DASHEN ZUCIYA

Office Bisma tafara shiga, wayar data fara amsawa ta mai sanyinta ne, bayan sun gaisane tayiwa su Rumaisa jagora zuwa Dakin da aka kwantar da Hamdan, muryar Rumaisa kawai yaji ya bude ido lokaci guda yaji sonta yana kara shigarshi, Nabilah suka Gani ta amsa a yatsine Bisma tace “Ina Babar taku yasha magani kuwa?”
Nabilah tace “Baxan iya saniba saidai kijira zuwa anjima taje gida ta dawo”.
Bisma tace “Kinsan cewa bacin banso inci haram koh kallon dakinnan baxanyiba, saboda your are not my type kingane, so ga kannina nan inajin kingane Wannan ta nuna ruma tace itacedai wacce kuka danganta da inyamura kuma yaxama wajibi Ku hada zuri’a damu, kallonsu Ruma tayi tace Ku zauna kujirata kila ta dawo yanzu”.
Nabilah irin yarannan ne marasa kunya, kuma babu Wanda ya isa yace mata bari tabari saboda taurinkai irin nata, waje ta tashi tafita tabar Ikram da Ruma acikin dakin shidai Hamdan koda kallon Rumaisa aka barshi ya warke, saboda jiyake Kamar ya rungumeta, ganin irin kallon da Hamdan yakeyi wa Rumaisa ne yasa ikram tafita batareda Ruma ta saniba, ganin ikram tafitane Hamdan yayi kokarin tashi amma kirjinsa ya sarkeshi yarasa, me yake masa dadi lokaci guda yafara kiran Ruma.
Juyowa tayi bataga kowa ba, tashi tayi ta matsa kusa dashi, tana mishi sannu tace “Ka k’oma ka kwanta basai ka tashiba” Hamdan yace cikin muryan ciwo yace “Rumaisa kece annurin zuciyana kice kinasona ko sau dayane kozan samu saukin abunda yake damuna Rumaisa kece silar ciwo na, Dakin ce Wallahi zan warke” kallonta yake cikin ido gashi ya rike mata hannu kauda kanta tayi yace “Ruma juyo ki kalleni kice kina sona in warke daga wannan cutar”
har hajiyarsu Hamdan tashigo basu saniba jira kawai take Rumaisa tace tanason danta amma Ruma taki magana.
[2/9, 3:43 PM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
2⃣0⃣
Hamdan dake kwance riris yace “Pls say something pls my own” kallonsa tayi tace “I love you dearly I quest cewa zaka samu sauki yanzu?”
Kallonta yakeyi cikin karfin hali ya mike da karfinsa yace “Kin yarda da cewa ciwon sonki ne ya haifarmun da ciwon zuciya?”
Ruma ta gyada kai alamun eh ta yarda,
Hajiyarsu Hamdan tayi Sallama lokaci guda Rumaisa taji wani irin kunya dukta lullubeta ta sinna kai cikin gyale yace “Ina kwana ya mai jiki?” a takaice Hajiya ta kalli ruma daga sana har kasa tace gaskiya Hamdan zaku haifi yara farare Ruma akwai fari Kamar tsada.
Hajiya tace “Da sauki” Ruma tace “tareda direba muke yanzu zamu tafi” hajiya tace “An gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi” Amin Rumaisa tace.
Suna fita sukayi wa Bisma Sallama suka wuce Shinkafi,
Kwanan Hamdan uku a asibiti aka sallameshi Rayuwa ta kasance mai dadi shida Rumaisa haka soyayyar yam mata ke bani sha’awa musamman ranan da samarin suke tsarawa don zuwa su sada zumunchin soyayya, iyayensu sai murna suke dafatan Allah yasa farincikin su ya daure har yaumuttanadi.
*BAYAN WATA BIYU DA SATI DAYA*
Ka mai yawan rai biki ya matso ya karato yan’ uwa dangi na nesa Dana kusa sunata lisafin ranar wannan gagarumin aure, acikin haka ne Rumaisa ta kamu da wani mugun ciwo Wanda kuraje ke fito mata a fata anrasa wane irin kurajene lokaci guda tazama abun kyama, dukda ba wari takeba amma abun ba kyan gani, Nan mahaifinsu ya tuna da wani ciwo datakeyi tun tana karama ina tunanin shine ya dawo yanzu kuma babu inda za’a iya samun maganin abun sai a kaiyen Mada dake cikin jahar zamfara, zamanta achan shine kawai maganin wannan ciwon nata, ran Kowa ba dadii ciki harda na Hamdan gaba daya yaji ya karason Rumaisa, kallonta yakeyi yace “Rumaisa zan soki har karshen numfashina, indai acan garin mada zaki samu sauki zanbiki duk inda zaki” kuka kawai Rumaisa takeyi tace “My Own zuciyana Takasa samun sukuni ganin irin ciwon danakeyi nasan yan’uwanka bazasu soni ba”
“Kidaina kuka Ruma digan hawayenki Kamar digon dalmane acikin zuciyana kisa aranki ni nakine kuma aure ba fashi dani dake sai an buga mana taken so”.
A haka mahaifin Su Ruma yakira iyayen Hamdan ya sanar dasu, a waya suka amsa da bakomai amma Bayan wayan, sukace Sam dansu bazai auri miskiniya ba kilama ciwon kuturta garesu, maganganu iri daban daban harya kaiga kunnen Hamdan yadinga bori shi gaskiya saiya auri Ruma ita yake kauna yakeso koda dukiyarsa zata kare akan Neman lafiyar Rumaisa shi yaji kuma yagani.
Abun sai mamaki yakeba yan’uwa tuni mahaifin Hamdan yace anfasa auren kowa yakoma gidansa Hamdan koh ajikinsa yace “Idan kunki Tara jama’a don aurena toh tabbas zaku tara jama’a takai danku kushewa” fit ya fice gidan Aunty dinsa yaje yake sanar da ita halinda yake ciki batayi kasa a gwiwa ba suka hada wani shegen plan Wanda ni kaina saida na girgiza.
Kubiyo yar MUTAN ZAZZAU donjin wani plan ne wannan?
Kuyimun afuwa rashin wuta muke fama dashi shiyasa kuka jini shuru.
[2/10, 7:26 AM] Melody????????♀????: ???? *DASHEN* ????
*ZUCIYA*
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_????
*Dedicated to Abeeda(Tautah)*????
2⃣1⃣
Hamdan yace “Aunty ya za’ayi?”
Tace “duk yadda za’ayi ka dauko Rumaisa ka kawota gidannan, nasan za’a bazama nemanka babu Wanda yasan inda zakuje, sai kuzo nan dakwai wajen dazan ajiyeku sannan, duk sauran plan din saidai kayi nasaran dauko Ruma matukar tana sonka toh dole ta biyoka” hamdan yaji abun ban barakwai anya zai iya yake yambayan kansa wani tunani yashiga inda batareda bata lokaci ba, Aunty dinsa tace “Maza ka kama hanyan Shinkafi ka aiwatar da abunda nakeso”.
Cikin gaggawa ya kama hanyan, cikin haddadiyar Motarsa, sai shinkafi kofar gidansu Ruma ya tsaya ya aika akirata amma batareda yafadi sunaba, cikin ikon Allah kamar taji a jikinta hamdan ne, tafito sanye da doguwar Riga wacce ta lullube kafarta da hannunta daman daganan matsalar take, kallon juna sukayi suka sakarwa juna wani murmushi mai kawata zuciya, hamdan yayi saurin cewa “Nasan sak’o ya isheku daddy na yace kowa ya watse babu biki, Rumaisa inasonki zanyi duk yadda zanyi ganin kinzama mallakina don haka tafiya zamuyi karkiji komai babu abunda zai faru matukar kina sona dole kiyi abunda nakeso” tuni idanunta sukayi rau rau “yanzu My blood meye makomar guduna daga gida kana ganin haka bazai kawomun matsala ba?”
Hamdan yace “babu abunda zai faru matukar su hajiya suka aminche na aureki tom zanyiwa kowa bayanin dalilina nayin haka, ruma kidubi girman Allah da son da nakemiki, kizo mutafi” batada wani choice saina tabi shi gudu yakeyi a mota cikin Awa daya da rabi suka isa cikin garin zamfara, basu zarce koh inaba sai Bayan Asibitin yariman bakura, cikin gidan suka shiga hankali kwance tuni Aunty din Hamdan ta tarbi Rumaisa ba tareda ta k’yamaceta ba.
Gida tuni ya rude ba’aga Rumaisa ba, har garin Gusau suka je amma iyayen Hamdan sukace aisu sunce anfasa biki saboda bazasu hada jini da musaka ba,
Yaya salim daya fusata yace “Ina danku indai muka ganshi toh sai kanwata ta fito don babu inda zamuje”
Mahaifin Hamdan yace “Kuna iya zama Ku jira shi Donni kunga tafiyata”.
Fita zaiyi yaya salim yace “Babu inda zaka saika fitomun da kanwata inada daman kamaka saboda inada ID card, yaciro IDCard dinsa na shedar zama Police mai Anini, kana iya bina police station Tunda naga abun naka da rainin hankali” tuni gida ya rude haka yaya salim yayi matching din Mahaifin Hamdan har police station dake hanyan unguwar gwaza da kauran namoda.