DASHEN ZUCIYA

Basu Dade ba saigasu cikin motoci nagani na fade, zan iya cewa iyayen NURU sune a baya wajen Arziki amma kwata kwata Bisma ba Arzik’insu takeso ba Annurin zuciyanta kawai take burin mallaka,
Cikin falo aka shiga dasu Anyi musu tarban Arziki daga bisani suka fara abunda ya tarasu, anan aka tsaida watan aure wata uku, dukda halinda ake ciki na rashi Daddy yaso asa Shekara amma suka nuna su Sam basu yardaba, matan sukeso ba kayan kyalekyale na duniya ba.
Haka yan’uwa suka kama hanyan komawa gidajensu, akabar Samarin da yan matansu donsu tattauna a tsak’aninsu, daga Bisma Har Ikram suna cikin walwala dajin dadii, Ranshin ganin ruma yasa Hamdan shiga wani tension, gashi yana masifar jin kunyan NURU dama BISMA.
Ummi ce ta bude taga ta hangi Hamdan tsaye yana kada mukulli, ranta yayi kololuwar tashi, tace “Wato Ruma bata fita wajen Hamdan ba yau nida itane, dakinsu ta zarce tana kwala mata kira, Ruma! Ruma!! Ruma!!!
[2/5, 8:04 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
1⃣5⃣
Kiranda Ummi take mata ne yasata dawowa daga tunanin data shiga Ummi ta kutsa Dakin ta wankama Rumaisa mari tace “Wato kega isassa shafaffa damai, ubanwa kika ajiye dakika wulakanta bawan Allah a waje koh bake yake jiraba ?”
Rumaisa cikin muryan kuka tace “Ummi bansan me kike fadeba,”
“Toh maza kifita Ga Hamdan chan yana jiranki saura kiyi mai rashin kunya tabbas zaki hadu da fushina”…
Tunda Ummi take bata taba daukan hannu tasa akansu Ruma da ikram ba saboda marayu ne mahaifinsu ya rasu tun suna kanana Ummi itace tazama Kamar mahaifiyarsu.
Ruma tashiga tension tarasa kuka zatayi mezatayi oho, gyale ta dauka ta fita tana zuwa ta Tsaya tace “Ina saurarenka” juyowa yayi yana murmushi yace “Koda yaushe kara kyau kikeyi, sannan idan kina tsiwa gani nake Kamar in saceki, saurare kuma ai kingama tunda ga Hamdan agabanki mai shirin zama abokin rayuwanki”
“Dakata ban wannan na tambayeka ba cewa nayi ina saurarenka shikenan sai ka hau bani Wasu tsoki burutsu? Look am not in the mood of talking pls you can take your leave” ta nunamai hanyan fita.
Hamdan yace “koda kince kar in sake zuwa gidannan Rumaisa bazan kara zuwaba koda ranan daurin aurene baizama dole inzo ba kinga Lokacin da aka kawoki dakina kinga kinzama mallakina” cizon yatsa Ruma takeyi tace azuciyanta Wato duk abunda zanyi mai baxaiji haushiba toh ajuri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe.
Mota ya bude yaciro wasu ledoji yace “gashi wannan shine tukwici na, na farincikin ansamun rana da abar kaunata Ruma” kallonsa ta tsaya yi “lallai nema hamdan ya rainani toh zanyi maganinka mik’a mata yayi yace “Gashi kidauka a matsayin wannan ce kyauta ta farko sannan ina rokonki da karki maida hannun kyauta baya”.
Mtwwwww wani dogon tsaki Ruma taja tace “ka maida abunka banida bukata ai ban rokaba koh nacema ina yunwansu ne?”
Dukda abunda hamdan ya tsana shine tsaki amma saiya nuna bakomai, yace toh shikenan ngd kwarai da kika bani lokacinki ki gaida Ummi, da sauri tabar wajen shima yayi kaman ya shiga mota fitowa yayi ya samu mai gadi ya mika mishi kayan yace kashiga dashi ciki kacewa Ummi injini abawa Ruma babu yawa.
Haka mai gadi yashiga yayi yadda akace masa, Ummi ranta yakara baci tacema ma mai gadi “kin amsa tayi?
Shiko yace “Eh hajiya yanata magiya amma saita gayamai magana”.
Ummi tace “Nagode yi tafiyarka, kayan ta kwasa tashiga cikin Dakin ta watsa mata tace “Amma Ruma ke munafuka ce Ashe dakwai ranan da zamuyi miki Abu kice bamu iyaba? Toh kisani koh kinaso koh bakyaso aure da hamdan ba fashi sannan idan har kika kasa yimai biyayya wallahi babu yafiya tsakanin mu dake inhar kuma kinada wani zabin kiyi magana”.
Fuuuu Ummi ta fice Kamar zata tashi sama, tabar Ruma zaune tana kukan bakin ciki saboda bata taba tunanin Hamdan yazama mijinta ba,
Ranan da akasa kowacce zataje gaida dangi Dukkansu haka sukaci kwalliya Kamar ranan aurensu, kowacce farincikinta ya dauketa, sukayi dangi Ruma dai saida tasamu yan rakiya guda biyu Abeeda da Aneesa,
Haka sukabar shinkafi zuwa garin Gusau, Abeeda da Aneesa suketa magana amma ruma koh kwakkwaran motsi batayi.
Bayan filin polo dake cikin Zamfara suka isa wani gidane tank’ameme mai suna ihunka banza, tuni Aneesa tace “Inane nan?”
Hamdan yace “Yankaku zanyi inyi kudi daku Nasan kan wata acikinku zaiyi tsada” kutsakai yakeyi har packing loge ya tsaya yan gidansu ne suka fito suna dariya suna ma Rumaisa maraba, tuni yan gulma akafara Anya ba inyamura yaya ya Jajibo mana ba?
[2/6, 7:52 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
1⃣6⃣
Saboda tsabar farin rumaisa duk Wanda yaganta zaiyi tunanin inya murace, ganin yadda kowa yake kallonsu ne yasa kowacce tashiga *frowning mood activated* Gashi sunci uban kwalliya sannan dukkansu buba mai dogon hannu suka saka shigardai Tasu kaman bata hausawa ba kowadai yasan mafi akasari yarabawa ke irin shigar koh inyamurai.
Shiko Hamdan farincikine fal cikin ransa, “Tabbas na iya zabe nasan kowa zaiyayi maganan Ruma” kanwarsa ce Nabilah tace “kushigo mana saikace wasu Baki”,
Tafe suke zasu shiga Abeeda taji wata na cewa “yasin Kamar inyamurai tunda har yanzu sun kasa magana sai wani hada rai da sukeyi abun gwanin kyama” Aneesa data kasa hakuri tace “Abeeda nikam haushin wasu halittu nakeji saboda gaba daya idan kafisu kafisu saboda me nace haka bazasu taba taranka sugaya maka magana ba sai a bayan keyanka”
Ai gaba daya sai sukayi sarere, wani palo aka kaisu yasha kayan Ado amma Dayake sun saba ganin irinshi sai bai basu sha’awa ba.
Anyi musu tarba na mtunci, mahaifiyar Hamdan ce da sauran abokan zamanta, ganinsu Rumaisa yasa duka fara yar kallon kallo, yake sukayi ganin su Abeeda na kallonsu sukace “Maraba dayan shinkafi, shinkafi garin manya garin kyawawa, maraba maraba lale marhabin, zama sukayi har kasa su Ruma suka gaidasu cikin ladabi amma kwata kwata mahaifiyar Hamdan bata gamsu cewa su Ruma bahaushiya bace kuma yar Asalin garin Shinkafi ba.
Kowa yan’uwa saida sukazo ganinsu kuma ba komai bane su nabila ne suka feshesu cewa suzo suga matar da Hamdan zai aura, mahaifin shi kansa saida yashiga ko kwanto, sudai su Abeeda da Aneesa saida sukaci sukasha itakoh ruma duk a takure tace, basu wani jimaba Ruma tace ma Hamdan “Mudai zamu tafi mun gaji da kallon yan kauyen da danginka suke mana sai kace yau suka fara ganin mutane”
Tashi sukayi sukace a tare “Zamu wuce saboda garin namu dakwai Dan tabi”
Tuni mahaifiyar Hamdan ta ta tashi ta hado musu sha Tara na Arziki sannan suka kama hanyan komawa shinkafi.
Haka suma ikram da bisma tafiyar Tasu ta kasance sun tsinci Kansu cikin farinciki dajin dadii saboda samum abunda zuciyoyinsu ke muradi, bayan sati
gudane wata gagarumar kura ta tashi acikin family dinsu Hamdan nacewa su Sam basu yarda hamdan ya auri Rumaisa ba saboda sunce irin dadaddun inyamuran nanne masu zuwa garin Wasu suyi kaka gida harsu hayayyafa su musulunta, Hamdan yashiga tension saida ya kusa haukace musu sannan sukayi lakwas.