DASHEN ZUCIYA

Ikram ce zaune cikin gidanta aka doka sallama jiki ba kwari ta mike ta ajiye bushra, fitowanta keda wuya taga yan sanda har UKU tuni ta zare ido tace
“Lafya bayin Allah wa kuke nema?”
“Mijinki muke nema mai gidannan, ana zarginsa da kisan wata yarinya yar kimanin shekara 20 wacce report ya nuna cewa saurayinta ne shi kuma a yadda zancen ya nuna sun kama hotel ne wajen hutawa, haka bayan yayi amfani da ita Allah yayi mata rasuwa, har yanzu likitoci basu fadi mak’a sudin rasuwar nataba” abun ya dameta amma kwata kwata Kausar bai bata tausayiba saboda ya cutar da ita kuma tabbas Tasan karshen alewa k’asa,
“Kuyi hakuri kusan sati daya kenan bansashi a ido ba amma Duk sanda yashigo nayi muku Alkawarin damkashi a hannunku koda duniya zata zageni, bakincikina daya Bushra wacce batasan me duniya take cikiba”
Godiya sukayi suka wuce suna xancen cewa itakanta matar tasa batajin dadi.
Bayan k’wana biyu da zuwan yan sanda sai gashi tuni ikram ta sanarda su sukaxo sukasa masa handcuff sai station, tuni ikram ta koma gida, haka akayita tafka shari’a kamar ba gobe karshe dai an gano cewa bashida hannu amma kotu tabada ixinin a kaishi gidan yari na shekara ashirin da biyar saboda case din kaman na fyade ne.
Haka akayita yadawa kafin a tafi dashine Ikram ta bukaci Alkali daya amsar mata takaddarta saboda batada raayin rayuwa dashi koh bayan ya fito, haka aka umurceshi yabata saki UKU reras babu jeka kadawo.
Haka kowa yake jinjina mata saboda babu Wanda yasan halinda take ciki sai makociyarta Amrah sai ruma, haka duniya ta dauka gidan redio harda jaridar Aminiya Dana daily trust, wannan shine kaddarar data fadawa Kausar saboda rashin kare hakkin iyalinsa bakasan cinsuba bare shansu yaushe zaka gama da duniya lafya mace ita yar Hutu ce, kuma ranar gobe sai an tsaida iyaye akan tarbiyan dasukaba yayansu, miji da mata wane irin kyauta tawa ne sukayiwa juna idan wani ya xalunci wani toh tabbas Dole akwai hisabi mai girma, haka Ikram taci gaba da training yarta amma tana tunanin anya Bushra zata auro saboda abun kunyan dayabar mata a idon duniya Niko humaira da Aysha sayedi mukace mace bata kwantai duk muninta aka auri shegiya yar gaba da fatiha bare gori akan abun duniya fatana anan shine Allah yasa mudace mufi karfin zuciyanmu Ikram taga ta kanta kuma komai yayi farko zaiyi karshe hakuri ribane gamaiyi yakamata yagani.
[3/4, 7:48 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
5⃣5⃣
Dole in gayawa duniya irin k’aunar da kukemun tabbas kun chanchanci in karramaku
*MAMAN MUJEEBA*
*MAMAN KHALEEL*
*AISHA*
*HUSSNAT*
*ABEEDA*
*ZARAH ABDULLAHI*
*UMMEE GEE*
_*Da sauran masoyana masu kirana da turomun sako masu yimun fatan Alkhairi Allah yabar zumunchi ysbar kauna ya raya mana zuri’a????????????????*_
Ruma da hindatu kuwa zama yayi dadi amma hindatu babu abunda take tsinta sai bakinciki daman duk Wanda yazubda tsakinsa a cikin yashi yasan abunda zai tsinta……………
Ruma ce ta kasance mai tausasa zuciyanta gashi koh primary batayiba bare azo zancen secondary yaxuwa jami’a, haka ruma tasamu tasata a makarantar yaki da jahilci dukda kudinta, don hamdan yace babu ruwansa, har takaita kawo yace shifa banda kaddara data fadamai babu abinda zaici da hindatu, Ruma tashiga daki tayi dariya ta daga hannu sama tace
“Allah Kaine abun godiya nasan cewa baka bacci, baka haifaba baa haifeka ba hmmm yau naga karyan rawan kan Hamdan yau gasu a rana fatse fatse Allah baya bacci kuma mai hakuri mawadaci ne wataran zai dafa dutse yasha romonsa ya more abunda hakuri bai bakiba wallahi uwar gida rashin hakuri bazai taba bakiba”wannan kenan.
Labiba ce xaune akan tabarma tana gayawa inna abunda ya faru budar bakinta tace
“Dolensa ya aureki dole muci arziki mubarshi inda yake auta guda ai kamar anyi” nidai HUMAIRAH nace tabbas duk abunda baasa Allah aciki ba duk shirmene, kuma dayawanmu haka muke magana kamar zarar bunu babu insha Allah aciki
Takanas ta kano inna tayi tattaki zuwa Zaria da isarta Hajiya tace
“Sannu da zuwa yaya anzo lafya?
“Dakata bana bukatar wata kalma daga bakinki aure dole a hada da nuru da labiba dan’uwanta ne jini yafi ruwa kauri king dole yar uwarsa tafi bare” Nuru dake tsaye a bakin kofa yaji cin mutuncin da takeyima Hajiya tuni yasa baki yace
“Inna ruwannan dabaikai jini ba ita nakeso nake kauna saidai labiba tabi wani sarkin amma baniba da ake zancen auren dole ba yanzu ba, maimakon kiyi mata fatan Alkhairi na samun miji nagari kin bige da Hadata da jininta Toh badai wannan jinin ba saidai kamal don inajin shine Wanda ya dace da ita bani ba”
Yana gama magana yayi waje Hajiya tayi zugudi tunda kuruciya Hajiya ke fama da yaya amma har zuwa yanzu bata hutaba, cikin dare ne da Alhaji ya dawo
Baysn sun gaisa take gayamai bukatunta budar bakinsa yace
“Idan har nuru yanason labiba babu Matsala idan koh yace bayaso ba zanyi mai dole ba saboda rayuwa babu dole musamman Wanda ya mallaki hankalin kashi” tayi matuk’ar mamaki tayi tunanin cewa zai goyi bayanta amma saitaga akasin hakan, a daddafe ta kwana washe gari sai tashi sukayi sukaga bata, Hajiya tace “Agayas mun yarda kwalon mangoro mun huta da K’uda” Mujeeba taba Hajiya hak’uri sosai tayita bata labari har zuciyanta tayi fari kal, koda yaushe hajiya tana alfahari da Mujeeba,
Usman sai girma yake dadayi haka kowa ke rubibinsa, inna kuwa sun bazama basu boka basu malam amma an gayamusu cewa auren bazai taba yuwuwa ba haka suka fawwalawa Allah suka hakura harta samu wani yataya akayi shagalin aure amma abunka da barbada kwana daya yasakota batareda yagadi dalili ba haka suka rungumi kaddara.
Mujeeba ta natsu sai haihuwa takeyi tana kara zama hamshakiya itakadai cikin gidanta tana wandaka hajiya koh ansamu mutuwar gefe daya, haka Mujeeba ta ajiye aikinta ta koma jinyar hajiyar Nuru, kusann Kullun saita shimata albarka, taci kashinta taci fitsarinta, Ashwa Kullun saitaxo duba hajiyar ranar wata laraba Allah ya amshi abunsa harta komaga Allah tana yiwa Mujeeba kyakkaywan fata, haka mutuwar Hajiya ta girgiza kowa ciki hard a Mujeeba datayi mugun Sabo da ita, amma babu yadda suka iya saidai fatan muyi kyakkywan karshe.
[3/5, 5:32 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
*LAST PAGE*
5⃣6⃣
Bayan wasu shekaru da damane, Su Mujeeba ana cikin kwanciyan hankali da miji, Alhaji Wato mahaifin Nuru yana gadon asibiti jikoki da yaya sun zagayeshi, da surukai Ya kalli Nuru yace
“Inaso ka auri labiba saboda banaso zumunchi ya lalace, Ya kalli jikokinsa yace kuma Allah yayi muku albarka kuda iyayenku, Yana juyowa wajen Mujeeba yace
Allah ubangiji yasa kikagama da duniya lafya, tabbas ke yar halak ce yadda Hajiya ta rasu tana mai yabon halinki haka nima zan cika yimiki adua, tuni suka fara kuka Mujeeba kuwa jingina tayi da jikin Nuru, yaci gaba da magana kizauna da abokiyar zamanki lafya insha Allah babu abunda zai faru sai Alkhairi sannan Ku kasance masu farantawa juna rai, shakuwace ta sarke shi aka bashi ruwa amma yace ah ah haka likita yace kowa ya fita daga Mujeeba sai Nuru, Alhaji dai da kalman shahada yacika haka akayita koke koke Wanda yaxaman ma mutane al’ada……
Bayan anyi kwana arba’in ne aka daura auren nuru da labiba amma badason ran Nuru ba biyayya yayiwa mahaifinshi kamar yadda ya umurta.