DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
59…..
Khaleel ya juya yana kallonta bayan ya gama parkn bbu yabo bbu fallasa yace “ki fita ki xabi abubuwan da kike so, sae kuma ki kuma xuwa ki ce ma ummina ban siya maki komae ba,” yana kai wa nn ya fita, bbu musu ta fito ta bi bayansa suka shiga tayi shoppn dinta mai yawa, komae taga ni ko bae mata ba jefa shi cikin trolley take tsabar mugunta, shi dae bin ta da kallo kawae yake, har ta gaji don kanta fuskarta daure tana kallonsa tace “na gama.” Yyi murmushi yace “tot baki gama muguntan ba ae” Kusan kayan dubu hamsin ta diba don yawancinsu duk turarruka masu tsada ne da takalma, ya biya kudin snn suka fito aka loda masu kayan a bayan mota, sae da ya fara siyan table water a gun da ake sayar da drinks cikin mall din snn ya nufi motarsa, Ashnaah ta juya tana kallon ruwan hannunsa ta hade rae tace “to ni ma Ae xan sha ruwan” juyawa yyi yana kallonta da kmr xae yi mgna sae kuma ya fasa, ya bude ruwan hannunsa ya sha kusan rabi snn ya rufe ba tare da ya kalleta ba ya mika mata, ta xaro ido tace “tab” ajiye ruwan sa yyi ya tada motar ys kama hanyar gida. Biyar saura suka isa gida, bata bi ta kan kayanta dake bayan mota ba ta nufi cikin gidan da sauri don xuwa ta ga gyaran da aka yi ma dakin amarya, mutane ssae ta tarar cikin gidan, duk suka bi ta da kallo, ita ma hka, tabe bak tayii ta nufi sama, dakin da ke kusa da nasa ake jeran, ta karasa bakin kofar dakin tana leken dakin ba karamin hadewa dakin yyi ba, kmr na wata yar shugaban kasa, ta tabe baki hadewa da cewa ikon Allah, kallonta kawae mutanen dake ciki suke da mmki, sae da ta gama kare ma ko ina kallo daga Bakin kofar snn ta juya xata bar wajen dae dae lkcn da Khaleel ya hauro sama, kallonta ya shiga yi yace “me kike yi a nn” a takaice tace “bai ma ido na abinci” bata jira cewarsa ba ta shige dakinta, sae da ta cire kayan jikinta snn ta dauki xani ta daura tayi kwanciyarta xuciyarta fess nn da nn bacci ya dauketa. Can after magrib ta farka tayi sllh, snn ta sauko downstairs sanye da hijab dinta, tsit kke jin gidan alamar duk an watse, falo ta tarar da Khaleel xaune yana cin fruit lkci daya yana waya, kallo daya tayi masa ta nufi kitchen tana tunanin me xata girka ta ci, daga karshe ta ga indomin ma baya ranta ta hada tea mai kauri ta fito, har ta nufi stairs sae kuma ta dawo tana kallon Khaleel fuskarta daure tace “gobe fa xan tafi sch” juyawa yyi yana Mata mugun kallo yace “get out ki ban waje” xaro ido tayi tana kallonsa ta ajiye tean hannunta da sauri ta xa gayo cikin falon tana kallonsa tace “ban gne ba, da xu nayi ma Abbana mgna, har ya ban kudin mota da xan fara xuwa, dama mun kusa fara exams in ji su ummi” yana mata mugun kallo yace “to bbu inda xa ki, bar min falona” kuka ta saki ssae tana cewa “wllh sae na je, tunda kace sae in ubana ne xae dinga biya min, kuma gashi ya bani kudin mota ya ce in tafi” mikewa
yyi ya daka Mata tsawa yace “bar min falona kar in taka ki, Baban ki ke da iko da ke a ynxu ko ni, nace bbu inda xaki, kuma hkn ya xauna” kuka takaici ta kuma fashewa da ta rufe ido ta shiga fesa masa rashin kunya, ya yo kanta ta bar gun da gudu tayi ball da cup din tean da ta ajiye kasa, mug din ya tarwatse ruwan tean ya malale ta fasa ihu ta durkushe wajen, karasowa kusa da ita yyi da sauri ganin jini a kafarta, ya duka gabanta yace “subhanallahi” kuka ta dinga rusa masa tana yarfe hannu, ya Duba kafar ya ga yankewa kawae tayi a tafin kafar, daukar ta yyi ya nufi sama da ita ya bude falonsa ya shiga snn ya nufi bedroom dinsa ya xaunar da ita gefen gadonsa, cire mata hijab din jikinta yyi ganin har kasa yake ja, spirit ya dauko da cotton wool xae wanke mata gurin ta rike sa a tsorace tace “aa ni wllh bna so xafi xae min” ya ce “dan kadan xan sa maki, rufe idonta tayi lkci dayata ta saki ihu ta dafa kafadansa jin wani shegen xafi yana wanke wajen, daga kai yyi yana kallonta har lkcn yana rike da kafarta idonsa ya sauka kan kirjinta da yake hangowa daga durkushen da yake, bude ido tayi a hnkli tana kallonsa, ta xaro ido ganin abinda yake ta kare kirjinta da sauri, mikewa yyi shima da sauri ba tare da ya kalleta ba yace “jinin ya tsaya, nxt wk sae ki fara makarantar kafin nn an kawo min amaryata” mikewa tayi cike da jin ddi ta fice daga dakin. Ran Friday bayan an sauko daga juma’a aka daura auren Ameesha da Khaleel, Ashnaah kam ko a jikinta don ko momynta ma bata gaya ma ba bare wani nata, throughout ranan gidansu Khaleel ta yini da su Meenah don tun da safe ya kai ta, ummi tausayin Ashnaah kawae take don ta ga kmr yarinta yyi Mata yawa ganin ynda take ta harkan gabanta kmr ba kishiya aka mata ba, ita ko ranan dama ta samu dn sun fi awa biyu suna waya da usman dinta, bayan isha Ashnaah na kwance dakin Rukayya tana game da Sabon wayarta Meenah ta shigo rike da Jakarta alamar xata wuce, Meenah tace “wae fateema baki fada min ynda ku ka yi da Baban Zeenat ba ko daxu ta kirani wllh, ko dae har kin fara tausayin mijin naki ne” Ashnaah tace “wani tausayi? Ni wllh na ma manta, ae gwara da kika tuna min bari ma in je in kirasa ynxu wllh” Meenah tace “dare bae yi ba” Ashnaah tace Karfe fa takwas da rabi ynxu” mikewa ashnaah tayi ta fita don xuwa garden ta kira dad dn Zeenat, Meenah na biye da ita a baya. Dai dai bakin kofar fita suka hadu da Khaleel xa su shigo da su Najeeb, Meenah ta koma baya da sauri Khaleel ya shiga Mata wani irin kallo can yyi murmushi yana kallonsu Najeeb yace “nn da wata biyu xa ku kuma xuwa daurin aurena idan Allah ya yrda,” Najeeb dae bae tanka sa ba sae kallon Ashnaah yake, juyawa Ashnaah tayi ta koma sama cike da jin haushin kiran da bata yi ba, Meenah ma ta ja tsaki ta bi bayanta. Karfe tara saura Khaleel ya sallami momynsa da ta ki sakar masa fuska tun da ya shigo gidan tafiya da Ashnaah, nasiha ssae ummi tayi ma Ashnaah kmr ynda xata ma yar ta snn tace ta tashi su tafi, Ashnaah ta mike tana kallon Khaleel shi ma ya mike snn yyi ma umminsa sae da safe ya fita.
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
60…..
Khaleel ya juya yana kallon Ashnaah bayan ya gama parkin yace “ina son maki wata
tambaya” juyawa tayi tana kallonsa da mmki fuskarta daure tace “tambaya kuma” ya
dan yi shiru snn yace “ki fada min gskya tsakanin ki da Allah, ke kika mare ni ko ba ke
bace” dariya ma ya bata ssae, tana kallonsa da kyau tace “idan bani bace ba fa?” Bbu
yabo bbu fallasa yace “yea sae in sake ki, in dauki revenge Dina kan warce ta marenin, I
mean ur twin sis, don ni bana cuta, nd I wil ask for ur forgiveness of course” shiru
Ashnaah tayi tana kallonsa, ba dan ba dan ba da tace ba ita bace but tana mugun son
yar uwarta baxa ta so wani abu ya sameta ba, can tace “to idan bani ba ce fa?” Ya
shafa sajensa yace “baxan sake ki ba har sae kin duka don kanki bayan na gama koya
maki hnkli kina rokon in yafe maki kin gane kuskuren ki” Ashnaah tayi masa wani
matsiyacin kallo snn ta fashe da dariya tace “dats d last thing da xan yi a rayuwa in
duka ina baka hkuri don ni nasan ban maka komae ba kai ka min, ni da kai xa mu ga
wnda xae gaji yyi surrender. Kuma karka kuskura ka sama yar uwata ido bbu ruwan ta
ni ce nn Fateema na mare ka” Bata jira cewarsa ba ta fice daga motar ta nufi cikin
gida, bin ta yyi da kallo snn yyi murmushi ya fito ya kulle motarsa ya bi bayanta.
Ashnaah ta tsaya corridor din dakuna tana ta kallon dakin Ameesha tana tabe baki,
dakin ta nufa ta tura kofar a hnkli tana kallon cikin dakin, xaune ta ganta kan rug din
tsakar dakin ga kanwarta farida da kawayenta biyu xaune suna ta hira, da mmki
Ashnaah ta ke kallon Ameesha don bata san ita ce amarya ba sae ynxu da take
ganinta, Ameesha dae ta dukar da kanta, Ashnaah tayi murmushi tace “welcm to hell on
earth yar uwa, har na tausaya maki wllh” juyawa tayi ta fice daga dakin, kawayen
Ameesha da ransu ya baci suka ce wacece kuma wnn yar yarinyar ko ita ce uwar
gidan, Ameesha bata ce masu komae ba sae hawayen da ta shiga yi, kanwarta Farida
da baxa ta wuce Ashnaah ba tace “wat? Kuka kike ko me yaya? Wait wae ita kike ma
kuka” a sanyaye Ameesha tace “nace ma Khaleel ya raba mana gida ya ki, ni bana son
tashin hnkli wllh” farida ta fashe da dariya tace “wllh ba ki yo xuciyar mama ba Anty,
ko ni na xage baxan ma yarinyar nn duka ba, dubeta kawae galallawa rai ba gata”
dariya sauran kawayen Ameesha suka yi, Ameesha tace “ni dae bbu ruwana bana son
tashin hnkli ki tashi ki tafi gida” farida tace “wllh bbu inda xa ni, in ta isa ta kuma shigo
mana ta ga ko baxan ballata ba” Ameesha tamike a fusace ta nuna mata kofa tace
“kinga tashi ki bar nn kar in bata maki rai” mikewa farida tayi ta fixgi Jakarta da yar
mayafinta ta fice daga dakin, kawayen nata ma sun yi niyar kwana amma ganin abinda
tayi ma yar uwarta yasa su ma suka mata sallama suka kara gaba, hkn yasa ta shiga
kuka a hnkli ita kadae, a hka Khaleel ya shigo ya sameta, ya xauna gefen gado yana
kallonta yace “wae kuka kike yi Khadija” bata ce masa komae ba hkn yasa ya mike ya
fita ta bi sa da kallo a sanyaye. Bayan kusan minti talatin ya dawo dakin sanye da
jallabiyarsa ya ajiye coffen hannunsa yana kallonta yace “kina ji na” ta dago tana
kallonsa ya dan sakar mata murmushi snn yace “hope xa kiyi amfani da abubuwan da
xan gaya maki” ta gyada masa kai kawae, yace “Kinga ke ce matata a gidan nn, don ita
wancan she is just here for some tym, don hka duk wani responsibility na gidan nn na
kan ki, tun daga kan girki nd every other chores, more importantly bbu ruwan ki da
wancan yarinyar, ke ce matar gidan nn ba ita ba duk da nasan baki da fitina,” yyi shiru
snn yace “I think dats ol” ta sunkuyar da kanta tace “in sha Allah, I wil abide” daukan
coffensa yyi ya karasa shanyewa, ita kuma ta mike ta nufi bathroom. Washegari da
safe Ameesha na kitchen tana hada breakfst Ashnaah ta shigo kitchen din, ta tsaya
daga bakin kofa tana kallonta, Ameesha ta dan yi murmushi tace “gud mrnin” Ashnaah
tace “mrnin Amarya, girki kike?” Ba tare da Ameesha ta kalleta ba tace “ehh” Ashnaah
ta karaso kitchen din ta dauki wata yar kula ta ajiye kusa da ita tace “to in kin gama ni
ma ki xuba min nawa” tana kai wa nn ta juya ta fice daga kitchen din. Ameesha ta
gama hada break din ta jera dinnin ta ajiye wnda ta xuba ma Ashnaah, dae dae nn aka
bude kofar falon Farida ta shigo da kulan abinci, da mmki take kallon yayarta tace “wae
girki kika yi” Ameesha tace “eh har na gama,” farida ta tabe baki ta ajiye kulan hannun
ta tace “sae anjima.” Khaleel ya sauko downstairs yana kallon Ameesha yace “wa ya
shigo ynxu” tace “farida ce ta kawo abinci” yace “OK” snn ya nufi dinnin ya xauna yana
bude girkin da tayi, kulan da ta xuba ma Ashnaah ya bude yace “wnn fa” tace “Ca tayi
in dibar Mata ita ma” wani kallo ya shiga yi mata yace “ita me ya hanata saukowa tayi”
dae dae lkcn da Ashnaah ta sauko falon tana kallon Ameesha tace “har kin gama
amarya” Ameesha tace “ehh ga shi can a dinnin na xuba maki” Ashnaah ta nufi dinnin
din ba tare da ta kalli Khaleel ba xata dauki kulan ya Riga ta daukewa yana mata
mugun kallo yace “ki shiga kitchen kiyi girkin mana” Ameesha ta karaso dinnin din tana
murmushi tace “ae ta shigo taya ni daxu”
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
61….
Ashnaah ta gama feshe jikinta da turare snn ta
saka hijab dinta ta dauki yar Jakarta ta rataye a
kafada snn ta dauki dubu biyu cikin kudin da
momynta ta bata ta fito, dakin Ameesha ta nufa
ta sameta xaune gaban madubinta, Ashnaah tace
“na tafi sch” da sauri Ameesha ta juya tana
kallonta tace “da gske, ya bar ki ne” Ashnaah ta
tabe baki tace “kar ma ya bar ni mana, kinsan ne
xa ki girka mana yau” Ameesha tace “aa”
Ashnaah tace “jollof rice” Ameesha tace “OK
Allah ya kiyaye hanya amma ki fara gaya masa
kan ki fita kar kiyi laifi” Ashnaah tayi dariya tace
“ae ni bana laifi” juyawa tayi ta fice ta sauko
kasa, xaune ta same shi falo, ba tare da ta
kallesa ba ta nufi kofa, mikewa yyi da mmki yace
“ina xa ki?” Ashnaah ta hade rae tana kallonsa
tace “ba kace yau Monday Zan yi resuming ba”
tsayawa kallonta yyi ya ma rasa me xae ce mata,
can ya daka mata tsawa yace “to baxa ki ba, yar
rainin wayo” kmr jira take ta fashe masa da kuka
tace “amma kae fa kace min yau” yace “don
nace maki yau shine xa ki xo ki wuce ni ba tare
da kin ce xaki fita ba” ta dan marairaice gudun
kar ya hanata tace “to nayi xaton bacci kke ae”
tsayawa kallonta yyi ta sunkuyar da kai da sauri,
ya kauda kansa yyi murmushi, can ya kuma
kallonta yace “to a hka kike tunanin xa ki fita
fuskarki a waje? Ina nikaf din ki” juyawa tayi ba
musu ta koma ta sako nikaf snn ta sauko, daukar
makullin motarsa da ke kan center table yyi
fuskarsa daure yace “mu je” kmr xata fasa ihu
take kallonsa don bata so ya kai ta ba, amma
bata ce komae ba gudun kar yace bbu inda xata
kuma, ta bi bayansa, har cikin makaranta Khaleel
ya ajiyeta yana kallonta da kyau yace “na hane ki
da yi ma ko wani namiji mgna, Karfe nawa xa ku
gama lecture” tace “shidda” bata jira cewarsa ba
ta bude mota ta fice. Ba karamin farin ciki su
ummi suka yi ba ganin Ashnaah, ita kanta ta ji
ddin ganinsu togeda once again, Karfe uku da
rabi suka gama lecture dinsu na ranan, duk ta
karbi handouts tayi foto copy don saura sati biyu
exams dinsu, suna xaune karkashin wata bishiya
gaba daya da kawayenta wajen shidda saura sae
tambayarta ya mijinta suke ta ki basu amsa,
mota suka ga yyi parkn dai dai inda suke,
Ashnaah ta mike tana murmushi ta nufi motar,
duk suka bude baki suna kallonta don tunda suka
fito lecture ta kebe gefe guda tana waya basu
kuma san da wnda take ba, bude motar tayi ta
shiga, ya wara ido yana kallonta yace “waow my
Ashhyy I missed yhu a lot ” Ashnaah tayi
murmushi tana kallonsa ita ma tace “same, sae
da shidda ya kusa ka xo ko?” Yace “wllh daga
xaria na taso sbda ke Ashnaah” tace “eyya to ya
aiki ya kwana biyu” Yace “Alhmdllh dear, kin
rame da yawa,” murmushi tayi tace “ba dole ba”
ya dan yi shiru snn yace “kin san bae dace mu
xauna hka ba kina da aure Fateema, let move out
mu samu ko karkashin tree ne mu xauna sae mu
yi mgna” ta hade rae tana kallonsa tace “hka
nace maka,” yace “no dats d reality” Ashnaah
tace “to na ji sae anjima” kiranta yyi a hnkli ta
juyo tana kallonsa yace “ba mgnan fushi bne
wnn its d fact,” Ashnaah ta sakar masa kuka
tace “ni ban san ynda xanyi ya sake ni ba, bana
son shi, na tsanesa ya cuce ni, ya raba ni da
kowa nawa” kuka ssae ta shiga yi, usman yyi
shiru ya rasa abun cewa, can yace “to ina kika
san shi Ashnaah” bata boye masa komae ba ta
fada masa abun da ya faru tun daga farko har
karshe, usman ya kasa daina kallonta da mmki, a
hnkli yace “to ynxu ya kike so ayi” xata yi mgna
ta hango motar Khaleel, cak komae na ta ya
tsaya ganin dan nesa da su yyi parkin, tana
kallon usman tace “na shiga uku gashi can ya
xo” juyawa yyi yana kallon motar Khaleel, a
tsorace Ashnaah tace “kasan me ka dan koma ta
can sae in fito” bbu musu yyi ynda tace masa, ta
bude Jakarta ta ciro nikaf da sauri ta sa snn
tace “sae mun yi waya” ya gyada mata kai ta
bude motar ta fice kmr munafuka. Da sauri da
sauri ta isa gun da motar Khaleel yake tun daga
nesa ya hangota ya kafa mata ido, tana iso wa
ya hade rae yace “Daga ina kke” ita ma ta hade
rae tace “cafe mana, na je foto copy” fito masa
da handouts din Jakarta tayi da sauri tana nuna
masa, bae ce komae ba ta xaga ta bude motar
ta shiga ya tada suka bar wajen. Karfe takwas
da rabi Khaleel ya shigo gida daga masallaci,
Ashnaah na xaune falo da Ameesha suna kallo
suna cin abinci, kallon abincin Khaleel ke yi yana
yatsine fuska yace “meye wnn” Ameesha tace
“jollof rice ne” yyi mata wani mugun kallo yace
“kin ga ina cin sa ne da xaki girka,” ta dan yi
shiru snn tace “Ca tayi muyi jollof ne shi yasa
nayi” Tsawa Khaleel ya daka mata yace “ita wa?
Ita ta ajiye ki ko ni” Ameesha tayi shiru, Ashnaah
ta mike hade da yin tsaki ta nufi sama da plate
din abincin ta kmr xata tashi sama, masifa
Khaleel ya shiga ma Ameesha kmr xae maketa
ita dae bata ce komae ba har don kansa ya gaji
yyi shiru ya nufi sama, sae a snn Ameesha ta
fashe da kuka Ashnaah ta sauko a fusace tana
kallonta tace “sae ki xauna takaicin namiji ya
kashe ki, shi din wa da xae tsaya yana maki ihu
kmr wani ubanki, iyye? idan ya maki ba kya iya
ramawa sae da ki tsaya kiyi ta kuka, to wllh xa ki
sha wahala, hka kawae ya maida ki kmr baiwarsa
kullum cikin masifa, to wllh gwara ki canxa halin
ki in xa ki ji ta nawa idan ba hka ba kina da
wahala, kuma ko gobe abinda ran mu ke so a
gidan nn xa mu girka, da da bae auro ki ba wani
ke masa girkin ba eatry yake xuwa ba, to ynxun
ma sae ya koma can” ynda kasan wata uwa da
‘yar ta hka Ashnaah ta sa Ameesha a gaba tana
mata fada, Khaleel da tun saukowar Ashnaah shi
ma ya fito ya tsaya daga stairs yana kallonta
yana murmushin courage dinta.