DASHEN ZUCIYA

Kutsakai tayi cikin daki taga an shirya mata abinchi mai rai da motsi Wanda iya ganin kayan kyale kyale Wannan bata taba ganiba Ikram tace “Daman ance dakwai iska masu taimako dakwai kuma azzalumai wayanda burinsu su cutar da Dan Adam amma ina shakkan cin abincin nan kar yazo wata rana suce saina basu wani Abu don in biyasu” magana taji daga k’uryan daki “Kici da zuciya daya Kituna Abunda nace baki ba kunci a rayuwa ” wani hocky voice taji jiki na rawa ta juya amma bataga kowaba, tashi tayi taji ance
“koma kizauna kidaina wahalar da kanki Sannan kidaina sa damuwa cikin ranki kuma Karki sake kikai kara gidanku domin babu Wanda zai aminche da Abunda zakice saboda yardan dasukayi da mijin naki Sannan yana mutuntasu fiyeda yadda kike tunani”
Zufa kawai Ikram takeyi saboda wani mugun tsoro datakeji, haka ikram taci gaba da rayuwa cikin jin dadii lokaci guda ta sauya bata zubda hawaye koh kwaya duk lokacin da KAUSAR yashigo da yan mata har sannu da zuwa take musu amma saidai wani Abu guda duk yar dayayi tarayya da ita saita mutu, Abunda yakoma tadawa KAUSAR hankali kenan yafara tunanin kodai wata cuta gareshi?.
Wata ranar lahadi ta tashi da nakuda, mai tsanani Wanda bata iya tashi bare ta nemi taimakon wani , KAUSAR naciki shida budurwarsa amma koh kallo bata isheshi ba haka ta haihu cikin galabaita haka Allah yabata karfi ta yankewa Dan cibiya uwa tabiyo baya haka tasamu ta gyara jikinta, tasa ruwan zafi ta yiwa danta wanka kamar wacce tayi haihuwa biyar, acikin zani ta kudundune Dan saboda koh pant KAUSAR bai siyaba haka tayi wanka kamar bata haihu ba, waya ta dauka ta aro kudi takira gida takira Ruma har Mujeeba saida takira tasanar da ita cewa ta haihu ya mace, jin tana waya ne yasa KAUSAR saurin fita ta kofar baya tunda tabar gidan koh waige sai ma aiko wani abokinsa yayi daya radawa Dan suna saboda baimasan meta haifaba.
Gida tuni yafara cika da mutane amma babu kaya ajikin jaririya zuwan abokin sane yaje yasiyo gobe suna akasamata, haka ya radawa Yarinya suna *BUSHRA* Ikram tayi farin farinciki haka yadinga bata hakuri akan halin abokin nasa koh kadan bata nuna mishi bacin ranta ba.
Ni Humairah nace da wuya asamu mata irin ikram azamanin nan damuke ciki, irinsu ikram basuda yawa masu shanye bakin cikin Namiji, yan uwan KAUSAR sunzo dana Ikram sunzo Amrah ma makociyarta tazo amma babu Wanda yasan halinda take ciki illah Amrah da ruma datake Yar’uwarta sune kawai sukasan dawar garin, Ummi tuni ta aiko da kayan jariri da take siya na tari itamai yaya mata.
Haka Allah ya rufawa Ikram Asiri amma dayawa mutane sun gane cewa Ikram batajin dadin gidan kausar musamman yar mahaifinshi datakeyi mata wankan jego, Anyi suna anyi shagali amma babu KAUSAR babu labarinsa Ikram harta manta da KAUSAR ragon suna ma mahaifin KAUSAR ne yakawo, haka kowa ya watse sunsamu kaya Wanda sai wanda yagani bushra tayi goshi.
“Abokina wallahi narasa yadda zanyi in maido da Mujeeba kusa dani wallahi Inajin sonta acikin zuciyana sosai gashi ita batada niyyan cewa zata biyoni Mujeeba tanada qualities din da kowani Namiji zai yaba gashi babu inda tabar bisma Tabbas Allah yayi gaskiya dayace Ku rok’eni zan amsa muku da gaggawa, Abokina inata rokon Allah daya musanyamun Da wacce zata mayemun gurbi toh Allah ya amsa”
“Nuru kenan Tun farko Kaine kaki jin shawara kawani ce ba yanzu zaka tareda itaba kaga yanzu saika yi hakuri kaxubawa sarautar Allah ido”.
NURU ta turnuke fuska yace “mafita nake nema shiyasa nagaya maka amma kana maida hannun agogo baya ” mtwww tsaki yaja ya juya fuska.
[2/26, 3:19 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
4⃣4⃣
“Abokina bakasan yadda nakejin Mujeeba acikin raina da gangan jikina ba bakasan, yadda sonta ya mamaye ilahirin ruhina ba, Abokina ina ganin mutuwar Bisma kaman komai ya kwance mun amma sai naga akasin hakan pls abokina meye mafita bansan yazanyi da Rashin Mujeeba akusa daniba ka taimakeni” Mu’ammar ya karewa NURU kallo yace
“Nuru waishin meyasa ka gagara gayawa Mujeeba irin wayannan kalaman ina gani da tuni ta aminche da kudirinka nasan itama a halin yanzu kai kadai zaka iya bata agaji, Nasan cewa furucin bakinka kawai takeda buk’atan ji Wato kace kana sonta face to face kaga irin murna da farincikin dazatayi banaji kace tanada wayaba? Toh tanan ai zaka dasa mata mashin sonka text safe da rana waya akai akai hakane zai nuna mata cewa itama macece mai jida kanta”.
Haka suka ajiye shawara haka yafara gwada fasaharsa, waya safe rana dare yana gida yana office baya gajiya har hajiya tafara fuskantar abunda ke wakana, don daxaran tace Mujeeba dawakike waya zatace da yayane, haka sukafara son juna kamar zasu cinye juna har takaiga Mujeeba tafara dauka zafafan hotuna tana turamai
Wayar Mujeeba ce keta ruri cikin sauri ta daga
“Hello dear”
NURU jiyayi kaman bisma ce ta amsa amma saiya basar
“Mujeeba daman inaso in sanar dake wani Abu Dana Dade ina fatan Allah yakawo mun ranar dazan iya furta miki Wannan kalman” yana xuwanan ya dakata yace zai kirata anjima yanada baki.
Haka Mujeeba ta k’agu dataji abunda zai sanar da ita, Wanda tayi hasashe cewa bai wuci yace yana sonta abunda ta Dade tana jira taji daga wajenshi.
Ashwa itama ta kamu dason mansir Wanda gaba daya yake bata kulawa ta musamman batada wani aiki saina shigewa daki suyita zuba love, abun mamaki da baya k’arewa Wai shima mahaifin mansir son Ashwa yakeyi saboda budurwar zuciya tun ina gani yana faruwa a TV wasan kwaikwayo gashi a zahiri yana shirin faruwa, Dukda basu taba haduwa da mahaifin mansir ba amma yana kashe mata kudi na fitar hankali, itadai fatanta da Adu’arta Allah yayi mata zabin abunda yafi Alkhairi.
Datake ba Mujeeba labari bakaramin razana tayiba saboda tsabar mamaki, Tabbas idan kabi ta bado saika yi nutso cikin kwaru,
“Ashwa ki lazimci adu’a tsakanin ikama da kabbaran harama bakaramin amsa Adu’ar bawa Allah keyi a Wannan yan tsakanin ba, don kina bukatan adu’a” Ashwa tanisa tace “Mujeeba wazan zaba uban kodan? Tambayan danakeyiwa kaina kenan ”.
Nidai anan saidai ince Allah yaraba kwarto dashan duka.
Mujeeba sunata shirin xana Waec da neko harda jamb don suna ajin karshe a makarantar secondary dake therbow school dake zaria, tafe suke sun Dawo daga school direba ya daukosu wayarta tafara ruri duban screen dinta keda wuya taga Ya nuna Nurul-Qlby murmushi tayi ta gyra xama da dauka.
“Hello”
Daga dayan bangaren nuru yace “Kiyi hakuri jiya inata zuccin zuccin in kira ki amma nagaji da yawa Mujeeba ina daman so nake ince miki” dukta sakan kance tana jira ya gayamata abunda yake bakinsa yakara cewa “Oh Mujeeba kiyi hakuri Dan Allah Zamu shiga meeting ne” lok’aci guda taji ranta ya baci kashe wayan tayi.
“Yaya Kullun burinsa yajamun rai I wonder abunda yakeso ya gayamun”
Kiran ya k’walam tayi suka gaisa da jood’a mahaifinta tace
“Inna ina kewanki ina Ummi intana kusa kibata mu gaisa, ummi ce ta amshi wayan suka gaisa da Mujeeba “dafatan babu wata matsala Mujeeba? ”
Mujeeba tayi dariya tace “Babu Ummi kawai son ganinku nakeyi kawai Dan Allah kiyiwa yaya magana idan yazo ya taho dani shinkafi, Ikram ta haihu banzo barkaba”.