DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Nuru yasamu aiki a United kingdom, a state din Kasar Wato Florida inda sukayi karatu an daukeshi a matsayin lecturer haka ya kwashi iyalansa sai Chan harda Labiba, ya kwalam an tsufa Ummi kam kwance take saboda ciwon sugar dake damunta, Mujeeba batasamu zuwa yi musu sallama ba amma dai sunyi waya sannan ta turawa iyayenta makudan kudi, Jood’a kuwa shanu yasiya dukda tsufa dayayi jiyake tamkar matashi gidan gona aka budemai achan yake wuni wataran har kwana…………….
Yara kowa yayi aure daga gidansu Bisma kowa saida yasa sunan bisma saboda kaunar da suke mata, Haka mutuwa ta dinga dauki daidai saida tadau Ummi kannan ta zagaya tadau jooda mahaifin Mujeeba, haka su Mujeeba aka rankaya sai Nigeria inda tabar yaran wajen labiba.
Mujeeba tayi kuka rashin mahaifinta saida kowa yakoma bata hakuri saboda yitake kamar ranta zai fita, idan ta kalli hoton Ummi saitaji duniyar tamata fadi.
Alhaji kuwa shi akayiwa mutuwa babu Ummi babu jood’a banda imani da tuni yafadi shima yabisu, saboda shakuwar dayayi da jood’a tayi yawa harta kaiga bayacin abinchi sai dashi, sunkulla alaka wacce duniya take alfahari dashi.

Haka aka gama zaman makoki su Mujeeba aka koma taso tafiya da ya k’walam amma babu hali tana cikin takaba, haka su ikram suka rik’e ya k’walam kamar Ummi tana fita takaba su yaya salim da babban wansu hadi da nabil suka sa aka daurawa ya k’walam aureda mahaifinsu, su Mujeeba labari kawai sukaji abunda ya dadada musu rai kenan zumunchi yakara karfi zuria sai bunk’asa takeyi, tako ina Alkhairai budi ta koh ina saboda sun gama da iyayensu lafya.
Mujeeba ce zaune a falo bayan shekara labiba ta haihu Nuru yasawa yarinya Bisma atafau tace bataso sunan matacciya Allah shi kyauta, haka Nuru ransa ya baci tuni ya karbe yar tasa yayi mata bisa yace ta wuce Nigeria saiya nemeta nikam nace mai hali baya chanza halinsa, Dan talaka bai iya samun wajeba Mujeeba tayi juyin duniya yabata yarta yace ina har abun yadawo kanta nikam HUMAIRAH nace ina dalili ina Dan mafari ai ki kyaleshi kawai,
Mujeeba ta hada da tata yar macen mai sunan Hajiya taci gaba da rainonsu haka rayuwa takasance mai dadi, haka Mujeeba tadinga haihuwa harta koma tsarin iyali, tafara kwalliya kamar wata budurwa abun sai Wanda yagani anan sai ince Allah yabamu rayuwa da zuria mai amfani.

 

Alhamdulillah……

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button