DASHEN ZUCIYA

“Ina baki shawara Karki sake wannan yafaru don idan tafiki iyawa zata fiki kwashewa, ai ni koh tsohuwa ban yarda da itaba don idan batada ya zata bashi jika” Ruma tace
“Kwarai kam Hajiya nima saboda Dan aikin nan ne yasa na daukota, don a gidanmu Wallahi bamuda yan aiki har yau kuma har gobe ” .
Haka suka gama hiransu ta wuce gida abun Al’ajabi tun kafinta isa gida gabanta ke fadi
Hamdan kuwa ya sakankance Ruma sai dare zata Dawo Dan haka yadinga lagudan Hindatu dayake ta saba har cewa takeyi bataso ya daina shiko gani yake babu mai rabashi da Hindatu saboda tana sarrafa shi yadda takeso don harijace ko goma ne zata dauka, bude idonsu Ruma suka gani tsaye tarasa abunda ma zatayi sai hawaye dake zuba a kwarmin idanunta, Tsirara tasamesu babu koh sutura Hindatu kuwa tashiga rudani don tasan ajalinta tazo.
“Hamdan Nagode Kwarai wannan shine sakayyan dazakamun koh Allah yasani ban Gaza a kowani fanni ba da wannan shirmen Wallahi da auro Hindatu kayi insan cewa aurenta kayi amma meye ribar Zina banda bala’i da masifa sannan baxai tseratar dakai daga shiga wutaba ke kuma tsohuwar muna fuka yau sanayi ajalinki yar iska kawai Mara mutunci, shake Hindatu tayi tadinga dukanta saida taga bata motsi sannan tabarta takoma kan Hamdan tace zamana dakai yakare saidai ka auri yar aiki kuxauna tare amma Kasani Rashin haihuwana saina shigar da kara kotu don abimun hakkina, idan kaki sakina anan Kasani nice kotu zaka bani a bainar duniya inda zakaji kunya Alhamdulillah bani da yaya a tsakanin mu damunsha kunya amma dayake kai dayane sai kasha kunyarka.
“Ruma Wallahi bazan taba rabuwa dake ba zama daram kidauka kaddara ne Ruma sharrin shaidanne, kuma kisani kinada laifi kin fifita aikinki akan sauke hakkina daya rataya akanki, bakida lokacin dafamun abinci da kanki sannan, awajen auratayya kinada rauni ki gafar ceni Ruma”.
“Dakata shine ka zab’i ka cimun mutunci saboda wayannan abubuwan karasa wacce zaka nema sai yar aikina? Hamdan kayi kuskure kuma aure dani dakai babu saida wata Ruman amma baniba” fuuuuuu ta fice daki tashiga tana kuka tace nashiga uku Hamdan meyasa kaci amanata? Meyasa ni humairah nace ihu kikeyi Bayan hari keda kanki kika debo kaimami kuma yazo yaji miki rauni,
_*Da yawa mata suke jefa maxajensu ga halaka, suke kashe aurensu da Kansu nasan cewa zamani yanzu ya canza mata suna fita neman halaliya suna karatu amma Meyasa bazaki sauke hakkin daya rataya akanki ba kina ganin Allah baxai tambayeki ba? Hmm mata iyayen shagali sai Abu yafaru ace haka Allah yaso bacin ke kika sowa kanki*_ Haka hamdan yayita kokarin shawo kan Ruma harta sakko ta hakura amma fa da sharadi saiya auro Hindatu yakawota cikin gidan don shine kawai kwanciyan hankali, haka Rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Hamdan harya auro Hindatu Bayan tayi *ISTIBRA’I* wata uku wato jini uku, inda Ruma take gasa mata gyada a hannu lokaci daya suka dauki ciki murna wajen Hamdan baa magana saidai mujira haihuwa.
[2/28, 12:03 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
5⃣0⃣
Anata shirin tarewa MUJEEBA tana ta kaiwa da komowa haka yan’uwa suka baxama zuwa Zaria achan akayi Jere aka shirya komai Hajiya tayi musu tarba na mutunci ranan Alhamis aka shirya liyafar ban girma a garin Gusau, Duk Wanda yaga MUJEEBA saiya tofa kowa ya halarta bikin harda Ruma dake laulayin ciki harda Hindatu abun tausayi batako iya shiga mutane saboda kyrar da Ruma take mata, har saida Ummi tayi mata magana tace
“Amma Ruma kina ganin Allah baxai sakawa yarinyarnan ba jitafa yadda ta rakube toh wallahi ki daina wannan zalunci ne kiriketa Wallahi wata rana zakiyi alfahari da ita, kisani Ruma zakaran da Allah yanufa da chara koh ana muzuru ana shawo sai yayi ki rike girman ki kishinki azamanin nan aljihunki maza ki kirata ta zauna kusa dake an riga an daina irin wannan kishin” haka Ruma takira Hindatu suka zauna tare har hira sukeyi dayake katon gidane shiyasa aka kira masu decoration suka k’awata wajen.
Kayanda MUJEEBA tasa abun azo a ganine Ashwa kuwa tamance da wani mansir tacigaba da harko kinta, itama tadau kyau Kwarai saboda tsabar fari Wasu cewa sukeyi MUJEEBA tanada jibi sa yan India shiko NURU banda huta dayadan ratsashi bakine Kwarai, sai idanu ka tsawo abun sai Wanda yagani, baba lanti kuwa gaba daya hashin NURU takeji saboda taso ace yarta Labiba ya aura amma iyayensa suka zabamai MUJEEBA amma fah taci alwashin sai yarta tashiga gidan koda boka koda Malam,
Baba lanti yar Alhaji Usman ce itake binsa haka hajiya taci bak’ar a zabanta don har saki Alhajin yataba yiwa Hajiya saboda ita.
Haka akayita shagali saboda tsabar haushi labiba tashi tayi tafice sai gida saboda arayuwanta tana masifar son NURU shiko koh gidansu baya zuwa, bare ya kare mata kallo.
Haka aka watse abokan NURU sunata yaba kyawun mujeeba yace
“Ku dakata matata ce meyasa kuke irin haka ba kusan cewa haramun bane yaba matar daba takaba?”.
Dariya sukayi washe gari aka kawo motoci kusan goma haka akayi sakko sai Zaria, inda akakai mujeeba dakinta, gida ya tsaru iya tsaruwa haka suka Kwana aka watse, Kanwar Ummi ce takira Mujee tace
“Wannan ya k’walam tace in baki kidinga sha saboda akwai yan bakin ciki tsarine sosai kuma tace zakuyi waya”
Karba tayi ta boye haka washe gari akayi mata fada aka watse shiko ango NURU yana garin Zaria don an bashi hutun wata guda, kunga amarci sai anci anji ba dadi,
“Misalin shida na yamma NURU tashigo Ashwa ya tarar suna hira tana ganin yashigo tace
“Allah ya bamu Alkhairi”Nuru yace
“Amshi ki kaiwa hajiya” haka tafita tabar Mujeeba a zaune ta kudundune fuska, tana wani irin shu’umin dariya tuni NURU ya matsa kusada ita yace yau dai gaki ga yaya Nuru, lokaci guda yafara tuno wani Abu tuni yaji hankalinsa ya tashi ji yayi bazai iya kwanciyan aure da Mujeeba ba don gani yake Tabbas yaci amanan BISMA, ganin Nuru ya sauya ne yasa Mujeeba zare ido tace
“My soul and heart lafya naga dukka canza koh nabata maka Raine? Girgiza kai kawai yakeyi saboda wannan tsakaninsa da zuciyansa ne.
Haka ya daidaita kanshi ya rungume Mujeeba yace
“hmmm kiyi hakuri Mujeeba wata sa’in nakan rasa tunanina ta kowani fanni sai inji duniya inama banzo ba, narasa meyasa Wasu abubuwa suka kasa bacewa daga kwakwalwa na,”
Dayake Mujeeba yarinyace mai fasaha tuni tagane abunda yake nufi itama saita nuna bakomai
“Damuwa dolene musamman idan karasa muhimman abubuwa, a duniya nima idan na tuna yan’uwana dangina da dukiyar mu Wato shanu hankalina yana tashi” lokaci daya tafara kuka lallai damuwar mujeeba tafi nashi tunda shi Alhamdulillah yanada dangi harma da dukiya.
Lallashinta yakeyi har suka fara dariya har bacci ya dauke Mujeeba a kan kafarsa nidai nace waiyo Mujeeba kinsamu soyayya wajen NURU amma har yanzu da sauran Rina a kaba, dakyar nuru sai iya saduwar aure da ita, gashi Mujeeba ta jik’u iya jukuwa Tabbas dakwai matsala Ku biyo ni yar MUTAN ZAZZAU kuji yadda zata kaya don nasan dole asamu mafita.
*kuyi mun afuwa banso littafinnsn yayi tsawo ba amma babu yadda na iya saboda labarin bai karaba*????????????❤
[3/1, 3:33 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*