Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

49……

Khaleel ya kasa daina kallon Ashnaah da taki kallon

inda yake, duk da bae yi wani mmkin abinda tayi ba

yasan xata iya aikata fiye da hkn dama, da kyar ya

iya maida dubansa ga Ummi ya ga kallonsa kawae

take, ya sunkuyar da kansa, ummi tace “to tashi ka

bar min dakina” bbu musu ya mike yana kallon

Ashnaah ya fice daga dakin, sae a snn Ashnaah ta

dago kanta tana kallon ummi, kmr xata yi kuka tace

“momy dukana fa xae yi in mun koma gida wllh, ki

ce ya bar ni a nn” da mmki ummi tace “duka

kuma?” Ashnaah ta gyada mata kai, ummi ta ma

rasa me xata ce mata can dae ta mike ta fice daga

dakin, Ashnaah ta bi ta da kallo tana murmushi.

Goma saura ummi ta dawo dakin har lkcn Ashnaah

kallo take, ummi tace “tashi ki dauki hijab din ki ku

wuce gida” Ashnaah ta dan xaro ido tace “gida ynxu,

na tsamman a nn xa mu kwana ae” Khaleel ne ya

shigo dakin yana kallon Ashnaah yace “tashi mu

wuce ke nake jira” Ashnaah ta juya da sauri tana

kallon ummi kmr xata yi kuka, ummi tace “gobe xa

da safe xa ku dawo” mikewa Ashnaah tayi ta dauki

hijab dinta ta sa, tuni gabanta ya soma faduwa, tayi

ma ummi sae da safe ta fice daga dakin ya bi

bayanta. Har suka isa gida Khaleel bae ce mata

komae ba, har karkarwan sanyi ta shiga yi don tsoro

amma ko kadan hkn bae nuna a fuskarta ba, sae da

ya jira ta fito snn ya kulle motarsa ya nufi cikin

gida ta shiga jan kafarta da kyar tana bin sa a

baya, oh ko wani irin duka kuma xae mata yau, kin

shiga falon tayi ta tsaya daga bakin kofa tana

kallonsa fuskarta daure, bae ma san tana yi ba din

jira kawae yake ta shigo ya rufe kofar sa, ganin

bata shigo ba ya sa ya daga kai yana kallonta,

dauke kanta tayi da sauri still ta ki shiga falon, ya

juya ya nufi stairs kawae ya haura sama, ta kusa

minti talatin bakin kofar taki shigowa falon ga wani

mugun bacci da take ji, daga karshe dae ta gaji don

kanta tayi shahada ta shiga falon kmr xata yi kuka

ta rufe kofar ta nufi cikin falo ta xauna, har bacci

ya samo dauketa daga xaunen da take taji kmr

motsi kusa da ita ta mike tsaye a tsorace ta gansa

a gabanta ya duka, da sauri ta bar wajen ta ga

remote din dake kan kujerar da take ya dauka snn

ya mike tsaye yana kallonta yace “ni bani da lkcn ki

ynxu, i mean ban gama gather din tym dinki ba”

kashe tv dinsa ta ga yyi snn ya kashe wutan falon

ya nufi sama ta bi sa da kallo snn ta yi murmushi a

xuciyarta tace ko dae momy tace kar ka taba ni ba,

sama ta nufa xuciyarta fal murna ta bude dakinta ta

shige. Washegari da safe Khaleel ya kai ta gida gun

Ummin sa kmr ynda ta umarce shi, bbu yabo bbu

fallasa ta amsa gaisuwarsa ya juya ya fice daga

dakin, ummi na kallon Ashnaah tace “kina ji na

fateema, ki kwantar da hankalin ki, in dae har ina

Raye a doron kasa baxan taba barin Khaleel ya

walakanta ki ba, ki kyalesa yyi auren sa kar ki tada

hankalin ki kin ji” da mmkin ummi sae gani tayi

Ashnaah tayi murmushi ssae tace “to momy dama ni

bn daga hnklina ba” Da rana Khaleel ya xo tafiya da

Ashnaah gida, ko kadan bae ji ddin irin ynda

umminsa ke amsa masa gaisuwa ba, Ashnaah tayi ma

Ummi sallama ta sa hijab dinta ta bi bayan Khaleel,

yana gama parking a gida ya bude motar ya nufi

cikin gida ba tare da ya tsaya kulle wa ba ya bar ta

nn ciki. Washegari lahadi yana kwance dakinsa idonsa

lumshe kmr me bacci ya ji an danna bell, ya mike

xaune yana kallon agogo ya ga goma da kusan rabi

to waye kuma wnn, tashi yyi ya fita daga dakin don

xuwa ganin Wanda ke bakin kofar. Najeeb ne tsaye

yana kkrin kiransa, Najeeb yace “bacci kke ne”

Khaleel yace “aa na tashi tun safe” hanya ya basa

ya shigo falon snn ya shiga tambayarsa daga inda

yake, Najeeb yace “gida mana” Ashnaah ce ta fito

daga kitchen sanye da dogon rigan baccinta har kasa

pink colour me tsantsi, gashin nn nata me kyau na

daure da ribbon baki, hannunta rike da cup din tea,

Khaleel ya juya da sauri da kuma mmki yana kallonta

don bae san tana kasa ba da baxae bude kofar ba,

kallonta kawae Najeeb yake ko kiftawa baya yi, wani

irin tsawa da ya raxanata Khaleel ya daka mata ba

tare da yasan yyi hkn ba yace “me ya sauko dake

nn” tsayawa kallonsa tayi kmr wata sha sha sha don

ita dariya ma ya bata, Khaleel ya juya yana kallon

Najeeb da har lkcn bae kifta ido ba yana kallon

Ashnaah, a fusace Khaleel yyi kanta, ta fasa ihu ta

juya xata koma kitchen da gudu, ya cafkota don

tsabar tsoro hka ta sake cup din hannunta tana

kwala ihu, janyeta yyi daga wajen da sauri ganin cup

din ya tarwatse da ruwan tean ciki, bata ankara ba

taji ya dauketa kmr wata yar bby ya nufi sama da

ita, dakinta ya bude ya jefata ciki yana nuna ta da

dan yatsa yace “wllh wllh kika sauko min falo sae na

kusan fasa maki kai” bae jira me xata ce ba ya fice

daga dakin ya sauka kasa, sae a snn Najeeb ya

sauke ajiyar xuciya ya xauna, Khaleel ya hade rae ya

nufi kitchen ya dauko broom da packer don kwashe

kwalaben da ke kasan falon, sae da ya gama tidy

din wajen snn ya xauna yana kallon Najeeb yace “ya

aka yi guy any prblm” Najeeb ya sauke ajiyar xuciya

yace “wae wnn ita ce yarinyar Khaleel” Khaleel xae

yi magana ya ji muryar Ashnaah a bayan su.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar50….Mikewa Khaleel yyi ya bude baki da mmki yana kallonta, rasa ma me xae ce mata yyi, to wae ita wnn wace irin mutum ce, tambayar da yyi ma kansaknn a xuciyarsa yana ci gaba da kallonta, ta galla masa harara tace “to wae sbda kayi bako sae in ta tsayawa da yunwa baxan nemi abinda xan sa a cikina ba” Najeeb ya fashe da dariya har da kyakyatawa, a fusace Khaleel yyi kanta kan tayi tunanin gudu har ya kamata ya kuma komawa sama da ita ya bude dakinsa ya tura ta ciki da karfi snn ya kulle dakin ya jingina jikin bango ya dafe kansa, yana tunanin shi kam me xae ma yarinyar nnya ji ddi bnda Wanda yyi niyyar mata da, yana ji tanarusa kuka tana bubbuga kofar ya juya ya sauka kasa, Najeeb yace “haba doctor, ka barta tayi harkangabanta mana, me ta tsare maka a nn, ko kuma in ce me ta tsare mana” kallon bnxa kawae Khaleel ke masa, can ya ja tsaki yace “look, idan bbu takamaiman abinda ya kawo ka ka tashi ka bar min gidana in tafi in kwanta pls” Najeeb ya hade rai yace”ka ga fa wlkncin ka ke hadani da kai wllh, is there anything wrong with my coming here? Sae in tashi in bar maka gidan ka malam” Khaleel ya dan yi murmushi yyi kwanciyarsa kan 2sitter din da yake xaune yace “to Allah ya baka hkuri” Najeeb yace “to ynxu dae wnn ita ce yarinyar da ka aura” Khaleel yace “yeah” Najeeb ya dan yi shiru snn yace “kayi ynda nace maka?” mikewa Khaleel yyi da sauri ya xauna yana kallonsa yace “look ni fa bbu abinda xanbari ya shiga tsakaninmu, ni dae nasan I only romance her once or twice, ta min yarinya da yawa nd beside wahalar da kaina kawae xan yi, in ma ka ga nayi sha’awarta to I saw half naked ne amma hka kawae bata bn sha’awa, ka bar big gals irinsu Ameesha da sauransu” Najeeb ya dan shafa gemunsa yace “to ka saketa Khaleel, stop wasting ur tym wllh” Khaleel yace “dats d lst thing I wil do onearth a ynxu dae” Najeeb bae kuma cewa komae basae tsakin da yyi. Karfe sha biyu da rabi Najeeb ya bar gidan, Khaleel ya rakasa har gun motarsa snn ya dawo ya nufi dakinsa ya bude ya tura a hnkli ya shiga, kwance ya sameta kan 3sitter ta juya baya a falo, ya karasa kusa da ita a hnkli ya duka yana lekan fuskarta don duk a tunanin sa bacci take, ido hudu suka yi ya koma baya da sauri ta mike xaune fuskarta a daure tace “meye kke wani lekana” daukekai yyi ya nufi kofar falon ya bude yana nuna mata waje yace “xo ki fita” mikewa tayi ta fice daga dakin kmr xata tashi sama ya bita da kallo har ta sauka kasa snn ya dan yi murmushi ya kulle dakinsa. Washegari Ashnaah na kitchen da rana tana girka shinkafa da miyar da xata ci, sae gunguni take ita daya a kitchen kmr xata yi kuka tana cewa ni dae nagaji da wnn wahalan yaushe rabon mutum da ya ci nama kullum abinci lami to Allah ya Isar min tunda ba hka ake yi a gidan mu ba naga, jin an bude kofar falon yasa tayi shiru tana sauraro taji wnda xae shigo, shirun da taji yasa ta dan leka falo taga Meenah tsaye, da sauri ta fito tana washe baki tace”lahh ashe ke ce Meenah sannu da xuwa” Meenah tace “baya nn dae koh? Don bn yrda da masu gadin nn ba” Ashnaah tayi dariya tace “baya nn wllh” Meenah ta xauna nn tsakiyar falon ta shiga bude Jakarta ta ciro kwalin wata yar karamar waya me kyau techno, da dan envelop fari karami tace “ga wayar da na siyo maki, wnn kuma maganin da kika tambaya ne gashi” Ashnaah ta galla mata harara tace “bayan har na gama period din ma, ae mutuwa kadae ne bnyi ba wllh” Meenah tace “eyya, wllh momy ce ta hanani fita, ki ce daurewa kawae kika ta yi” Ashnaah tayi dariya tace “yayanki ne yyi min allura wllh” Meenah tace “Ahh anyi abun arxiki su Khaleel” Ashnaah tayi dariya ta dauki wayar tana dubawa tace “amma yana da kyau wllh, bari in dauko nmbr mu gwada kira, kin dae sa min kudi koh” Meenah tace “ke Zeenat fa ta koma gidansu tun shekaranjiya” Ashnaah ta dafe kirji tace “ki ce wllh” Meenah tace “wllh kuwa, bn san ynda suka yi ba ni ma, duk bin kwakkwafi na ban gano komae ba wllh” Ashnaah da har jikinta yyi sanyi ta maxa tace”to ae bae baci ba, still sae na kirasa wllh, ae baxae san khaleed din ne ya sace yar sa ba” Meenah ta fashe da dariya tace “ke khaleel sunansa ba khaleed ba” Ashnaah tace “ayyo” bell suka ji an danna duk suka mike a tsorace lkci daya tace”waye?” Murya masu gadi taji, Ashnaah tace “ya aka yi?” Suka ce kaya ne oga yace a shigo da, Meenah tace “ya dawo ne” suka ce “ehh” sama ta nufa da gudu har tana faduwa, Ashnaah ta dauki wayarta da sauri ita ma ta nufi sama don ta boye, sae da ta boye snn ta sauko ta bude masu kofar ta ga akwatuna hudu a bakin kofar, dae dae lkcn da Khaleel ya karaso balconyn yace “ku shiga da su mana” waje ta basu suka shiga da akwatunan tana binsu da kallo, Khaleel ma ya shigo falon yana bin ko ina da kallo yace “me ke konewa hka” da gudu Ashnaah ta nufi kitchen tana cewa “innalillahi wa inna ilai hi raji’un” ya bi ta a baya da sauri, tana shiga kitchen din ta fasa wani ihu bayan ta sauke miyar ta durkushe kasa da sauri tana ci gaba da ihun, ba karamin tsorata shi tayi ba ya durkushe gabanta ya dagota duk a tunanin sa abu ne ya shiga idonta, a rude yake tambayarta “menene?” Kin bari ya daga fuskarta tayi, yace “wait don Allah ki gaya min me ya shiga idon” da kyar ta bari ya daga kanta,yana kallon idonta da ko digon hawaye bbu yace “to me ya shiga idon” kmr xata yi kuka tace “miyar da na sha wahala nayi ya kone”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button