DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
92…..
Juyawa Abba yyi yana ma momy wani irin kallo har lkcn mmki bayyane a fuskarsa, kuka momy ta saki tana kallon likitan tace “ciki fa kace doctor” likitan ya mika masu takardan hannunsa snn ya kara da cewa “amma ta nuna min auransu da mijinta na nn, don hka kar kuyi saurin yanke hukunci, bincike shine abinda…” Wani kallo kawae Abba ke masa, bae Bari ya Kai aya ba yace “ka gama aikin ka yallabae, xan turo driver da kudin ka anjima, tnx 4 ur help” Ashnaah kam tun bayan fitan likitan take ta rusa kukan tashin hnkli ta rasa abun yi, tasan yau kila sae dae wata ba ita ba, duk sae ta nemi xaxxabi da kasalan da take ji ta rasa, mikewa tayi xuciyarta na bugawa ta dauki hijab din ta tasa snn ta dauki wayarta ta fice daga dakin, su Ashfah da shigowarsu knn suka shiga tambayarta lfya amma ko ta Kansu bata bi ba, sakkowa kasa tayi ba tare da ta kalli kowa na falon ba ta nufi kitchen da sauri, dai dai lkcn da Abba ke sallaman likitan sa knn fuskarsa a daure jin maganganun da yake kkrin kawo masa, juyawa Abba yyi ganinta ya daka mata wani mugun tsawa yace “ina xa ki,” Ashnaah bata ko kalle inda yake ba ta shige kitchen a guje ta bude kofar da xae sada ta da garden ta fice, Abba na ganin hka ya bi ta gaban gidan da sauri shi ma, likitan ya bi bayan sa, momy kam xubewa kan kujera tayi tana kuka ssae su Ashfah suka sauko suna tambayarta lfya amma ba bakin mgna, tunda Ashnaah take bata taba irin gudun da tayi ba ranan don kan kace kwabo har ta isa gate, dai dai sanda Abba ya fito knn cikin tsawa yake ce ma mai gadinsa ya rufe masa gate kar ya bari ta fita, kuka Ashnaah ta saki ganin mai gadin ya kulle gate din ga Abba na tahowa, ta durkushe gabansa tana rusa kuka hnklinta a tashe tana cewa “don Allah don annabi kayi min rae ka bude min, kashe ni xae yi wllh” Tahowa kawae Abba yake fuskar nn tasa bbu alamar rahama idon nn nasa ya kada, hkn ya kuma tada hnklin Ashnaah ta shiga kwala ihu, tun kan Abba ya karaso mai gadin ya shiga basa hkuri duk da bae san me ke faruwa ba, amma ko kadan Abba bae Ma san yana yi ba, likitan ya sha gabansa da sauri yace “Haba Alhaji kar ka ce xaka taba ta don Allah, consider situation din da take ciki kar ka ji ma yar ka ciwo, ka kwantar da hnklinka ka saurari bayanin ta tukun” Abba ya tura likitan daga gabansa cikin tsawa yace “gwara in kasheta kawae yau in huta” Ashnaah na jin hka ta shiga gudu tana xaga gidan tana rokon Abbanta cikin kuka, tana ganin momynta ta fito ta nufeta da gudu ta tsaya bayanta tana cewa ta taimaka mata don Allah, Ashfah da tuni ita ma ta fara kuka ta nufi Abbansu ta durkushe gabansa cikin kuka take cewa “don Allah don Annabi Abbanmu kayi hkuri” cikin kuka momy tace “wllh Adam kar ka kuskura ka taba min ‘ya ta da ka taba ta gwara ka Kore mu gaba daya gidan yau” Abba ya tsaya kallonta can yace “hka kika ce koh” kai tsaye momy tace “ehh hka na ce” Abba yace “fine, Ni baxan ma Fateema baki ba amma daga yau na cire ta cikin ‘ya ya na, wato na yafe ta, kar ta kara tunanin tana da uba a duniya, ba ita ba gidan nn, snn idan ta kuskura ta sa kafa ta taka gidan mahaifiyata bn yafe mata ba, ta tafi duk inda xa ta bnda gidan uwata, bn haifi yar da xata ja min abun kunya a duniya ba” cikin tsawa Abba yace “ta xo ta fice min a gida” Momy tace “in har Fateema ta bar gidan nn to ni ma na bar gidan nn” Abba ya daga kafada yace “fine! Ki tafi amma a bakin auren ki” Abba na kai wa nn ya nufi cikin gida da sauri, Ashnaah ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka tana kallon momynta tace “A’a momy kiyi hkuri,
Kar ki ce hka, amma ki yafe ni don Allah nasan tun tasowa ta na kasance warce bata jin maganarku amma momy ni ban taba bin maxa ba duk rashin ji na, ki yrda dani momy mijina bae sakeni, tun daga ranar da na ga takardan nn nasan bashi ne ya rubuta ba don ba ma shi da lfya ranan da na ga takardan, snn ya sha gaya min baxae taba saki na ba idan na bukaci hkn tun farkon aurenmu lkcn ma ba ddin xaman gidan nake ba, amma da yake na dde ina son ya sakeni shi yasa na dauka takardan kawae na dawo gida duk da raina bae so hkn ba, nasan ko min daren ddewa gskya xata bayyana kuma Abbana xae yafe min.” Ashnaah tayi shiru tana kallon momynta da ke hawaye har lkcn, can ta juya ita ma tana hawayen tace “ki daina kuka momy xa mu dinga waya, amma ki taimaka min ki ba Abbana hkuri” Ashnaah na kai wa nn ta soma tafiya ta nufi gate, Ashfah ta bi ta da sauri tana kuka tace “ina xa ki sister” Ashnaah ta share hawayenta tace “gidan mijina xan koma” tana fadin hka ta bar gun da sauri ta bude gate ta fice daga gidan.
Plss sisters ku bar ni in rubuta littafina ynda na tsara, wnda ya ga littafin nn yyi masa ya karanta wnda kuma ya ga bae masa ba ya bar shi kawae, nt dat xa ayi ta min complain ace hka ya kamata in yi ba hka ya kamata in yi ba, hkn bbu ddi Sam, hka aka min lkcn littafin Ikram, gskya ni dae bna jin ddin hka.
5 mins · Khaleesat Haiydar…
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
93…..
Tafiya kawae Ashnaah take ba tare da tasan inda xa ta ba gashi bata fito da kudi ba bare ta sami abun hawa ta hau, gajiya tayi ta nemi dakalin wani da shago ta xauna ta dalilin jirin da take ji ssae ga kasala, lkci daya taji xaxxabin ya dawo mata, wayar da ke hannunta ta kalla don ta ma manta ta taho da shi, nn da nn ta shiga neman layin Khaleel taji bbu kudi a wayar, dafe kanta tayi ta rasa me ke mata ddi ga wani aman da ke taso mata, gun kwanciya kawae take nema a lkcn, pls cal me ta tura masa da sauri bayan kusan minti goma ta ga bae kira ba, ta kuma tura masa ta jira still bae kira ba, ta kusa minti talatin a xaune kanta hade da gwiwanta can dae ta dago a hnkli tana tunanin abun yi, tasan ko taku daya baxa ta iya ba daga wajen faduwa kawae xata yi tsabar jirin da take ji, wasu hawaye ne su ka shiga bin kuncinta ita kam ko me yasa bata da sa’a a rayuwa, a hnkli ta shiga bin inda take da kallo tana tunanin to ko taimako xata nema don gun Akwae mutane da dama suna ta harkan gabansu, ji tayi baxata iya tashi ba kawae ta ci gaba da xamanta a gun, Sadeeq ne ya fado mata, ta dago wayar a hnkli tana kallon screen din, please cal me ta tura masa shi ma, Sadeeq dake xaune kasa falon Abba da dad dinsa ya ciro wayarsa jin alert din msge, ganin sakon yasa ya mike ya ce yana xuwa snn ya fita, kiranta yyi bugu daya Ashnaah ta daga da sauri, Sadeeq yace “ya aka yi Fateema,” a sanyaye Ashnaah tace “kati xaka turo min don Allah” Sadeeq yace “me yasa kika yi abinda kika yi?” Ashnaah da hawaye ya shiga bin kuncinta tace “sbda mijina bae sake ni ba” Sadeeq ya dan yi shiru snn yace “kina ina ynxu?” A hnkli tace “gidan mijina xan je, ina son kiransa ne bni da card” Sadeeq yace “Shknn, Allah ya huci xuciyar Abban ki ya sassauta maki” kai kawae Ashnaah ta gyada masa kmr yana ganinta tana hawaye, yace “xan maki transfer ynxu” yana kai wa nn ya katse kiran, cikin minti biyu taga transfer din dari biyar ta tura masa da text din gdya, tana kkrin dailin nmbr Khaleel kiransa ya shigo, dagawa tayi bata ce komae ba, da damuwa yace “wife kiyi hkuri sae ynxu na ga text din ki, am srry I wasn’t OK ne xuciyata na damuna shine nayi alluran bacci, I just woke up ynxu” kuka Ashnaah ta sakar masa, nn da nn ya rikice mata yana tambayarta me ya faru ta kasa cewa komae sae kuka, ganin ynda ya birkice ya sa a sanyaye tace “Ka kuma hada ni da parent dina hnklin ka ya kwanta, ba ka min adalci ba, sae in iya cewa ka cuce ni ma kawae, me yasa ka min hka doctor….” Kuka ne ya ci karfinta ssae, Khaleel da hnklinsa yyi mugun tashi duk da ya gano dalilin maganganun nata yace “plss ki gaya min me ya faru, kina ina ne?” Cikin kuka ssae tace “ba dole ka tambaye ni ina ina ba” kmr xae mata kuka yace “plss wife kar ki bari a cire cikin nn am beggin yhu ki tausaya min don’t let dat plss, ki bari mu ga bbynmu” Ashnaah da mmki ya cika ta ta ma rasa me xa ta ce masa, wato ashe ya ma san tana da ciki knn, Shiru tayi tana naxarin magungunan da ya bata ranan har yana cewa kar ta kuma shan ko wani magani xa a bata a gida, kuka ta fashe da tace “wllh baka da imani, ka hada ni da iyayena kawae ka raba ni da su don son xuciyar ka, to bana son cikin xubar wa xanyi” kuka kawae take kmr ranta xae fita ta katse kiran, Khaleel da idanunsa suka kada suka yi ja ya dafe kansa da ke Sara masa xuciyarsa nai masa kuna. Kiranta ya kuma yi, Ashnaah da ke kuka har lkcin ta kasa kin daga kiran nasa duk da ta so yin hkn, ta dauka tayi shiru, a sanyaye yace “kiyi hkuri fateema xan cire maki cikin na maki alkawari tunda ba kya so, ynxu plss ki gaya min inda ki ke” taki cewa komae na wani dan lkci snn a hnkli ta gaya masa inda take, cikin mintunan da ba su wuce sha takwas ba Khaleel ya iso gun da ta gaya masa take, yana gama parkin ya fito ya nufi inda ya hangota da sauri ya durkusa gabanta ya kamo hannunta da damuwa yace “am vry srry wife, I caused all dis” kuka ta sakar masa, duk ya rikice yana lallashinta, ganin taki yin shiru yasa dago ta ya rungume abarsa, ta tsaida kukan da take da sauri ta kwace kanta ganin a titi suke, kama hannunta yyi tana ganin jiri har suka isa motarsa snn ya bude mata front seat ta shiga, ya xaga ya shiga shi ma ya tada motar suka bar wajen, ssae ta ba Khaleel tausayi ganin ynda ta da da ramewa da ganinta ka ga mai laulayi, ga kuma kukan da ta ci, kwantar mata da kujerar motar yyi ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa, gidansa ya nufa da ita, yana gama parkin ya fito ya dauki abarsa ya shiga ciki da ita, ta bude ido da sauri tace “meye hka” bedroom dinsa ya shiga da ita, ya cire bedsheet din kan gadon snn ya kwantar da ita.
94…..
Mikewa xaune tayi da sauri ta wani daure fuska don haushinsa kawae take ji, a sanyaye yace “srry na ga kina bacci ne” ta dauke kanta kawae har lkcn fuskarta a daure, mikewa yyi jiki ba kwari ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, hawaye ne ya shiga bin kuncinta duk she is confuse fushinta xata nuna masa ko jawo mijinta xata yi jiki. Jinginar da kanta tayi jikin gadon tana tunanin rayuwarta tun daga ranan da ta fara haduwa da Khaleel, wasu hawaye masu xafi suka shiga sakko mata, tana nn a hka har bayan minti talatin ta ji an kira sllhn Azahar, mikewa tayi a hnkli don xuwa tayi alwala taji jiri ya debeta ta dafa bango da sauri kan ta kai kasa ta koma kan gadon ta xauna, kasa mikewa tayi har aka idar da sllh Khaleel ya shigo dakin, ba karamin tausayi ya bata ba yanayin da ya shigo, ya karaso gabanta ya duka ya ajiye mata ledan abincin hannunsa da plate yace “ga abinci na siyo maki ki sakko ki ci” kallonsa kawae take ya bude abincin ta ga dafa duka ne da naman kaxa, nn da nn cikinta ya hautsine aroma din abincin na bugar ta, mikewa ta shiga kkrin yi da sauri ya lura da hkn ya mike yace “me ya faru, amae kike ji” toshe bakinta tayi ta sakko daga kan gadon tayi baya xata fadi ya kamota da sauri ta durkushe kasan dakin ya bi ta har lkcn yana rike da ita ta shiga kwarara masa aman a jiki, ssae ta bashi tausayi ganin bbu komae cikinta, gashi she is too young ace tana da ciki ynxu, yana rike da ita yana mata sannu a sanyaye har ta gama ta fada jikinsa tana mayar da numfashi ya rungumeta, sun fi minti biyar a hka snn ya dago kanta a hnkli yana kallon idonta da yyi ja yace “Sannu wife” sunkuyar da kanta tayi kawae, mikewa yyi ya dauketa suka nufi bathroom, da kansa ya gyara mata jikinta bayan ya cire mata kaya, snn shima ya gyara nasa jikin ya daukota suka fito ya kwantar da ita kan gado ya lulluba ta da bargo snn ya shiga gyara dakin, ko da ya gama har tayi bacci ya xauna gefen gadon a hnkli yana kallon kyakkyawan fuskarta wani mugun shaukin sonta na fixgarsa, yasan he can’t do without Fateema, daura hannunsa yyi a hnkli kan goshinta ya ji xafi ssae, ya mike ya fita xuwa kitchen ya hado Milo kawae ba madara ya dawo dakin snn ya shiga tashinta a hnkli, bude ido tayi tana kallonsa, ya dago ta yace “ki daure ki sha tea plss sae in ba ki magani, jikin ki yyi xafi” girgixa masa kai tayi da kyar tace “Amae xan yi” rungume ta yyi yace “A’a baxa ki yi ba ruwan tea ne kawae, ki rufe idon ki ki shanye ynxun nn” girgixa masa kai tayi alamar baxa ta sha ba don ta kasa mgnr ma gaba daya, ya dauko tean ya dago kanta, ta sakar masa kuka tana girgixa kai, da kyar ya lallabata tayi sip uku don bbu xafi, yyi yyi da ita amma ta ki karawa, rungumeta yyi ya shiga shafa bayanta a hnkli ganin amae take son yi, har sae da ya ga ya fada mata snn ya kwantar da ita yace yana xuwa, makullin motarsa ya dauka ya fita ya nufi pharmacy ya siyo magunguna da allurori ya dawo ya sameta tana bacci, yana cikin hada alluran wayarsa da ya ajiye gefen gadon yyi ring, ya dauko wayar yana kallon screen din ya ga Dad dinsa ne me kiran, gabansa ya fadi don har ya manta rabon da ya kirasa, ‘karan wayar ya tada Ashnaah ta shiga juye juye don wani ciwo da taji cikinta ne ko mararta ne ta kasa tantance wanne ne ke mata ciwon, mikewa Khaleel yyi ya daga kiran, gabansa na ci gaba da faduwa yyi sallama a hnkli, “Maxa maxa ka xo ynxun nn ka same ni a gida duk inda kke” abinda ya ji dad dinsa ya ce knn ya katse kiran a take, Khaleel ya ajiye wayar a sanyaye ya juya yana kallon Ashnaah ya karasa kusa da ita da sauri ya dagota yace “me ya faru” ta fashe da kuka tace “wayyo Allahna ciwo yake min” da damuwa yace “ina?” Taki cewa komae sae kuka take tana yarfe hannu, allurorin da ya gama hadawa ya dauko don yi mata, da kyar ya samu yyi mata don ta basa wahala ssae, ya rungumeta yana lallashinta ta gaji da kukan tayi shiru don kanta daga karshe bacci ya dauketa.
18 mins · Khaleesat Haiydar…
Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
95…..
Mikewa Khaleel yyi bayan ya lullube ta ya koma can gefen gado ya xauna ya dafe kansa yana tunanin kiran da Dad dinsa yyi masa na gaggawa, juyawa yyi yana kallon Ashnaah, can ya Mike yana kallon agogo ya ga uku da rabi ya dauki car key dinsa ya fice daga dakin don xuwa amsa kiran dad din nasa don ya san baxata tashi ba a lkcn, ana kiran sllhn La’asar ya isa gidan, sae da ya fara shiga masallaci yyi sllhn snn ya shiga gida, Ummi na kitchen da rukayya suna girki, ya shiga kitchen din ya gaida umminsa, ta amsa masa ba tare da ta kallesa ba, jikinsa yyi sanyi jin irin amsawar da Ummi tayi masa, yana kallon rukayya yace “Abba fa?” Rukayya tace “yana falonsa” a sanyaye Khaleel ya nufi falon dad dinsa a Sama yyi sallama ya shiga, xaune ya sami dad din nasa da amininsa sae kawunsa, ya nemi kasa daga gefen kawunsa ya xauna ya gaishe su kansa a kasa, Kawunsa kadae ne ya amsa, Dad dinsa ya mike yana masa mugun kallo yace “me na gaya maka kwanaki Khaleel” shiru Khaleel yyi bae ce komae ba, ya daka masa tsawa yace “are yhu daft?” Khaleel ya dago a hnkli yana kallonsa still bae ce komae ba, Dad yyi murmushin takaici yace “har ni xaka dinga ja ma ana biyo wa har gida ana ci ma mutunci ko Khaleel,” sunkuyar da kai Khaleel yyi kawae, Kawunsa yace “wae yarinyar nn ita kadae ce mace a duniya Ibrahim, yau ko da ace baka saketa ba baxa ka iya rabuwa da ita ba ko dan tijaran da mahaifanta ke ma ubanka?” Dad yace “to bari ka ji khaleel wllh daga yau ka kara nuna kasan yarinyar nn ba ni ba kai har abada, maxa maxa ka sallameta ta koma inda ta fito idan ba hka ba ka ga bacin raina, na haneka da kara interact da ita bbu kai ba ita, na raba ka da yar matsiyatan nn daga yau ta je can ta karata, kuma duk inda xa mu shiga ka amsa cikin da ke jikinta na ka ne bn yafe maka ba, tashi ka ban waje malam” Khaleel da tun fara mgnr Dad dinsa xufa ke karyo masa ya dago kai da kyar yana kallon dad din nasa da idanuwansa da suka kada, Alhaji mukhtar ya daka masa tsawa yace “uban me kke jira mister man, c’mon get lost” hawaye ne suka shiga sakko masa da kyar yana girgixa kai yace “Dad ni bn saketa ba wllh matata ce har ynxu, kayi hkuri dad I can’t deny her pregnancy” bae rufe baki ba dad ya sauke masa mari, tunda yake a iya saninsa Dad dinsa bae taba marin sa ba sae ranan, Khaleel ya kasa dago kansa cikin tsawa dad yace “har ni xaka bude baki kana gaya ma wnn mgnr? to wllh Khaleel I mean my wordz idan har baka rabu da yar marasu mutuncin nn ba bbu ni bbu kai, shari’a fa ubanta yace xae yi da mu,” Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye yace “kayi hkuri Dad idan nace xan guje ta ban san halin da xata shiga ba, kuma ni ina son matata, forgive me dad” kallonsa duk suka tsaya yi da mmki, dad yyi murmushin takaici yace “hka kace koh?” Khaleel bae ce komae ba har lkcn yana rike da kansa, dad yace “gud, bani dukka makullan gidajena dake hannunka da documents dina,” Khaleel ya gyada kai da kyar yace “toh” snn ya mike ya fice daga falon duk suka bi sa da kallo da mugun mmki, gida Khaleel ya koma, har lkcin Ashnaah bata tashi ba ya dauki duk kaddaran dad dinsa dake hannunsa a dakinsa, snn ya fito ya samu mai gadinsa ya basa cheque din dubu hamsin yace ya ja jari ya sallamesa don xae rufe gidan ne sanin gidan dad dinsa ne ba nasa ba, abubuwan da yasan xae bukata ya kwashe a dakinsa ya kai cikin mota, snn ya dawo dakin ya shiga tada Ashnaah a hnkli, bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace “srry na tashe ki koh?” Dagota yyi ya dauki hijab dinta ya sa Mata snn suka fito ya kulle gidan, ita dae bin sa kawae take don jiri ne ke dibanta, mota ya bude mata ta shiga ya kulle snn ya xaga ya shiga motar ya fice daga gidan ya fito ya kulle gate din ta waje don har mai gadin ya wuce snn ya koma motan ya shiga ya tada ya nufi gidansu, bacci Ashnaah take daga xaunen da take cikin motar ko da ya isa kofar gidansu, hkn ya basa daman fita ya nufi cikin gidansu ya haura sama xuwa falon dad dinsa, ynda ya barsu hka ya same su, ya isa gaba