DASHEN ZUCIYAHAUSA NOVEL

DASHEN ZUCIYA

Fadawa tayi kan gado tana imagining yadda rayuwanta zata kasance da Nuru Wanda ayau ya nuna mata SO, tabbas wani hanin ga Allah Baiwa ne, Ashe Allah zai musanyamun da mafificin Alkhairi, Allah nagode maka.
[2/2, 3:33 PM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

1⃣2⃣
_*this page goes to you ANEESA A RIMI,???? thanks for the love and care may Allah continue to give you strength Amin????????*_

 

 

Ummi kawai dariya abun yabata tace, “maza ki k’washe kayannan kikai mata Daki, ita tasan yadda zatayi dasu wannan nakune yan’mata” dariya ikram tayi tadinga kwashe kayan tana kaiwa daki, Bisma tace “ikram am so lucky to have Nuru as my second love, he is damn kind oh ya Allah thanx be to you” ikram tace “Bisma haka daman haka Allah yake tsara abubuwansa batareda yayi sha’awara da mutum ba, Allah kadai yasan dalilin dayasa kuka rabuda Hamdan, Allah yasa yazaman miki garkuwa a rayuwanki”
“Amin” Bisma tace haka ta dauki turaukan ta raba ma kanninta, Ummi kuwa tace bataso nasune na yara.

Bayan Kwana biyu dazuwan, Nuru yakara dawowa amma wannan karan har office dinta ta isketa, tana ganinsa taji wani kunyansa tace “you are welcome have a sit”, zama yayi yana kallonta yace
“Nasan zakiyi matuk’ar mamak’in zuwana amma wannan karya daga miki hankali, nazo miki da proposal ne, dafatan zakiyi accepting dina hannu biyu, sorry fah nasan kina kan aikin ki ne na tsayar dake amma nasan bazanci lokaci mai yawa ba,” Biro yaciro daga aljihunsa yace
“miki hannunki”.

Babu musu ta mika masa ya rubuta mata kalman I LOVE YOU da manyan baki, saboda tsabar dadi Bisma kaman kanta zai fashe, itama biron ta ta dauko tace “miko hannunka amma saidai kayi hakuri ni bahaguwa ce” dariya yayi yace “shiyasa naga likitar tawa guruwace” itama I LOVE YOU ta rubutamai tana gamawa yace
“nizan tafi banaso naci miki lokaci, kinsan turawa da girmama lokaci”.

Dariya bisma tayi tace Allah ya tsareka ya kareka, “Amin yace” a ranan da kyar bisma ta iya kammala aikinta, misalin karfe shida ta rufe office saboda abokin aikinta yazo.
Waje ya fita tashiga cikin motarta tayi mata key amma taki tashi, fitowa tayi tana duba engine din motar da kyar ta tashi da isanta gida tayi wanka tayi sallah, tashiga ciki yan’uwa aka gaisa Bisma tace “Ah gaskiya umma aikin taimako da wuya yake fatana Allah yasa kada in gaxa wajen bada gudun mawata,” Amin suka amsa dashi.

Yaya salim ne zaune yace “a gaskiya bisma kinyi dacen masoyi Wato Nuru mutum ne Wanda baidau duniya abakin komai ba, baki gazu daya shigo gaida Ummi ba yadda kikasan yasanni”
[2/3, 7:13 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

1⃣3⃣
_*This page goes to UMMI AISHA thank for the humble love and care, Am happy for you for the completion of your Novel RUWAN KASHE GOBARA????MAY WE SEE THE NEXT Lafya????????*_.

 

 

Dariya Bisma tayi tace “Haka yake koh lokacin muna makaranta yakan bata lokacinsa don ganin ya farantamun rai ta Dan kaga mun rabu toh Hamdan ne yaxo saboda basa ga maciji dashi, don Hamdan yakance Nuru snatching zaiyi mishi” kowa acikin gidan yabon Nuru yakeyi ba’ayi wata gudaba Nuru ya sanarda Bisma cewa za’a turo gidansu, ranar murna a wajen Bisma dama sauran yan’uwanta ba’a magana, daddy kuwa yakasa zaune yakasa tsaye, saboda murnan tarban surukai.

A Daren ranan daddy ya tarasu, acikin katon falon su, yace “Dalilin dayasa na kiraku shine, Kamar yadda ikram tace batada Zabi, toh nayimata Zabi Wanda zatayi Alfahari dashi, na zaba mata KAUSAR a matsayin miji kuma shima ya aminche dake ikram a matsayin wata bangare nashi, Kamar yadda kuka sani Kausar dandan abokina ne kuma Aminina”

Ikram tunda taji ance kausar taji wani dadii acikin ranta daman ta Dade tanason Koda gaisuwa ce ta hadasu amma a yadda ta lura bai damuda magana ba, hasalima koh aboki bayidashi,
Daddy yace “Ina fatan kin aminche ikram?” Saboda kunya tashi tayi da gudu tashiga cikin Daki, Rumaisa dake zaune tarasa abun cewa itama kanta daddy ya juyo yace “ke kuma Ruma tunda kin kasa fitowa da miji nazaba miki miji”.

Yana faden haka ya mike yafice, Ruma sarairai tayi tana tunani shin waye daddy yaza bamun a matsayin miji? Kanta take tambaya amma takasa samum amsa, Ummi ce ta dafata “Karkiji komai Ruma duk Wanda yazaba miki ki karba kiyi biyayya koba komai yaci arziki a matsayinsa na wan ubanku”.

Ruma mikewa tayi tace “Umma naji zanyi biyayya Allah ya kara muku Nisan kwana”
“Amin”
Bisma dake gefe tana duba wani katon littafi idanunta sanye da medical glass, ta juyo tace “Ninasan Wanda Daddy ya zaba miki kuma zakice na gayamiki” Ummi dake gefe tace “ke kin shiga uku ina ruwanki so kikeyi kisata cikin tunani toh inkin fasa”.

“Haba Ummi wasa fa nake mata Dan Allah kiyi hakuri wallahi so nake in rabu Daku lafya saboda nima gaba abani girmana a matsayin uwa, pls am sorry”
Ummi dariya tayi tace “Amma keko akwaiki da abun ban dariya na hakura aini bakuyimun komaiba kuma Allah zaishi muku Albarka”

Washe gari yak’asance ranar Asabar tunda sanyin safiya suka tashi, sunata aikin tarban bak’i Daddy kuwa tuni ya sanarda kawunnesa na kauye tuni suka hallaro,
Ummi ta kware wajen yin kayan snacks, inda Bisma ta kware wajen iya sanwa, ikram kuwa wajen hada Lemuka nan tafi kwarewa, Ruma kuwa indai roasting ne da grilling toh nan tafi kawarewa, kuma duk sun koyi hakanne wajen Ummi saboda tun suna yara take shiga kitchen dasu shiyasa batada yar aiki ko guda daya, saboda bata yarda da masu aikiba saboda tsaro badan tsoro ba.
[2/5, 7:25 AM] Melody????????‍♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*

_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????

 

1⃣4⃣

 

Alokacin da suka kammala aikine, *NURU* ya kira Bisma “My Love mun kusa isowa nanda minti goma go slow ne ya tsaidamu” dariya tadanyi mai kwantar da zuciya tace “Haba my destiny you don’t have to worried we are all here for you guest” ikram ce zaune akan dressing mirror tana sheka kwalliya, itama taji wayarta tana ruri juyowa tayi taga wata bakuwar lamba jiki a sanyaye ta dauka tace “Hello” cikin sexy voice dinta, daga dayan bangaren aka amsa da “Sallama yakamata kiyi ba hello ba saikace ba yahudiya? Pls take note nasan zakiyi mamaki ganin bakuwar lamba toh inamai farincikin sanar dake cewa *KAUSAR* ne inaso in sanar dake cewa mun kusa karasowa nanda mintoci kadan ina fatan kina cikin farinciki dukda yaune zamu fara ganin juna”
She’s out of words tace “Allah ya kawoku lafya” ta kashe wayan saida tadau mintoci biyar tana kallon wayarta tana murmushi saboda sonda takewa Kausar dinta.

Allah sarki Duk Wanda yaga Ruma abun bazai bashi sha’awa ba, saboda wani takurewa datayi saboda har yanzu tarasa waye wannan Wanda aka zaba mata a matsayin abokin rayuwanta? Kallon Bisma tayi tace “Bisma duk naga kuna cikin farinciki amma narasa meyasa Nina kasa samun farinciki, babu komai cikin raina sai tsantsar Tashin hankali, bansan dalilin dayasa tunda na wayi gari yau bana cikin walwala”

Bisma tace “Ruma kenan Zabin Allah shine zabi ba zabin daddy koh mutum ba, karki sake kisawa ranki damuwa saboda wannan karamin abun, ki tashi maza kiyi wanka ki shirya cikin Expensive Cloth Wanda zaiyi suiting dinki, toh kowaye wallahi saiya yaba miki duk kasaitarsa haka duk mulkinsa” Ruma ta tabe baki tace “Nagode kwarai barina tashi, mikewa tayi zata shiga bandaki kenan wayarta tafara ruri juyowa tayi kaman bazata daukaba ikram ce ta taimaka ta mika mata wayar amsawa tayi takasa cewa komai, cikin hocky voice yace “My joy nasan kila kinata sa idon ganin call dina sorry for calling late kinsan you’re the apple of my Eyes you’re my nose without you baby I can’t breathe for once” batasan Lokacin data fara murmushi ba dukda bata gane da Wanda take waya ba cikin muryan shagwaba tace “you don’t have to worry your self sai kunzo” karaf ta kashe wayar……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button