Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

41

Shiru Ashnaah tayi tana kallon Ameesha da ke bayan Khaleel ta ki shigowa, ya daka mata tsawa yace “ba kya ji na ne, nace takalmin waye wnn” Ashnaah tace “wacece wnn a bayan ka” bude baki yyi da mmki yana kallonta yace “ina maki tambaya kina min tambaya” dauke kanta tayi fuskarta a daure taki cewa komae, ya kuma daka mata tsawa yace “nace takalmin waye wnn” ta juya tana kallonsa tace “sae ka fara gaya min wacece wancan a bayan ka” ta karashe mgnr tana hararansa, ihu ta fasa ganin ya yo kanta ta nufi bayan kujera da sauri tana cewa “wayyo wllh xan gaya maka ka tsaya” ganin kamata yake son yi yasa tace “don Allah kayi hkuri na wa ne ina son in fita in siyo abu ne sae mai gadi ya hanani, sae na manta ban shigo da shi ba” tsayawa kallonta yy, yyi kwafa yace “bace min a falo” hararan Ameesha tayi snn ta haura sama. Bayan kofarta ta tarda Meenah a labe, ta fada kan gado ta dinga kyalkyala dariya, Meenah ta fito da sauri ta mata alamar tayi shiru, Ashnaah tace “ae ba shigo wa xae yi ba,” a hankali Meenah tace “to ya xa ayi in bar gidan nn yau, ga shi nace ma momy ba ddewa xan yi ba” Ashnaah tace “ae xae shi ga dakinsa sae ki fita da gudu, muyi hirar mu don Allah,” Meenah ta galla mata harara tace “da wani bakin xan yi hira, kin san ynda ciki na ke kara kuwa, ba mutun ci gare mijin nn naki ba sae ya iya wurga ni waje wllh” Ashnaah tayi dariya tace “to sae kiyi ta tsayuwan, nace maki baya shigo min daki sae in nayi laifi” dakinsa suka ji ya bude, Meenah ta koma bayan kofa da sauri har tana bugewa, Ashnaah ta toshe bakinta kar ta Tona masu asiri da dariya, fitowa Meenah tayi tace “to ya shiga dakin, ta ina xan bi” Ashnaah ta mike tace “ina xuwa” snn ta fice, ba a jima ba ta dawo rike da takalman Meenah tace “oya xo ki gudu yarinyar da ya kawo ma na kitchen, amma yaushe xa ki kuma dawowa don Allah” Meenah tace “gskya ba ynxu ba” Ashnaah ta marairaice tace “haba don Allah to wayata fa gashi fa kinsan abinda yasa nake son siyan wayar” Meenah tace “to xan yi kokari gobe in na siya in kawo maki amma fa baxan dde ba” Ashnaah tace “yauwa don Allah kar ki manta ki siyo min maganin ciwon ciki in xaki xo, wllh tsoro nake ji period dina ya kusa xuwa kuma wahala nake sha wllh, ynxu ma ya fara damuna” Meenah tace “to Allah sa kar in manta” Ashnaah ta riko hannunta tace “Aa don Allah kar ki manta ki siyo min, ina jin jiki in ina yi” Meenah tace “to naji, amma kuma ba ga ki da likita a gida ba” Ashnaah ta bude baki tace “au likita ne, ki ce wllh” Meenah tayi dariya tace “ohh da baki sani ba, wllh likita ne kuma babba ma” Ashnaah ta tabe baki tace “oho ni ina na sani” Meenah ta saka takalminta tace “kin ga sae na xo” a hnkli ta bude kofar ta shiga sauka daga stairs da sauri, da gudu gudu sauri sauri kmr munafuka ta fice daga gidan gaba daya, Ashnaah da ke lekenta ta window sae dariya take har da kyakyatawa tana rike ciki, bude kofar ta taji an yi ta juya da sauri taga Khaleel ne, da mmki yace “ke kina da hnkli kuwa, wa kike ma dariya a window” Ashnaah ta kuma kwashewa da dariya har da durkushewa inda take tana rike ciki tana kallonsa, dariyar shima ta basa, ya kauda kansa yyi murmushi ya juya ya fice daga dakin, sae da ya sauka kasa snn shima ya shiga dariyan, anya yarinyar nn ita kadae take kuwa tambayar da yyi ma kansa knn bayan ya shigo falo. Har Ameesha ta gama girkin da Khaleel ya sa ta Ashnaah bata fito ba, tasan kila adduarta Allah ya amsa, don tun da ta shigo kitchen din take adduar Allah yasa kar Ashnaah ta sauko, don ita hka kawae take tsoron ta, kan dinnin ta jera masa abincin ta karaso falon tana kallonsa tace “na gama,” ya mike xaune yana kallonta yace “thnk yhu dear, kawo nn mu ci” ta girgixa masa kai tace “ni na koshi gida xan tafi” ya harareta yace “ae kya bari in ci abinci ko” murmushi tayi ta gyada masa kai, yace “to kawo min abincin nn falo” juyawa tayi ta je ta dauko abincin ta shigo falon ta ajiye masa gabansa, bin ta kawae yake da kallo, ssae take basa sha’awa, kujera ta xauna tace “bari in jira ka a nn” ya gyada mata kai snn ya shiga xuba shinkafar gabansa a plate. Shidda saura ya mike yana kallon Ameesha yace “tashi in kai ki gida dare na yi” ta mike tana gyara mayafin kanta, shi kuma ya nufi sama, dakin Ashnaah ya bude a hankali ya sameta kwance tayi dai dai tana bacci, no wonder yyi mmkin rashin saukowarta, har xae rufo mata kofa sae kuma ya fasa, yana kallonta yace “ke” a firgice ta farka, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, ya galla mata harara yace “hka aka koya maki a gidan ku ki dinga bacci da yamma” hamma tayi tana hararansa, snn ta mike tsaye tayi mika ta nufi bathroom abunta ta bar sa nn tsaye, binta yyi da kallo har ta shiga bayin snn ya kulle mata kofar dakin ya sauka kasa, bakin mota ya tadda Ameesha tana jiransa, ya bude motar suka shiga suka bar gidan. Bakwae saura ya ajiye ta a kofar gidan su yace xa su yi waya anjima, tayi murmushinta Mae kyau ta daga masa hannu snn ta nufi gate dinsu, bin ta yyi da kallo har ta shiga snn ya sauke ajiyar xuciya yyi reverse ya bar anguwar ya kama hanyar gidansu, a masallacin da ke kofar gidansu yyi sllh snn ya shiga gida, sama ya nufa ganin bbu kowa a falo ya shiga dakin umminsa, ya sameta xaune kan darduma, sae da ya jira ta gama addu’o’inta snn ya sauka kasa ya gaida ta, ta amsa tana murmushi tace “sae yau Abbana, ina Fateema” yyi murmushi yace “tana gida ummi, rukayya fa” ummi tace “ina jin tana dakinta, daga ina kke hka,” yace “daga gidan su Ameesha” Ummi tace “Ameesha kuma, lfya dae ko” yace “lfya ummi ajiyeta nayi ne” ummi bata ce komae ba, can dae tace “to ina fateemar,” yace “tana gida nace ummi” “to ya baka taho da ita ba xaka var ta ita daya da magariban nn” shiru yyi bae ce mata komae ba, can yace “Abba na nn” ummi tace “ina ga ya dawo daga masallaci ynxu ka Duba dakinsa” mikewa Khaleel yyi yace “ina xuwa mum” snn ya fita xuwa dakin Abbansa, Abba na canxa channel xaune falonsa da remote a hannu Khaleel ya shigo, wuri ya nema ya xauna nn kasan carpet snn ya gaida dad din nasa, ya amsa yana cewa “kayi wuyar gani son” Khaleel yyi murmushi yace “wllh kam Abba aiki ne ya rike ni” Abba yace “to Allah ya taimaka, ya iyalin ka” Khaleel yace “alhmdllh Abba” hira ssae suka yi da dad din nasa daga bisanni yace “Abba dama wata magana na xo maka da, Allah yasa xaka ban goyon baya” Abba ya tattara hankalinsa gaba daya kansa yace “to ina jin ka son, wace mgnar ka xo da”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button