DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Haka yakira gidansu Ashwa yasanar dasu ai Mujeeba tuni ta sulale tafadi asume tuni aka yayyafa mata ruwa tayi firgigit ta bude ido tace “Kar kucemun Ashwa tashiga halinda nataba tsintar kaina aciki waiyo ni duniya inaxaki damu, zabura tayi aka riketa tuni ragowan yan’uwa suka bazama Salama hospital, dayake babu nisa tsakaninsu haka suka taradda Mijin nata dukunnar dakai yana kuka maicin rai haka aka bige da bashi hakuri shiyasa sanar dasu komai, haka likita yafito yace Ku kwantar da hankalinku munasa ran matsalar mai saukice inajin batama bukatan dashen zuciyan, murna wajen kowa saida tayi wata daya cir a Asibiti aka salla mesu, gidanta aka kara maidata sai masuyi mata hidima shiko mijin nata tuni yasa aka kama mansir da duk wasu abokansa sai gidan yari daurin shekara goma ne duk Wanda aka kama da makami, kuma ba beli indo tayi kuka shiko koh a jikinsa.
Tuni sauki yasamu Ashwa aka dinga cin amarci duk Wanda yaga kulan da Dan tsohonnan yakeba Ashwa ai koh Mujeeba albarka, saboda yasan darajar mace shiyasa soyayya da tsoho ka aureshi ba aibu mutukar babu talauci aciki.
[3/2, 8:59 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

5⃣3⃣

Akwana a tashi babu wuya wajen Allah Kamar, haka Mujeeba tasamu juna biyu murna wajen nuru baa magana bashida wani buri a rayuwa illah ya farantama Mujeeba karshe Zaria yadawo da aiki, ABU suke zuwa direba garesu Wanda mijin Ashwa Alhaji bala mai vespa yasama musu, karatu suke babu kama hannun yaro, hajiya tana iya kokari wajen kulada Mujeeba haka Mujeeba take mutunta hajiya dama sauran dangi, Mujeeba tasamu kyakkyawan shedan mutanen gari harda makota, karatun likita takeyi saboda tacika gaba daga inda bisma ta tsaya, amma wani hanxari ba gudu ba labiba tuni ta tattaro kayanta ta dawo Zaria inda ta hana Mujeeba rawar gaban hantsi duk abunda tayi saita kushe ita kuma intayi ya kwabe, Mujeeba tashiga damuwa har takaiga tambayan nuru waishin wacece labiba, tuni yasanar da ita koh ita wacece sannan ya sanar da ita kudirinsu na ya auri labiba shikuma bata acikin tsarin matan dayakeso shiyasa baya sakar mata fuska.

Da sanyin safe ne Mujeeba ta shirya tsaf zata school fitowan da zatayi ta dauki lab coat dinta, taga anyi mata butu butu dashi tace
“inda jakku baba bankumajo wane Dan tsiyanne yamun haka toh koh yau da ruwan masifa acikin gidannan ba kwammace in fadi jarabawan akan wannan danyen aikin, wallahi duk ma Wanda yayi yafito imba hakaba yasin sai anyi k’aramin yak’i acikin gidannan, Nuru dake shirin fita office ne yaji hayaniyan Mujeeba abunda bai tabaji ba ko ada bare kuma yanzu,
“Wai Sweet kedawa kike hayaniya?”
muje tace
“nidawa banda akuya meeeeeeeeh kawai har wata halitta ta isa ta shigo gidan mijina tace zata fini fada toh wallahi wallahi ba’ayita ba”
Nuru yace
“wai me aka miki Kituna abunda ke jikinki baya bukatar tashin hankali pls sweet kiyi hakuri muje school din in siya miki sabuwa idan har kikayi missing Exam dinnan wallahi baki ba zuwa horsemanship”.

Gsjiya dake tsaye ta harde hannu tace
“Mujeeba kiyi hakuri kinji nasan cewa kemai rama sharri da khairan ne, Duk abunda mutum yayi don kansa”
Mujeeba tace toh amma kasan Fulani da ruko haka ta wuce makaranta ranta babu dadi saida nuru ya siya mata sabuwar riga saura minti UKU a rufe hall Mujeeba tashiga nuru yaji dadi sosai.
Wayarsa ce keta ruri bak’uwar lambace Etisalat, saida tayi ringing biyu ana UKU yadauka
“Hello yaya labiba ce ina kwana?”
Keeee yadaka mata tsawa“Ki kiyayeni wallahi meye dadi acikin kwanan daxaki tambayeni ina take pls look labiba wa’adin zamanki a Zaria ya kare gobe zaki wuce gusau don bazaki rudamun gidaba mtweee”ya kashe wayan yasata a blacklist, sakato tayi tace
“naga takaina duniya tabbas yaya Nuru ba ajina bane yayi nisa bayajin kira an gama dashi anjikamai ya dinkirama cikinsa amma inyasan wata toh baisan wataba”.

_*Waiyo Shikenan idan anga miji yana haba haba dakai shikenan anyimai asiri wallahi yan’uwa muji tsoron sarkin Mu, musamman yan’uwan miji wallahi kuna daukan babban zunubi, kyautatawa yanasa miji ya kaunaci matarsa, iya girki, kwalliya, tsafta, tattausan lafazi, hakuri juriya, da kai zuciya nesa, lallami, iya kwanciya, gyran Jiki wallahi dole namiji yayi zakwadin matarsa babu boka ba Malam abunda wasu matan basu ganeba kenan shiyasa karuwa take saurin am she miki miji saboda tsabar makaman tsaro da take dashi*_ Allah yasa mudace Amin.
Dawowar Mujeeba gidane taci karo da labiba tana waya tana kwarkwasa
“Yaya nuru wallahi nak’osa ka dawo gida I miss you” wai ita bariki Mujeeba tayi dariya tayi shewa tace
“Amma anyi asaran kudin tara indai Mujeeba ce nan gani nan bari Nuru kuwa, saidai jifa nidashi mutu karaba takalmin kaza, duk wani karatunki na iya saidai ki kara wani nasan koda second my belove husband will never give you a tiny space in his heart bare har kiyi waya da my humble love.
[3/4, 4:38 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

5⃣4⃣
_*Ina mika cikakken ta’aziya zuwa ga ILILEE a bisa rashi Aunty dinshi dayayi Allah yaji kanta yasa ta huta ya yafe kura kurenta ya raya abunda tabari Amin ya Allah????????*_

 

 

 

Banda ke gara aiba haka akeyi don kwatan abunda kakeso ba kinga tafiyata” tsaki Mujeeba tayi ta wuce kafin takai bakin kofar Hajiya tuni labiba ta dauketa da wani wawan mari Wanda saida Mujeeba taga wuta, daga bayanta Nuru ta dauketa da mari yace “Babu wani nahaluki daya isa ya tabamun mata banyi fito nafito dashiba, kisani har abada bazaki taba zama matata ba inshort gwara ma kin kwashe tsumman kayanki ki wuce inda kikafi wayo banza karya Mara zuciya”
Juyowa yayi yana kallon Mujeeba da fuskarta tayi jajir abunka da farar fata rike take da kuncinta takasa cirewa, babu abunda ke kona mata rai irin ramawar dabata samu tayiba, ni HUMAIRAH nace banda abunki ai taji hannun maza,
“Kiyi hakuri pls precious queen ki yarda dani babu wata mace bayanke, wannan itace mace tafarko data mareki kuma ki tuna na nuna mata kuskurenta kiyi hakuri” turbune fuska tayi tace
“tabbas zan iya barin gidannan matsawar an kasa daukan mataki akanta don zan iya kassara mutum in watsar banda rainin wayo azo a isheka har gida” haka nuru yajata sai daki, washe gari labiba ta kwashe komai nata sai Gusau ranta cikeda Dana Sanin zuwa gidan kuma duk inna ta matsamun gashi taja an cimun mutumci dawannan ta is a gida.

3years later
Mujeeba ta haihu da namiji, mai suna Usman Wato sunan surukinta akasa, Ashwa kuwa gwarne takeyi yayanta biyu duka maza, Nuru yana matukar son Mujeeba saboda hakurinta da hangen nesa batada wata damuwa bare matsala, hajiya ba karamin dadinta takejiba, saboda ba a gidaba hatta a waje shedar arziki ake mata wajen taimakon na k’asa da ita batada kyashin yimaka hidima kota nawane, bata damuwa da abunda tabaka, shedar duniya itace ta lahira toh Mujeeba tasamu kamar yadda Bisma tabar duniya, mutanen cikinta na yaba mata, Mujeeba batada rowa shiyasa yan’uwa suke cewa Itace Bisma ta biyu rayuwarsu sukeyi mai tsafta, haka ta kammala karatunta tazama babbar likita a Asibitin jami’an Ahmadu bello dake Zaria, karatun da kowa yake alfahari dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button