Al-Ajab

Hattara masu Abokai! Kalli Yadda Abokanan sa suka kashe shi akan zargin satar Waya a makarantar su dake Jihar Sakkwato

Innalillahi’wa İnna ilaihi raji’un saboda waya suka lashes hi????

 

Sanadiyar Kisan Matashi Maisuna Khalifa Wanda Abokan Karatun Shi Suka Kashe A Makarantar Lafiya A Jihar Sakkwato

~~ Labari ne mai sosa rai da tausayi da takaici hadi da tsotsayi acikin wannan lamarin da yafaru ga ‘yan makarantar gwadabawa.

DAGA Real Buroshi Mawaka Sokoto

Matashin dalibin maisuna Lukman wanda akafi sani da Khalifa dan garin kalambaina mai karatun sashen lafiyar hakori (Dental&surgery)

a makarantar lafiya dake gwadabawa ta jihar sokoto, ya hadu da ajalinsa ne ta sandiyar bugun taron dangin da wasu dalibai hadi da abokinsa kuma amininsa suka mishi ta hanyar daure shi da igiya suna azabartar dashi wanda hakan yayi sandiyar mutuwarsa har lahira akan zargin da sukayi mishi na satar waya.

 

Labarin da nasamu daga hukumar makarantar ya tabbatar min da gaskiyar abunda yafaru cewa ” Daliban sunie sun tayarda margavin ne da misalin karfe 2 na daren Lahadi 20-11-2022, inda suka fara sa’insa a tsakaninsu akan tuhumar da suke mishi na satar waya, daganan ne suke tilasta margayin da sai ya amsa zargin da ake mishi na dole sai ya basu wayarda suke tuhumar ya dauka” Bayan hakan bata samu ba sai suka rinjaye karfin khalifa har yakai suka daure shi suna mishi bugun akawo Wuka acikin daren tareda watsa mishi ruwan sanyi a wannan yanayin, tun daganan ne rai yayi halinsa kamar yanda wani shaidar faifan bidiyo ya bayvana inda ake jin muryoyinsu da irin kallon azabar da suke yiwa margayin.

A halin yanzu ankama mutun biyar Wadanda ake zargi da ballewar mutun daya dan asalin jihar kaduna wanda aka tabbatar cewa ya gudu ana tsakar bincike a asibitin Uduth dake nan cikin kwaryar birnin Sakkwato, wanda daga bisani aka kama direban da ake tuhumar ya boye yaron da ya gudu har sai ya fa fito da yaron a inda yake kafin asake shi.

 

Mahaifiyar margayin ta tabbatar da jadadda yafiyarta ga Wadanda suka yiwa khalifa kisan gilla, saidai hukumar makarantar tace ” Sam bazasu yafe ba har sai sun dauke mataki ga Wadanda suka kashe dalibin nasu maisuna khalifa domin hakan yazamo izna da darasi ga sauran mutane” sun kara da cewa ” idan har ba’a dauki wannan matakin ba watarana hakan zata iya sake faruwa ga wasu dalibai wanda ba’a fatar sake faruwar hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button