DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Bisma ce kwance akan doguwar kujera, mai gadi yashigo da hanzarinsa yace “Ana Sallama dake hajiya” a watse Bisma tace “kaje kace waye?” Bai Dade da fitaba sai gashi ya dawo “yace ince miki hamdan ne”
“What”!!!!!!
Lokacin ta mike tace “lallai Hamdan yace wani Abu meyake nufidani ne?”.
Cikin sauri ta fita tana isa gareshi ta wankamai mari tace “Wannan shine sannu da zuwa”.
[2/2, 8:21 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

9⃣

Rike kuncinsa yayi yace “You have evry ryt toh waz me slapp but believe me I will always love you till death do us a part, Bisma take dis as a mistake I don’t mean to hurt you, nasan nayi miki *rashin adalci na ILILEE* amma you have to forgive me dake kadai zan iya Rayuwa idan baki Bisma I will be no more”
“Heyyyyyh dakata rufemun baki, suda sarkin Zak’i waxaka cuta macuci toh kasani danade da dawowa daga rakiyarka don haka kwarya tabi kwarya”.

“Bisma duk abunda zakicemun wallahi bazanji haushiba, Nasan cewa har gobe kinasona kuma har gobe baki yarda alkawari ba, duk abunda yafaru kidauka kaddara ce”
“Meyasa kaddarar batazo da wuri ta hanani sonka ba saida tabari nayi nisa a sonka? Shine xatazo ta tarwatsa rayuwana nayi Dana Sanin barinka shiga zuciyana kasani Hamdan bana sonka bana kaunarka kaje wajen yar’uwata Ruma kila ita tanada sauran space dinka amma for me bakada shi”.

Da gudu ta shige gida, tabar Hamdan tsaye cikin kunar rai jingina nayi da bangon dake gefensa, yana hawayen takaici, yanzu inzai dosa Bayan yan’uwansa sun tsaneshi mahaifinsa yayi barin iska dashi, ji yayi an dafashi juyowan da zaiyi mahaifin Bisma yagani tsaye yace “yaro share hawayenka koda wasa karka sake ka zubda hawayenka gaban mace don haka shike kawo raini”.

Hannunsa ya rike suka shiga cikin falon baki yace “gayamun damuwarka”) nikuma inyi maka maganinta” nan hamdan ya fede masa bindi har wutsiya, bai boye masa komaiba, mahaifin Bisma yace “kayi kuskure babba amma haryau har gobe kanada damar taka rawa acikin birnin zuciyoyinsu, nabaka izini kaje wajen Ruma kila Allah yasa ka dace”.

Godiya yayi sosai ya mike bai zarce koh inba, sai gida cikin sasansa yashiga ya kulle, abunka da uwa takasa jurewa halinda danta yake ciki, ta dauko abinci tana tafe tana waige a hankali ta kwankwasa kofar tace “Hamdan ka bude nice” jin muryan uwarsa yayi saurin tashi ya bude tace “Gashi maza kaci nizan koma”.
[2/2, 8:40 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

????

Ciki yakoma yana tunanin yadda zai tukari Rumaisa da wannan Al’amari shin idan taki amincewa bukatarsa ina zaisa kanshi?
Ni Humairah nace kaika sani Wanda yace yaudara yasa gaba kuma ai karshensa baxai kyau ba,
Koh abincin yakasa ci washe gari ranan litinin Bisma ta saba Jakarta sai wajen aiki da shiganta tafara arba da marasa lafya tuni taji wani tsusayinsu ta kamata, saida tayi reporting kannan akayi mata jagora zuwa office dinta inda zata dinga Attending patients.

Zamanta keda wuya aka shigo da card din mutane haka tadinga Attending mutane, kowa sai yaba mata akeyi saboda hanzarinta wajen iya aiki, gashi turancinta daban yake hakan yanuna cewa baa gida tayi karatuba.

Hamdan ne tsaye jikin Motarsa kirar BMW 4x latest version, ya juya baya inda tuni akayi mishi iso da Ruma, da zuwanta ta gane kowaye tace “Sannu tabbatacce Mara mutunci meya kawoka cikin gidanmu in short harabar gidanmu? You must be dreaming”
Juyowa yayi fuskarsa babu alaman fara’a yace “idan mafarkine da baxanso in farkaba indai a harabar gidanku ne na gwam mace inta bacci har sai randa mafarkina yazama gaskiya, Ruma kidauka abunda yafaru tsakaninmu mukaddari ne daga Allah”.

“Allah sarki ustaz toh kasani bakada waje acikin zuciyana don haka get out of this house kafin inyi maka ihun kwarto”
Hamdan yacire glass din dake idonsa yace “Go ahead kice ni kwarto ne Nasan iya kaci inyi gidan yarine koh? Toh ai mak’aranta ce kuma duk Wanda yashiga dole ya koyi darasi bakin ciki daya zanyi a gidan yari babu darasi akan SO”.

Rumaisa kallonsa take “Wato ya maidani wata bigi bagiro koh? Toh zanyi maganinshi,
Tace “Kafin inyi irga uku kabar gidannan idan ba hakaba ba gidan yari ba duniyar zaka bari gaba daya”
Maida glass dinshi yayi yace “Zan tafi nagode da kulawarki gareni amma kisani Allah da kansa yace yanason mai yafiya”.
Cikin Motarsa yashiga saida tayi gunji kannan yabar haraban gidan.
[2/2, 11:28 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

1⃣1⃣
_*This page is dedicated to you Abdul-Aziz ILILEE Isma’il???? Tnx for the Love and Care????????RASHIN ADALCI yana bada magana keep it up????????.*_

 

Bisma ce tafe cikin motarta daidai roundabout din lahlah motor pack, sukayi kacibis da Nuru cikin Motarsa horn yayi mata daganan yadinga binta har saida suka shiga cikin unguwarsu, packing tayi shima yayi packing yafito yace “Beauty yakike kice harkin fara zuwa aikin waw bakiga yadda kikayi kyau acikin kayanki na likita ba, tabbas kin chanchanci yabo dole inyi miki kyauta ta musamman wacce ba kowa yake iya yiwa wata ya mace irinsa ba”, kallonsa kawai Bisma takeyi waishin mafarki takeyi ko kuwa ido biyu ne Nuru ne kobashi bane, BEAUTY???? Ta tambayi kanta cikeda mamaki Tabbas dakwai magana a bakin Nuru kuma yaxama dole inbashi dama don ya furta abunda ke bakinsa.

Nuru ne ya katse shurun da cewa “Inaso ki rufe idanunki, saboda inbaki gift din daya dace da kwararrar likita”, ilai batareda ta wahalar da Shari’a ba ta rufe, wani katon kwaline nidai nakasa gane koh meye aciki amma, nifa Feedoh mukace sai munga abunda yake ciki laidar gaba daya zanen love ne ajiki,
Yace “Gashi ya mika mata lokaci guda yace tabbas inaso alokacin dakika bude koh xaki bude kisa aranki cewa life most go on, the world most know dat a lion is a king, sannan karki bude idanunki har saina bar haraban gidannan”.

Haka akayi harya tada mota yafita sannan Bisma ta bude idanunta “wat a surprise, oh my God Nuru wat did I do to him to deserve such a huge amount of gift” tsintar kanta kawai tayi tana murna da kyar taja kayan cikin gida tana haki Ummi tace “Daga ina? Wannan kaya haka kasuwa kikaje ne?” Ummi ta tambaya tareda tsare bisma da ido.

“Ummi NURU ne ya kawomun su nima dai cewa yayi in rufe ido kuma kar in bude har saiya tafi, Ummi bansan meye nufin Nuru ba?”
Ikram dake tsaye tace “sonki yakeyi saboda naga alaman hakan a cikin kwayar idanunsa, yana cikeda shaukin ki don haka just kiyi accepting dinsa saboda daganinshi zaiyi jarumta a fagen nuna miki irin tasa salon soyayyan”.

Murmushi bisma tayi ta ajiye Wasu takaddu, da jakar dake hannunta ta fara bude kwalin wani kamshine ya doki hancinta nifa Feedoh kuwa ai har saida muka dunguri kwalin, saboda zumudi kati ne Wanda yake daukeda hoton zuciya, cikin zumudi Bisma ta kwashe su gefe wasu turaruka ne kayan sawa gaba daya zanen love ne ajiki lokaci guda taji wani kunya ya ziyar ceta da gudu ta haye saman bene sai Dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button