Yadda Malamar Makaranta Mai Shekaru 31 Ta Addabi Dalibinta Mai 15 Da Fyade


A rahoton Ance Har Sai Da Ya Yasamu Tabin Hankali Saboda Yadda Malaman Da Addabe Shi Tare Da Tilastawa Dalibin Su Sadu!”
Bawai maza malamai bane kadai suke lalata da dalibansu mata ba, suma Malamai mata ba a barsu a baya ba wajen yiwa dalibansu maza fyade.
Wata Malamar makaranta da aka nemi mu sakaya sunanta mai shekaru 31 dai haihuwa, ta samu wani yaro mai shekaru 15 dan ajinta ta sashi a gaba da ci sai da yaron ya soma samu tabin hankali.
Ance Malamar takan gayyato yaron ne gidanta a duk lokacinda mijinta yayi tafiya ko kuma zai dau lokaci bai dawo ba.
Bayan da yaron ya soma gajiya da jarabar matar ne, aka kuma fahimci ya soma samun tabin hankali. Bayan da aka kaishi gaban likitocin kwakwaluwa ne ya samu damar bayyana yadda malamarsa take huce takaicin abunda ta rasa a wajen mijinta akan yaron da bai balaga ba a dokar kasa.
Tuni dai ta amsa laifinta, alkali ya turata gidan yari na watanni 6 da kuma taran kudi kwatankwancin naira dubu 61.
Wannan yasa muke bada shawaran masu makarantu da iyayen yara su tabbatar da ingancin malamansu saboda tarbiyan yaransu.
~ Alfijir Hausa
[ad_2]