DASHEN ZUCIYA

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
6⃣
Ummi kallonta kawai take tasan za’a Rina, hannun bisma ta kama tace “kema fa naki” lokaci guda Bisma taji wani mugun dadii tayi tsalle sukayima Ummi Sallama suka kama hanyan Zuwa GRA biki.
Direba ne ya daukesu dayake an hanasu tuki, saboda rough driving da Bisma takeyi saboda sabo da kasar Florida,
Bakin wani hall sukayi packing lokaci guda suka fito kowacce sanye da Google a idanunta, yadda kukasan makafi wakane kawai ke tashi abun sai Wanda yagani, cikin tafiyar ka saita suka isa cikin hall din daman ansan da zuwansu kowacce kodata akeyi.
Guri aka sama musu a high table, inda manyan baki suke Bisma kawai ake kodawa likita likita kenan likita bokan turai, bakije Us a banza ba wallahi baba ba’ayi asaran kudin Tara ba, tashi bisma tayi ta isa wajen Mc tafara yimai barin Naira yan dubu dubu kawai take watsamai, saboda dadin washin dayayi mata.
Ba’a jimaba Aka fara Event wani Abu Bisma tagani daidai da shigowan Amarya da Ango lokaci guda zuciyarta tafara bugawa, Hamdan Munnir Hameed Weds Laila Ibrahim Wambai………….
Lokaci guda ta mike tace “Daman hamdan yaudarata yakeyi basona yakeyiba? Oh noo nayi regretting saninka Hamdan a rayuwana, amma yau saina bata maka ranar farin cikinka saina gayawa duniya cewa kai macuci ne maciyi amana kuma azzalumi Wanda baidau soyayya da muhimmanci ba, Hamdan menene don kace mun zakayi aure? What is dere?”
Dayake bamai saurin kuka bace ta zauna ta hakimce akan kujera dayake Bisma itace babbar kawa.
Itama Rumaisa abunda yake bata mamaki shine “tabbas wannan shine saurayina Wanda muka Dade munason juna har Alkawarin aure mukayi dashi shine zaiyi playing dina haka? Toh koh yadebo ruwan dafa kansa don saina canzamai halitta yadda matarsa bazata sake ganin kyawunsa ba”.
Bayan kowa ya zaunane aka bukaci babbar kawar Amarya Bisma Bassam Anka tafito lokacin Hamdan yaji wani tashin hankali lokaci guda ya mike zai fita Laila tace “babu inda zaka zauna tun dazu bakasan zaka fitaba saida Bisma zatayi magana kuma Sanin kankane babbar kawatace?”
Ai ba shiri yakoma ya zauna zufa kawai yake zuba ajikinshi lokaci guda yayi shar kab da zufa Kamar yayi wanka da ruwa.
Bisma ce tafito kan stage taga dubban mutane an taru saboda murnan bikin Hamdan da Laila, tace “ya dubban mutanen nan zasuji abunda hamdan ya tafka? Ya Laila zata daukeni? Ya makomar bikin Hamdan da Laila? I don’t care wannan yarage nasu”.
Farawa tayi da gaisheda kawarta Laila Ibrahim da Angonta Hamdan munnir, sannan ta juyo ta gaida dubban mutane sannan tafara gabatar da kanta a matsayin aminiyar Laila tabada tarihin Laila tun daga kuruciya harya zuwa yanzu, guri tuni yadau tafi sauka tayi daga kan stage din tareda loudspeaker din….
[2/1, 5:02 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
7⃣
Zagaye kawai takeyi tace “na hutar da Abokin ango ni Bisma zan Baku takaitaccen tarihin ango dafatan zaku bani kunnen baseerah?”
Tuni guri yadauka shiko gogan Hamdan yashiga rudani Wanda baitaba shiga irinshi ba, tuni idanunta sukayi jajir itako Laila abunne kawai yake bata mamaki, harde hannu wanta tayi don jin wane irin tarihi Bisma zata bada akan mijin daxa’a daura musu aure gobe?.
“Hamdan munnir Hameed kasaitaccen mayaudarine, sannan kwararre maciyi Amana, maha’inci Wanda baisan darajar ya mace ba, Tabbas ban zaci haka kakeba da tun fari banyi ginin tubaliba, da ginin kasa nayi da baxan damuba, munso juna lokacin muna Florida kayimun Alkawarin zaka aureni ka yaudareni da jahilan kalamanka Ashe dakwai wacce ka ajiye agefe donka aura toh kayi kuskure Azzalumi kawai kuma Allah baxai taba barinka ba”.
Ajiye loudspeaker tayi tayi waje da gudu, itadai ikram abun ya daure mata kai lokaci guda na hangi Rumaisa tana taku daya Bayan daya ta haukan stage tace “Nasan koba komai Ango yasan koni wacece”
Lokacin Hamdan ya zare ido yace “Nashiga uku”
Rumaisa taci gaba da cewa “Nima kaci amanata ka ha’inceni bantaba Sanin cewa kai macuci bane sai yau Allah ya toni asirinka da wannan kadai nabarka sauran hukunci yana gareki amarya idan har kin zabi zama da wannan toh, kinyi zaben tumun dare”.
Itama ajiye loudspeaker tayi ta fice daga cikin hall din itama ikram ta mike ta bi Bayan su, tuni guri ya rude Laila kuwa suma kawai takeyi saboda tsantsar takaici, tuni taro ya tashi ran kowa babu dadii,
“Gaskiya Hamdan is a player ji lokaci guda yayi playing mata biyu at the same time” wasu samarine ke magana.
[2/2, 8:00 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
8⃣
Cikin mota suka shiga direba yajasu, sai gida suna shiga gida kowa ya fada bandaki donyin wanka, ran Bisma a bace na Rumaisa a bace gaba daya haushin mutum daya sukeji Wato Hamdan, Ummi ce tashigo tace “wai lafya kuwa naga kunshigo kowa tayi jugum jugum maye ke faruwa ne?”
Kallon juna sukayi sukace “Ummi babu komai kawai bikinne babu wani armashi duk yadda mukadau event din ashe ba haka yakeba”.
Ummi tace “amma hakan ba Zaisa kushigo Baku gaidani ba, Toh kuyi maza Daddyn yadawo daga Abuja kuma nemanku yake bansan dame yadawo ba” tana gama magana ta fita tabarsu tsaye kowa hanjin cikinta ya motsa, Bisma tace “Nasan zancen Gizo baya wuce na kok’i”
Rumaisa tace “Nifa gaskiya saidai adagamun kafa saboda wallahi mazan yanzu tsoro suke bani sun zama horrors abun gudu”,
Ikram dake tsaye ta jingina da matakalan gadonta tace “Hmm nidai daman banida zabi duk Wanda Abba yazaba mun falillahil Hamdu”.
Gama shirinsu keda wuya, suka kama hanya cikin Falo suka shiga suna muzurai, Daddy suka gani zaune cikin manyan kaya gyaran murya yayi yace “Nasan kunsan dalilin kiran danayi muku koh?” Suka hada baki a tare sukace “Ah Ah”
Kallonsu yayi tacikin Glass yace “maganan aurene daman idan kun shirya inaso kowacce tafito da miji” dam gabansu yayi mugun fadi “Bisma kece babba kuma kece yakamata kiyi setting example akan kanninki dalili kuwa shine idan sukaga kin bada niyya toh yaxama dole suyi mubaya’a, ba burin mahaifinku bane kukai girman haka bakuyi aureba, Amma saboda Zamani shiyasa na bari kunemi ilimi Wanda za’ayi alfahari daku nan gaba Ku nake saurare”.
Ikram dake kusa dashi tace “A gaskiya daddy banida zabi amma duk Wanda kazab’a mun a matsayin miji zanyi Alfahari dashi”
“Alhamdulillah Ikram kinyi magana mai matukar muhimmanci kuma insha Allah bazan miki zaben tumun dareba, Ku kuma fa ya muke ciki koh kuma bakuda zabi?”
Rumaisa tace “Daddy inaso kadan karamun lokaci, saboda banida wani Wanda mukayi alkawarin aure dashi” daddy yace “kina nufin kice bakida tsayayye?”
Rumaisa ta sunkuyar dakai tace
“Eh daddy” numfasawa yayi yace “ke kumafa gadarkama?”
Bisma tace “Daddy Kamar yadda ruma tace nima hakanne amma nayi maka alkawari nan bada jimawa ba”.
“Duk naji kuma na Aminche don haka kutashi kutafi”
A tare suka mike suka rankaya sai daki nan suka dasa labarin Hamdan kowa tana faden yadda lamarinsu ya kasance.
Ilai haka bikin Laila da hamdan ya fasu saboda tace bazata iya auren mayaudari maciyi Amana ba, haka komai ya watse Laila ta kama wani reshen, Hamdan yaxama abun tausayi amma gaba daya baiyi ladaman abunda ya aikata ba.