Complete Hausa Novel.DR KHALEELHAUSA NOVEL

DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

57…..

Ashnaah ta bude motar ta shiga har lkcn tana kallon motocin da suka shigo gidan da kaya with much interest, ko kifta ido bata yi, Khaleel ya ja motar bayan ta shiga suka bar gidan, sae a snn ta juya tana kallonsa tana murmushi hade da washe hakoranta, ganin taki daina kallonsa yasa yace “wae lfya kike kallona hka” kmr jira take ta fashe da dariya har da kyakyatawa tana kallonsa tace “na ga ka kusa xama ango ne ina taya ka murna,” bae ko kalleta ba ya mayar da hnklinsa kan tukin da yake, tace “kayan amaryar ne aka shigo da ynxu knn?” Ya galla mata harara yace “wnn ba Matsalar ki bace” shiru tayi tana hararansa, can kuma tace “to yaushe ne bikin” nn ma bae tanka ta ba amma fuskarsa a daure yake, tace “to ya naga baka sauya kujerun falo ba da tv ko Akwae sauran tym ne” parkin taga yyi a fusace ya fixgota da shirin xabga mata mari, ta fasa ihu tare da rike hannyensa ta boye fuskarta jikinsa tana basa hkuri, kallonta ya tsaya yi ya kasa dukan nata har lkcn yana rike da ita, ta dago kanta a hnkli tana kallonsa kmr xata yi kuka tace “to don ina taya ka murna, da ina bakin ciki ae baxan dinga tambayarka ba hka, amma tunda baka so na daina” turata yyi ya ja motar suka bar wajen, ba ta kuma cewa komae ba ta hade rae ita ma, ganin tuki kawae yake yasa tace “to wae a ina kasan gidan namu ne da kke ta wani tuki,” ba tare da ya kalleta ba yyi murmushi yace “fitsararrki da girman kae ya sa nasan gidan ku” juyawa tayi tana kallonsa bata dae ce komae ba, can dae ta dauke kai hade da tabe baki tace “to ka ji ddi” har kofar gidansu yyi parkin ta bude mota xata fita ya fixgota yana kallonta da kyau yace “kika kuskura kika fita xuwa ko ina ban yafe maki ba don ba da izini na kika yi hkn ba, gidan ku kadae na kawo ki,” ya kalli wristwatch din hannunsa yace “dis is after eleven, xuwa Karfe biyu ki shirya xan xo daukar ki” yana kai wa nn ya turata, ta fice daga motar tana masa wani matsiyacin kallo tace “to kai kuma a suwa, ae wllh daga nn sae inda mai na ya kare, kuma ina jiran ka Karfe biyun in ga ko shigowa xaka yi ka jawo ni” tsaki tayi ta shige gate dinsu, ya bi ta da kallo yana murmushi yyi reverse ya bar anguwar, da fara’a Ashnaah ta gaisa da Mai gadinsu snn ta nufi falonsu gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parkn space, murya can ciki tayi sallama ta shiga falon gabanta yyi mugun faduwa ganinsa xaune yana kallon news, kallo daya yyi mata ta dauke kai, Ashnaah ta karasa inda yake jiki ba kwari ta durkushe kasa a sanyaye tana kallonsa tace “ina kwana Abba” ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan tv yace “lfya lau” daga nn bae kuma cewa komae ba, rasa abin cewa tayi, hkn yasa ta sunkuyar da kanta, ta kusa minti biyar a gun, shi dae bae ce Mata komae ba, nn da nn Hawkeye ya cika idonta ta mike a sanyaye ta nufi sama gwiwanta a sace, tana shiga dakin momynta ta xube nn gabanta ta shiga rusa mata kuka, momy ta dago ta a rude tana tambayarta me ya faru, cikin kuka tace “momy Abbana bae kulani ba” a fusace momy tace “to sae me, kada Allah yasa ya kula ki din ae ba gun sa kika xo ba” da kyar Momy ta lallasheta tayi shiru tana ajiyar xuciya, momy tace “daga gida kike?” Ashnaah ta gyada mata kai alamar eh, momy tace “ke daya kika xo” Ashnaah ta share guntun hawayen fuskarta tace “Aa shi ya kawo ni, Momy Ashfah pa?” Momy tace “tana gidan inna” Ashnaah tace “tana xuwa sch har ynxu ko” momy tace “eh tana xuwa” nn da nn wani hawayen ya kuma taruwa idon Ashnaah, a sanyaye momy tace “ke har ynxu baki koma ba ko?” Hawaye ya shiga bin kuncinta tace “ya ki Bari na in koma momy, ranan nayi ma mum dinsa mgna ta taya ni masa mgna ya bar ni in koma makaranta, sae da muka dawo gida yace shi baxae iya biya min kudin makaranta ba sae dae in babana ne xae dinga biya min” momy tayi shiru tana kallonta snn tace ” ki fada min gskya fateema, kin san mutumin nn ko baki san shi ba” Ashnaah tayi shiru don tasan in ta gaya ma momynta gskyar abinda yasa Khaleel ya aureta kila ita ma fita harkanta xata yi don sau tari xancen ta baya wuce ta bar walakanta samari don bata san xuciyar wani ba sanin halin Ashnaah knn wlknta mutane,” Ashnaah ta girgixa kai a sanyaye tace “Momy ni ban san shi ba” momy tace “to Allah xae saka maki, kuma ki kwantar da hnklinki wataran in Allah ya yrda gskya xata bayyana, kuma duk ran da hkn ya faru ni na tabbata ko Baban ki baxae bari ki ci gaba da xama da mutumin nn ba bare ni” Ashnaah dae bata ce komae ba kanta a kasa, momy tace “to ki tafi gidan inna ku gaisa kar kuma ki Mata xancen komae don tana iya tasowa ynxu ta xo ta sami Abbanku ta kuma ja maki matsala, kawae ki nuna mata lfya kike xaune da mijin ki, Ashnaah ta dan yi shiru duk da tana son xuwa taga kakar tata da yar uwarta Ashfah, can ta dago tana kallon momynta tace ” momy bae san xan je can ba ae, kums Ca yyi kar in je ko ina daga nn” sake baki Momy tayi tana kallonta, Ashnaah ta dauki wayar momyn tace “bari kawae in kira Ashfahn ta xo ta sameni.”

Like · 7 · Reply · Report · 12 minutes ago

~Dr Khaleel~ by Khaleesat Haiydar

58…..

Karfe uku saura mai gadi ya danna bell, Abban Ashnaah da ke xaune falo har lkcn ya mike da kansa ya bude kofar, mai gadin ya gaishesa da ladabi snn yace “wae fateema ce mai gidanta ke jira a waje” Abba yace “OK bari ayi mata mgna” wayarsa ya dauka ya kira Ashfah da ke sama, nn da nn ta sauko tace “gani Abba” ya bata sakon mai gadin, ta koma sama ta shiga dakin Momynsu tana kallon Ashnaah tace “wae mijin ki na jiran ki a waje” Ashnaah ta hade rae tana hararanta, Momy tace “haduwa ku ka yi da shi ne” da sauri Ashfah tace “aa, Abba ne ya kirani ynxu yake gaya min, ina jin mai gadi aka aiko” momy ta juya tana kallon Ashnaah da tuni yanayinta ya canxa tace “to tashi ki tafi fateema, tun da Abban ku aka ba sakon” bata yi musu da momynta ba ta mike a sanyaye ta sa hijab, Momy ta bude Jakarta ta kirgo dubu ashirin ta mika mata tace “gashi sae ki rike a hannunki kiyi transport xuwa makaranta, kawae nuna masa xa kiyi Abbanki ne ya baki, kiyi ta hkuri wataran sae lbri kin ji” Ashnaah ta share hawayen da ke bin kuncinta, ta karbi kudin a hnkli tace “to ngd Momy, Allah ya saka da alkhairi” turarruka momy ta harhada mata snn suka rakota har Downstairs da Ashfah, Ashnaah ta karasa falon Abbanta a sanyaye ta duka tayi masa sallama, ya amsa tare da cewa “Allah shi kiyaye hanya” mikewa tayi tana kallon momynta da ke ta hararan mai gidan nata, ta dauke kai suka kuma sallama da momynta snn Ashfah ta rakata har bakin mota inda Khaleel ke jiranta a waje, daga inda take tsaye ta gaishesa murmushi dauke fuskarta, kallonta ya tsaya yi da mugun mmki, sae kuma juya yana kallon Ashnaah da ta hade rae har lkcn hawaye na idonta tana kallon Ashfah tace “nagode sister, ki gaida min da inna in kin je” Ashfah tayi murmushi ta daga mata hannu snn ta juya da sauri ta shige gida ganin ynda Khaleel ke kallonta har lkcn mmki bayyane a fuskarsa, juyawa yyi yana kallon Ashnaah a karo na biyu kmr xae yi mgna sae kuma ya fasa, tada motar yyi suka bar anguwar, idonsa na kan titi yace “dama ke twin ce?” Bnxa tayi masa Hkn yasa bae kuma cewa komae ba har suka isa wani babban shoppn mall.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button