DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

4⃣2⃣
_*Ina mik’a taaziyya ta ga Mienerh Hamidan abisa rasuwar aminiyarta datayi Sadiya sani maitama Allah ubangiji yaji kanta yakai haske kabarinta yasa Yan matan Aljanna ne????????AMIN*_

 

 

Tsaye yayi yana huci takaici ya lullubeshi, ciki yakoma ya kutsa daki ya jingina da Allon gado Ga AC tana hurawa amma zufa kawai yakeyi.
“Mujeeba kinsan irin sonda yaya yake miki kuwa dole ya rude yarasa kansa you are killing baby”Dariya tayi
“Ashwa kenan nasan yaya yakamu dasona amma yakasa ya furtamun nasan cewa iya bakine baikai zuciyaba”.

Gaba daya suka dauki littafan su suna karantawa kwankwasa kofa sukaji anayi amma babu wacce ta damu data tashi ta bude, illah iyaka gyara kwaciya dasukayi.
Banko kofar akayi lokaci guda ko wacce ta boye littafin dake hannunta, yaya NURU ne tsaye yace “idan bakwa komai pls kuzo parlour” Ashwa tace “yata da kalau kuwa”? Ta tambaya wani banzan kallo yayi mata ai basusan lokacin da suka mikeba Ashwa ce ta fara fita Mujeeba ce ta karshe kayan baccine a jikinta mai shara shara amma mai wando ji yayi yaji kunya haka Mujeeba zata fita ga Alhaji a parlor a matsayinta na surika?
“Malama je kisa hijabi koh bakisan kunya bane koh kin manta gidan surukai kike? Pls do as I said” gani kawai tayi ta juya ta dauki hijabi gaba tayi yana binta koh ajinkin hijabi malam abun saida yayi magana.

Guri suka samu suka zauna babu mai cewa uffan nuru yace
“badan komai nakiraku ba saidon in mika muku waya wacce xata zama abokiyar hira Sannan kuma don yin Assignment for Dan an baku, Sannan Inaso inja kunnenki Mujeeba idan kika sake kikaba wani lambarki Tabbas Allah shi zaiyi mana sakayya saboda auren ki nakeyi banda chatting da wayanda ba muharramanki ba Hajiya kina sheda?”.

Hajiya tayi shuru daga bisani tace “kwarai maganarka gaskiya ne Mujeeba dole kiyi biyayya ga mijinki koda Baku tare hakkine akanki ki kare kanki ” Mujeeba tace “nagode Hajiya zan kiyaye”waya yamik’o musu *INFINIX HOTNOTE* kowacce da irin kalar tata kuma da layi aciki sunyi murna sukayi godiya suka koma daki washe gari suna bacci NURU ya wuce GUSAU.

*TUNA BAYA ROK’O*

Rayuwar gidan Ikram da Kausar abun sai godiyan Allah babu wani kwanciyan hankali tun bayan auren dukda yan’uwan taka kausar babu irin cin kashin dabaya mata, baxai Dawo gida akan lokaci ba Sannan bazai bata abinci ba, saidai ya ajiye mata naira Dari biyu, bakuma don bashidashi ba ah ah mugunta irinna namiji, cikinta yayi girma har yakaiga bata iya aiki yadda yakamata, tafe take dakyar KAUSAR ya daka mata tsawa Wanda saida taji Dan cikinta ya juya juyowa tayi ta kalleshi yace
“So nake ki k’washi kayan dattin chan dake daki ki wanke daga yau nadaina kai wankau ke zaku dinga wankesu daxaran sunyi datti” jitayi jiri yana dibanta dakyar ta iya cewa wani Abu
“Haba KAUSAR bakaga halinda nake cikibane amma kake Neman halakani da wanki kana gani hatta wankina yimun akeyi aikin gida sainayi dagaske ka tausaya mun KAUSAR”.

“Koda nakuda kikeyi saikin wankesu ubanwa yace kiyi ciki? Dazaki gayamun halinda kike ciki bansaniba makaho ne ni idan kuma baxaki wankeba kofa abude take you are Free to go” Tashi yayi yafita ikram zubewa tayi a k’asa tana rasgan kuka Wanda babu maijinta sai Almajirinta dake zaune yanacin tuwo.

Mikewa tayi tashiga Dakin kausar ta kwaso himilin wanki Wanda baita mai cikiba nida bake saket saidana razana haka tayi wankinnan tun safe har magriba kannan ta gama, Sallama taji tayi saurin amsawa Kausar ne yashigo tareda budurwarsa kallo daya yayima ikram ta kauda kai cikin falon ta suka shiga tun tanajin shewansu harta dainaji, Kara jigina tayi abango tana kuka haka ta bude kitchen anan ta kwanta ga yunwa gashi mukullin store a hannunsa yake, cikinta murdawa yakeyi
“Allah Kaine gatana Kaine abun bautawa ya Allah idan Wannan aure Alkhairi ne agareni ya Allah ka sassautamun Wannan musibar danake ciki idan kuma ba Alkhairi bane ya Allah ka kawo sanadiyyan rabuwana da KAUSAR” kuka takeyi Wanda saida nima nafara kuka nace Ashe haka mata suke hakuri da mazajensu tabbas dayawa maza wuta zasu shiga.

Misalin karfe hudu ikram tafarka daga nannauyan baccin daya debeta maicikeda mafarkai marasa dadi, dakyar ta mike tace “Tabbas Ana cewa dazaran namiji ya aureki yakai ki gidanshi kika dau ciki toh kin tashi daga matarso kin koma matar hakuri soyayya ta kare sai zaman hakuri Tabbas yau na gasgata maganar mutane amma wasu idan sukayi dace duniya dadi take musu” waje tafito taci karo da wata tsohuwa cikin gidanta bakaramin tsorata tayiba harta soma Jada baya tana Adu’a, tsohuwarnan tace “ke Yarinya kibarjin tsoro kuncinki yakare daga yau” yadda matar take magana gaba daya muryar saita ba mutum tsoro, nidai Humairah nace Ikram kinyi gamo da Aljanna.
[2/26, 10:19 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

4⃣3⃣

Adu’a kawai takeyi cikin ikon Allah matar nan sai matsowa take tace “Ke macece mai hakuri daidai ake samu masu irin hakuri ki, nayi alwashin duk budurwar dayayi soyayya da ita sai nayi Ajalinta Sannan kedai kici gaba da hakuri wata rana Zakiga sakayya Sannan duk lokacin dakika bukaci wani Abu zan kawo miki” kiftawan ido ta nemi aljana ta rasa Ashe cikin jikinta ta kutsa ta shiga, tana bacewa ikram tafadi ak’asa war was saida gari ya waye tangaran ta mike dakyar tashiga cikin daki abun mamaki anyimata face face da daki saboda kazanta amfaniyansa a gado yake zubawa saboda gudun kar budurwar ta dauki ciki, nidai danice kwarai da wata rana nayi Ajalin kausar saboda Dan akuyane ba karshe Wanda babu tsoron Allah acikin ransa.

Haka ta yaye zanin Gadon tana kuka tana kaiwa Allah kukanta, haka ta gyra Dakin cikin natsuwa da kwanciyan hankali lokaci daya ta maida komai ba komai ba, tana gama aikin tashiga mak’ota wajen wata kawarta tana kuka tana gayamata halinda take ciki matar taga kokarin Ikram dabata sabauta budurwar ba.
“Ikram kenan kedai abar kaza cikin gashinta idanko ba hakaba an dinga tonon silili kenan kowacce mace dakika gani da bakincikin da da namiji yake k’unsa mata saidai hakuri kawai shine zai kaimu ga cin nasara, shiyasa bodan wak’a yace Soyayya da dadi soyayya da ciwo mai hakuri mawadaci ne wataran zai dafa dutse don haka kedai ki kalli ko wacce mace duk arzikin mijinta saukin samu Abu biyu dayake mata Wanda yake kuntata mata”.

Ikram ta share hawayenta tace “Amra nagode kwarai inace duk duniya nice kadai namiji yakewa wasan kwallo Ashe mata da yawa boye sirrinsu sukeyi shiyasa bakajin damuwarsu Toh Allah yayi mana sakayya wata rana matar wani zaibi kuma ayi ajalinsa” Amra ce ta mik’e takawowa Ikram shayi mai kauri da bredi da kwai harda farfesun kifi haka Ikram ta dingaci kamar mai kwancen yunwa amra kallonta takeyi tana bata tausayi nima tabani don jinake kamar in wulla KAUSAR lahira saboda tarin haushinsa danakeji.

Tana gamawa ta mik’e da sauri sai gida inda taje ta taradda Kausar ya kulle gidan da kwado sabon bakinciki yakara ziyartar zuciyarta tuni ta zube ak’asa tana kuka mai tada hankali kowa yazo wucewa saiya tsaya yayi mata magana amma bata iya koh magana bare tabada amsa, daga idon dazatayi taga kofar gida a bude tai waigen duniya amma bataga KAUSAR ba mikewa tayi tashiga cikin gidan, tana shiga taji an gark’ame kofa garam saura kadan ikram ta kifa saboda tsabar tsoro, tace “Wa’inahu sulaimana wa’innahu bismillahi innanallahi wa’inna ilaihir rajiun Allah ka mun tsari da mugunji da mugun gani nashiga tsaka mai wuya inzan dosa ni Ikram? ”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button