DASHEN ZUCIYA

“Gaskiya inason Ruma Abba, saboda kawai kungasu farare shikenan saikuce musu inyamurai, su kadai aka raina ai duk farinsu basu kai yan gidansu Laila Ibrahim ba sudama suke Kamar larabawa , haka nakeso abata koda bayarabiyace zan aura tundadai musulmace yar’uwata”
Abba dake zaune yace “dakata Hamdan kada so ya rudeka ka kasa tantance baki da fari, har Yanzu bakasan komaiba maza ka bacemun daga gani sainayi bincike”
[2/6, 3:13 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
1⃣7⃣
Haka Hamdan ya fita, Dakin mahaifiyarsa yashiga yayi Sallama ya zauna Abunka da ‘da’ da mahaifiya ta matso kusadashi tace “Hamdan kayi hakuri komai mai wucewa ne, nikaina na yarda Asalin zamfarawa ne saboda naga akaman sunsha zamfaranci sun koshi, amma tunda yace saiyayi bincike kabarshi a haka kaci gaba da Adu’a kana Neman zabi,” Hamdan yace “Innanmu bakisan daya Ruma ta Aminche dani ba har yanzu ba wani matsuguni nasamu acikin zuciyanta ba taji wannan abun nasan confirm cewa zatayi tafasa gaskiya Nidai abar maganar nan gaskiya inhar bahaka ba xan iya yin komai Wallahi matukar wannan maganar takoma kunnen iyayen Ruma sukace anfasa”.
Tashi yayi yashiga cikin Daki, Ruma yakira saida yakira sau goma kannan ta dauka, yace “My love dafatan kun huta gajiya?” Rumaisa tace “Bansani ba toh inaso kasani bani bakai tunda har yan’uwanka suka kiramu da inya murai toh ka sanar dasu nima bazan taba hada jini dakuba, jinin munana kawai Kaidinma Allah yasa ba’a gidan marayu suka tsintoka ba mtwww” taja tsaki ta kashe wayar gaba daya.
Taci gaba dacewa “banda sun raina mana wayo daga sunganmu farare toh banda Ai dadinta bamu mukayi kanmu ba, tab farare sun bani Yanzu da irin wannan sharin za’a dinga aibatamu, ni humairah nace Allah yasoni wankan tarwad’a ceni????.
Hamdan tuni yaji wani jiri yana dibansa salati kawai yakeyi cikin karfin hali ya fita yana dafa bango harya isa Dakin mahafiyarshi yana shiga ya fadi yana rikeda Kokon zuciyansa, ihu nabila tayi tana kiran taimako asibiti aka wuce dashi, Ana zuwa aka kira likita, Bisma ce tsaye tace kufita kubamu waje tukunnan, itada nurses kawai aka bari abun mamaki Hamdan tagani lokaci guda taji wani mugun haushinsa inama ya mutu kowa ya wuta da wannan guban, tawani bangare saitaji tausayinsa Dana kanwar ta Ruma bazataso ta rasa shiba saboda shi aka zaba mata a matsayin miji.
A iya gwaje gwajenta ta gano cewa yana dauke da ciwon zuciya sanadiyyan natsanancin damuwa daya shiga, drip aka sa mishi sannan ta fita tace “zai samu sauki amma wacece uwarshi tabiyoni,” cikin rashin tarbiya Bisma ta fadi Nabila tace “Wannan likitar yar rainin wayoce gata yar k’arama Allah yasoki asibiti muke da saina lallasaki yasin” mtwwww taja tsaki ta tabe baki.
Suna shiga cikin Office Bisma ta zauna ta kalli mahaifiyar Hamdan tace “Saikinyi hakuri kinsan dayake farar fatace inyamurace ni ba Hausa na fiye ganewa ba” kawai taci gaba da cewa “A gaskiya danki yana cikin matsanancin hali kuma duk ta sanadiyyan damuwa a Yanzu haka yana dauke da cutar damuwa Wato (hypertension) inji turawa idan har ba’a samu mafitaba toh sai anyi masa *DASHEN ZUCIYA*”
Zare ido mahaifiyarta Hamdan tayi tace “likita menene abunyi yanzu?”
Tace “Abunyi shine idan ya farka saiku tambayeshi damuwarsa idanya fadi saikuyi mishi magani damuwarsa don muna bamuda maganin rage damuwa saidai idan har Zuciyarsa ta kasa toh shine nace zamuyi mishi *DASHEN ZUCIYA*
Bisma mikewa tayi tace “Muna iya fita dakwai magunguna dazaran ya Tashi kubashi Donni gida nayi tun daga shinkafi nake zuwa nan”.
Fita sukayi Bisma tace “Kadan ga Gani tunda kuka hada jininmu da inyamurai mun dinga kenan” mtwwww taja tsaki.
[2/6, 7:36 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
1⃣8⃣
*This page goes to you Ladies name seeks AYUSHA ILIYASU, AYSHA SAYADI, AYUSHA MUHAMMAD, AYSHA GANA, AEESH CHUCHU, AYSHA WAKILI???????? love you all the A’s Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya yasa kufi haka a Rayuwa.*
Komawan bisma gida keda wuya, tasamu umminsu tace “Ummi kun kasa gane koh waye Hamdan Wallahi Sam ba chanchanci abashi ruma ba Allah kuwa Ummi”
Ummi tace “dallah yimun shiru kotanaso kobataso aure ba fashi, saidai ta mutu irinkune masu zuga kanninku idan suna gidan mijinsu toh Wallahi kar inji kar ingani, idan tanaji zabin da mukayi mata baiyiba toh saita kawo nata zabin amma tasani duk abunda yabiyo baya ita tasani”.
Tashi Ummi tayi tabar Bisma Zaune ita kadai, itama tashi tayi tashiga dakinsu, ta taradda Ruma kwance tana tunani, dafata Bisma tayi tace “Ruma albishirinki” Ruma tace “Goro”
“Fari koh ja?” Ruma takara cewa “Fari kal”
“Toh hamdan yana asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, ciwon zuciya”.
Zare ido Ruma tayi tace “Kaddai maganar Dana fadane yasahi ciwo? Take tambayan kanta, karajin Daddy sukaji daga kasan bene yana kwalawa Ruma kira, gabanta ya yanke yafadi da sauri tafita jikinta babu inda baya kyarma, tana isa ya kwasa mata mari yakara kwasa mata mari yace “Wato ke ruma kinaso kice banina haifeki ba? Kinaso ki gayawa duniya cewa niba ubanki bane rikonki nakeyi?
Amma kunyi kuskure bantaba muzantaki ba acikin gidannan tun kuna kanana kawo yanzu amma shine ni kikeso kizama silar batamun rai da suna? Toh Ruma baki isaba kinyi kadan Wallahi ko Fatima bata isa inkafa doka ta taka ba ita datake mahaifiyarki”.
Kallonta kawai yakeyi cikeda baccin rai tuni ya fashe da kuka saboda Ruma da ikram amana suke a wajenshi ya zaiyi da rayuwansa gashi ya muzguna ma Ruma, Nidai banga laifinshi ba itadai ruma tanaso ta bijirewa umurnin wan abuntane kawai ba wani abuba, kuma batada Wanda zata tsayar idan tace batason Hamdan, kodai yaya Salim takeso? Muje zuwa mahaukaci yahau kura.
Rumaisa ta durkusa har kasa tace “Daddy na hakura kuma insha Allah bazan sake bata maka raiba sannan abunda nakeso a zuciyana daddy nabarwa zuciyana, fatana daddy kashi mana albarka” tuni wani imani yazowa daddy yace “Kije na hakura amma kisani inyamura da sukace miki kidauka kuskure ne sannan ina umurtanki daki je cikin garin Gusau gobe idan bisma zata aiki don naji labarin achan aka kwantar dashi”.
“Toh” tace ba musu tundaga ranan ruma tasawa ranta Salama, tana rokon Allah daya sanya mata natsuwa da Hamdan, washe gari suka shirya tsaf direba yadauki mota, Bisma tanajan tata, tafe suke Bisma take labartama Ruma yadda sukayi da iyayen Hamdan da irin wulakancin data musu, da isarsu asibiti suka kutsa kai duk inda Bisma ta gifta gaidata akeyi saboda halin girman data nuna musu.
[2/6, 8:09 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
1⃣9⃣
_*AUTAR HAJIYA* ban manta dakeba da kina raina *UMMI ADNAN* kema kin chanchanci in gaidaki, Ina kuma *RASHKARDAM* kema ta kwarai ce *MJAY* kema aminiyar arzikice, ina kuga ganomun *MISS XOXO* ina kaunarki my heart beat for you, Ina *MAMAM USSEEY* banida abuncewa sai godiya, Allah yabar zumunchi Amin????_.