsa tuni yaji numfashinsa yana Neman daukewa saboda wani kamshi dayaji *AROOSA* marairaicewa yayi yace “Mujeeba inazaki kikayi kwaliya haka dubi irin shigar dakikayi”cikin kafin hali tace “banason wulakanci Malam meye matsalanka da inda zani Sannan meye matsalan shigan danayi? Pls kaga banason irin Wannan policy din saikace ka ajiyeni tsakarmun hannu”.
Tashi tayi tana huci “Mujeeba Kituna ke matar aurece Karki manta ni mijinki ne”
“Dakata malam ta ina naxama matarka? Inace kace bazaka taba kirana ba matarka ba zaifi dadi idan kama koma cemun Baitu ba Mujeeba ba koh Matarka, inace bazaka iya sauke hakkina dake kanka ba, inace soyayya kake da matarka nikuma banaso na nisantaka da ita shiyasa neke Neman Wanda bashida soyayyar matacciya acikin ransa in aura” wani wawan mari yakaiwa Mujeeba amma tuni ta chabe hannunsa tace “kul ka kuskura ka tabani ba aureba koh dadirone saika sakeni, A tarihin rayuwana babu Dan Adam din daya tabasa hannu ya mareni bare duka, idan kana ganin kanason Bisma nasan bakakai iyayenta ba haka baka kaini ba saboda sa zuciyarta nake Rayuwa”sauke hannunsa tayi ta wuce aguje sai daki, fitan data fasa kenan.
[2/25, 7:57 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*