DASHEN ZUCIYA

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
5⃣1⃣
_*Washe gari tun da sanyin safe Mujeeba ta tashi Bayan baccin Bayan Asuba data koma, kitchen tashiga yaba kallon tsaruwan kitchen din babu wani colour rayot komai kala daya sai abunda baa rasa ba, dube dube takeyi har idanunta suka hango wani lungu ba tantama store ne wajen ajiye kayan abinci, gurin ta nufa tafara kici kicin daura abinci tuni tayi Abu Mara nauyi ta jera akan dinning table daki ta koma ta fetsa wanka tasa atampha super Exclusive tayi dauri mai Wanda ake kira da network sannan ta fesa turare kusan kala biyar, takalmi ta dauka plat Tafara tafiya cikin natsuwa cikin dakinsa ta kutsa ta zauna kusa dashi Tana hura mishi fuska yana bude idonsa yayi tozali da Mujeeba, tace “Good morning my prince ka tashi lafya? Yakamata ka tashi kayi brush muyi breakfast ”*_
_*Murmushi nuru yayi yanajin tsananin son mujeeba acikin ransa yace“Hmmm Mujeeba kenan har kin tashi lallai bakison ki kwanta ki huta koh” cikin shagwaba tace*_
“My nidai ka mik’e Muje inyima brush pls wani fari tayimai Wanda yaji jikinsa ya mutu, Tashi yayi suka shiga toilet din ta taimakamai sannan sukaci abinci, Rayuwa suke kaman ba ma’aurata ba kamar wa da kanwa abunda yake munana zuciyan Mujeeba kenan.
Tashi tayi zatayi Alwala Ta rik’e maranta wani kara ta saki Wanda yajawo hankalin NURU, tuni ya ajiye jaridar hannunsa Da gudu yashiga toilet yaganta kwance sai juyi takeyi, baiyi wata wata ba yafara salati daukanta yayi cik, yana zuwa falo yadauki mukulli yana fitowa yadinga kwad’awa Ashwa kira Hajiya ce tafito a gigice hankalinta yayi kololuwan tashi hijabi ta dauko sai
*SALAMA MATERNITY HOSPITAL LTD* dake cikin unguwan kwangila, dake Zaria daura da flyover cikin gaggawa aka karbeta batareda bata lokaci ba, likitoci ne suke dubata tuni akayi gwaje gwaje aka gane cewa maniyyinta ne ya taru a mararta shiyasa ta matsanancin ciwon Mara.
Cikin tashin hankali Hajiya ta juya ta kalli NURU tace
“kaji abunda Likita yace koh bakaji ba Wato yarinyarnan haka kake azabtar da ita toh Wallahi Kasani Allah baxai barka ba matsawar kace abunda zakayi kenan”Likita yace “Inason magana dakai”nuru ya sadda kai yabi bayan likita, suna shiga Likita yafara wayar mishi dakai sannan ya sanar dashi illolin dake tattare da barin mace da sha’awa nanya bashi shawarwari ingantattu Wanda NURU yayi alkawarin gujewa afkuwan hakan.
Fita yayi duk yaji kunyan Hajiya takama shi haka Mujeeba ta farfado suka wuce gida, haka NURU yake tarairayanta kamar kwai, yana lallabata hajiya ta leko tace
“nuru Inaso kasan wani Abu hannu mai miya shi akebi da lasa ” tana gama magana ta wuce adaren ranan Mujeeba tasan inda yake mata ciwo duk wani rawan kai taji babu shi taji maza, NURU yayi ihun dadi yayi godiya ga Allah sannan yayiwa Mujeeba godiya ji yake duniya ina Zaisa kanshi idan yarasa Mujeeba?.
Haka ya taimaka mata ta gyra jikinta sukayi sallah suka koma bacci abun mamaki nuru ya biyayi Mujeeba saboda jinta yakeyi on top the town.
Ashwa kuwa love akeyi sosai da mahaifin mansir inta kaita ma mai karatu har ansa rana, kishi da uwar mansir dole Ashwa tace “waiyo Allah sarki inji barawon takanda duniya sabuwa ango da daurin zani,” mansir duk yabi ya damu yana Neman yarinyar da ubansa zai auro kwatsam yaji ai Ashwa ce kofar gidansu yaje ya aika a kira mishi Ashwa tace aje ace waya mansir ya takarkare yakira sunan ubansa, cikin takama tafito lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi ras, amma saita dake ta karasa tace
“Barka da zuwa Dana dafatan kaxo lafya kodai ya aikokane? naga kazone kamar saukan mankade”
“Kwarai kuwa zuwa nayi insanar dake ki nisanci auren ubana idanko kikaki duniya tayi miki gwatson mage in kunne yaji gangan jiki ya tsira” buda Ashwa tayi tace
“Aure ba fashi nanda watan gobe kasan cewa duk rikan kadangare bazai zama kada ba don haka yaro bar kofar gidannan kafin in Tara maka mutane suyi mun butu butu dakai”
[3/2, 7:52 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
5⃣2⃣
Ba shiri mansir ya wuce sum sum amma hankalinsa baya tareda dashi yaza’ayi budurwarsa ta auri ubansa ai wannan abun kunya ne bagashi kadaiba har a wajen abokansa itako koh a jikinta Tashige gida, mahaifiyar mansir kuwa kamar tayi hauka har gidansu ashwa tazo tana mata barazana,
“Ke malama kiyi hakuri ki dauka kaddara ne don aure da mijinki ba fashi inda nice ke wallahi baxan tada hankalina ba koh kadan zanjene inta adu’a Allah yabada zaman lafya”
Shigewa tayi tabarta tsaye tanata haushi Mujeeba ta lek’o tace
“Ashwa memuke jira da ita tunda bakowa suka kulle gida sukaci wando sukayi mata dukan kawo wuk’a Ashwa tace “Sharia muzuba nidake kinsan duk inda mukaje kece Mara gaskiya ke kika biyoni don haka kinyi a banza”
Haka mahaifiyar mansir ta mik’e tana dinkishi sai gida, hankalin yayanta ya tashi baran ma yar budurwa saboda tana masifan kishin mahaifiyarta,
“Maman Mu kema banda abunki maiya kaiki kinsan cewa ko kotu akaje kece bakida gaskiya kiyi hakuri mama tunda aski yariga yazo gaban goshi…. Bata gama rufe bakiba saiji tayi ance
“Banji dadi da basu kassara kiba wallahi tunda ke bakida mutunci, da izinin wa kika fita gidan toh kisani aure sai nayi saidai ki mutu, ina mansir shima ina gargadinsa matsawar bai shiga taitayinsa ba”
“baban mansir menene banayi maka dazaka yimun kishiya? ” mtww
“Rashin mutunci dacin zarafin yan’uwana sannan ribar wulakantamun uwa da kikayi harta koma ga ubangiji shine wannan auren dazanyi wallahi kin cutar dani saidai Allah yayi mana sakayya”
“Sa’ar Mimi zaka auro yaza’ayi inyi kishi da yata yar cikina naji ance budurwar danka cema”
“Look indo wannan duk surutan banza kikeyi ba gida daya zaku zauna ba zancen mansir kuma wannan kedashi ne tunda dai ba abun kunya bane ya aureta Na aureta saikiyi hakuri” fuuuu yafice yana surutai, biki sai matsowa yakeyi lokacin indo take nan nan da yan’uwansa sai binsu takeyi suko tuni suka Riga suka gano inda ta dosa.
Shirye shirye akeyi sosai amma babu wani reception kowa daga zamfara gida yacika Ummi ce tazo ya k’walam gema dagas taki zuwa saboda kunya, ita aka bari sai jooda da girma yafara zuwamai, gidanta a hanwa Lowcost yake yaji komai da komai babu abunda baasa ba Andaura aure nisalin karfe shida aka kawo motar daukan amarya tasha fada sosai Wanda saida taci kuka kaman ranta zai fita ankai amarya kowa ya watse sai Mujeeba datake jira axo a dauketa, gida ya tsaru baran ma kitchen, duk basu gama secondary ba akayi musu aure amma anbada makudan kudi ayi mu komai,
Misalin Tara nuru yakira Mujeeba tafito su wuce nanma Ashwa tayi kuka amma yata iya sai hakuri, fitansu keda wuya mansir yayo zuga mai uban yawa hayaniya kawai Ashwa taji tana lekawa taga matasa da adda wuk’ak’e ai tuni taci hanjin cikinta sun kad’a sanda kawai takeyi har saidai takai gun wata kofa ta bude a hankali, tana bi a hankali Ashe gidan kofa biyo ce dakwai barauniyar hanya, cikin ikon Allah ta sameta a bude tuni ta bude kafa mai naci ban bakaba, wajen tsallaka titi ne wani mai mota ya banketa fitowan daxaiyi ashe mijin natane tuni akayo kansa, Ihu kawai takeyi yana kiran sunan Ashwa amma ina jiki Na bari ya sunkuceta sai asibiti, bakaramin rauni tajiba har ake sanar dashi cewa tana bukatan Dashen zuciya tuni hankalinsa yasake tashi yarasa wazai kira ya fadama halinda amaryar dako kwana daya batayi acikin dakinta ba, tabbas idan yagano musabbabin fitowanta kowaye sai hukunci yahau kansa.