DR KHALEEL, Complete Hausa Novel.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar102….Sae da wayar ta kusa katsewa snn Khaleel ya daga, shiru yyi da farko don ya rasa ta inda xae fara mgnan, jin momyn ta ambaci sunan Fateema yasa ya bude baki da kyar yyi mata sallama, shiru momy tayi daga daya bangaren, sallaman ya kuma yi momy ta amsa wnn karan, dukar da kai yyi kmr tanaganinsa ya gaisheta, momy ta amsa ta kuma yin shiru, rasa me xae kuma cewa yyi, can yyi saurin cewa “Amm bacci take momy, idan ta tashi xa ta kira” Momy tace “OK ngd” sallama yyi mata ta kashe wayan, Khaleel ya sauke ajiyar xuciya ya ajiye wayar ya xauna gefen gado yana kallon Ashnaah, wayarsa ya shiga ring ya daga yana kallonme kiran ya ga umminsa ce, ya daga tare da mata sallama suka gaisa, Ummi tace “Fateema fa? Ya jikin nata?” Yace “Da sauki Ummi, bacci ma take” Ummi tace “to Allah ya sauwake, dama Rukayya ce tace tana son xuwa, shine nace bari in kiraka ka fada mata inda kuke” Khaleel yace “to Bari in kirata Ummi” Ummi tace “toh shknn, ka gaida fateeman idan ta tashi” sallama suka yi ya katse kiran ya shiga neman layin kanwartasa don yi Mata kwatancen inda su ke. Yana ajiye wayar kiran Zeenat ya shigo wayar kuma, dagawa yyi suka gaisa tace “dama ina son xuwa in duba Fateema ne doctor” Khaleel yace “OK bbu damuwa, lemme sendyhu address” Address din gidan Al-ameen ya tura mata, Karfe sha daya Rukayya ta iso gidan ta kira shi, Khaleel ya fito ya tare ta su ka shiga gidan a tare, falo ta bar abincin hannunta da Ummi tace ta kawo ma fateema ya nufi sama da ita, a stairs yake tambayar ta ko dad dinsu na nan, tace “ya tafi Abujajiya,” yace “OK, me kika kawo a kula” tace “waina ce da miya” Ashnaah na xaune suka shigo dakin, ta daga kai tana kallon Rukayya, Rukayya ta karaso inda take ta xauna gefen gadon tace “sannu, ya jikin?” Ashnaah tace “da sauki” Rukayya tace “to Allah ya kara lfya” mikewa tayi ta fita daga dakin don ba sabawa suka yi ba ta koma falo, Khaleel yace “Ummi ta kawo maki waina xa ki ci?” Shiru tayitana kallonsa, nn da nn ta ji sha’awar wainan sae dae tana tsoron kar ya sa ta amai, kmr xata yi kuka tace “nima bn san ko xan ci ba” murmushi yyi ya mike ya fita dakin, sae ga shi ya dawo rike da plate din wainar da miya a wani bowl, dauke kanta tayi dasauri ya karaso yace “baxa ki yi amae ba wife, dan kadan xa ki ci” a hnkli ta dago kanta tana kallon abincin, ya sakko da ita kasa yace “toh ci kadan ba da yawa ba” ta dan leka miyan ta dauke kai tace “ni hka xan ci bbu miya” yace “to dauka ki ci” daukan daya yyi ya kai mata baki ta karba ta shiga ci a hnkli,tun da ta fara laulayi sae ranan ta sa abinci baki, wayarsa ya dauka jin ana kiransa ya ga Zeenat ce, ya dauka tace ga ta a kofar gida, Rukayya ya kira yace ta je ta shigo da ita, Ashnaah tace “wacece?” Ya ajiye wayar hannunsa yace “Zeenat ce xa ta xo gaishe ki wae” ta hade rae tace “me ya same ni?” Yi yyi kmr bae ji ta ba, sae kuma yace “momy ta kira kidaxu kina bacci na dauka” Ashnaah tace “wace momy” ya daga manyan idonsa yana kallonta yace”ur mum” shiru tayi tana kallonsa, a hnkli tace “me kace mata?” Ba tare da ya kalleta ba yace “na ce kina bacci” wayarsa ya dauka ya mika mata yace”gashi ki kirata” ba musu ta karbi wayar a sanyaye, ya mike ya fita daga dakin, bugu biyu momy ta dauka, Ashnaah tayi mata sallama tare da gaisheta, momy tace “kina lfya fateema? Ya jikin?” Ashnaah tace “da sauki momy, kin kira daxu ina bacci” momytace “ehh, kina dae cin abinci koh?” Ashnaah ta gyada mata kai tace “ina ci momy, Ashfah fa?” Momy tace “dama ita ce ke damuna tana son xuwa gun ki, shine nace Bari in kira in gaya maki ki tura mata address” a sanyaye Ashnaah tace “Abba fa momy?” Momy ta dan yi shiru snn tace “baya nn, yana Abuja” Ashnaah tace “toh xan turo mata address din ta nmbrta” sallama suka yi Ashnaah ta ajiye wayar Khaleel, jikinta a Sanyaye, duk lkcn da ta tuna kalaman Abbanta na karshe a kanta sae ta ji hnklinta ya tashi, bata fatan Allah ya dauki ranta bata yi reconcile da Abbanta ba ya yafe Mata, da koh ta bani a rayuwa, hawaye ne ya shiga sakko Mata, dai dai nn Khaleel ya shigo dakin, karasowa yyi inda take da sauri ganin hawaye fuskarta da damuwa yace “me ya faru wife, momy ta ji haushi na daga kiranta koh?, am vry srry I won’t do dat again” girgixa masa kai tayi tana hawaye a hnkli tace “bata ce komae ba, Abbana nake tunani” Khaleel ya dan sauke ajiyar xuciya yace “kar ki damu wife, wataran sae lbri, kuma In’sha Allah duk xa mu gama da iyayen mu lfya” gyada masa kae kawae tayi, yace “to share fuskar ki, kin ga Zeenat taxo gaishe ki” lkci daya Ashnaah ta hade rae tace”wae gaisuwar me xata xo ta min,” Khaleel yyi shiru snn yyi murmushi, Ashnaah tace “bana son gaisuwar, ta wani xo wajen ka ta fake da cewar ni taxo gaisarwa meye hadi na da ita, ina ta san ni ko kuma na Santa, kawae ta xo wajen ka ta wani ce ta xo gaishe ni” fashewa da kuka tayi, Khaleel ya danne dariyarsa yace “Haba bby meye abun kuka a nn, ba sae in bar gidan ba idan ta gama gaishe ki ta yi wucewarta” Ashnaah ta galla masa harara ya mike yana dariya ya fita, bin sa tayi da kallo lkci daya ta ji haushin kanta, share hawayen fuskarta ta shiga yi a hnkli, y will she show she cares dat much abou him, he is d cause of everythin she is goin through, me yasa son sa ya shigeta lkci daya bayan duk wahalan da ta sha a hannunsa, girgixa kai tayi ta tura wainan gabanta cike da jin haushin kanta, dae dae nn Zeenat ta shigo dakin da sallama rike daflask a hannunta da ledan fruit, Ashnaah ta sunkuyar da kai da sauri, Zeenat ta karaso gabanta tana murmushi tace “sannu Fateema, ya jikin” Ashnaah ta kasa yi mata abinda tayi niya, ta dago kanta ta dan kirkiri murmushi tace “da sauki, Alhmdllh,” Zeenat ta ce “toh Allah ya kara lfya, ga kunu na yo maki” Ashnaah tace “to ngdd Allah ya saka da alkhairi” Mintin Zeenat goma a dakin ta mike tace “xa ta koma” Ashnaah ta kuma yi mata gdya snn tace bari ta rakata falo, duk ynda Zeenat taso tayi xamanta ta bar rakiyan kn yadda Ashnaah ta yi suka sauko har falo, Zeenat na kallon Rukayya dake kallo a falon tace “doctor fa Rukayya?” Rukayya tace “ya fita wllh” Ashnaah na jin hka ta juya ta nufi sama, Zeenat tace “to idan ya dawo ki ce masa na tafi” Rukayya tace to, snn suka yi sallama ta fita, sae a snn hnklin Ashnaah ya kwanta ta koma sama, Karfe biyu saura Rukayya tayi ma yayanta da Ashnaah sallama ta wuce gida. Da yamma Karfe hudu da rabi Khaleel ya sa Ashnaah ta shirya suka tafi can gidansu tun da Abbansa na Abuja. Suna gidan har kusan Karfe shidda sae ga Abba ya dawo daga Abuja, ba karamin tashi hnklin khaleel yyi ba don bae taba xaton dawowan dad din nasa a lkcn ba, toh da wani idon ma xae kalli mahaifin nasa, da ma bae shigo da motarsa cikin gidan bne, ita kanta Ummi bata so dawowan mai gidan nata ba a lkcn sanin ita kanta sae ranta ya baci, ae kam hka ya faru don ko da ta je yi masa sannu da xuwa shareta yyi, ta bar masa dakinsa kawae, tana dawowa bedroom dinta Khaleel da ke xaune ya rike kansa ya mike da sauri yace “Ummi xa mu tafi” Ummi ya galla masa harara tace “tana baccin xa ku tafi” ya juya yana kallon Ashnaah da kebacci tun shigowar su gidan, a hnkli yace “tashin ta xan yi Ummi” Ummi tace “bbu inda xa ku sae ta tashi” kasa mata musu yyi ya koma ya xauna, ita kuma ta ci gaba da abinda take, a hnkli yace “xan iya xuwa gaida dad Ummi” girgixa masa kai tayi ba tare da ta kallesa ba tace “A’a kar ka je” bae kuma ce mata komae ba har aka kira sllhn Magrib snn ya mike ya shiga bathroom dinta yyi alwala ya ce ya tafi masallaci, Khaleel bae nufi masallacin da yasanxae hadu da dad dinsa ba, kuma ana idar da sllh ya dawo gida don ma kar su hadu bakin gate. Da kyar ya iya cin shinkafar da Ummi tayi masa ranan bayan ya dawo daga sllhn isha, Karfe takwas da kusan rabi Ashnaah ta tashi, Ummi ta kawo mata kunun da tayi mata, ta mike ta nufi bayi ta kuskure bakinta snn ta dawo ta dauki kunun tana sha, Karfe tara Khaleel ya shiga dakin rukayya yace ta duba masa falo ko dad na nn don xa su koma gida ne, ta dawo tace baya falo, komawa dakin umminsa yyi yace da ita xa su wuce gida, Ashnaah ta Mike ta dauki hijab din da Rukayya ta bata ta sa snn suka yi ma Ummi sae da safe, Ummi tayi masu Allah ya kiyaye suka fita daga dakin tana gaba yana biye da ita a baya, ido hudu Khaleel yyi da dad dinsa da sakkowansa falon knn yana cin fruit a kan centre table, Khaleel ya dauke kansa da sauri ya kasa ci gaba da tafiyar ya tsaya stairs din karshe, Ashnaah ta juya tana kallonsa, ita ma jikinta yyi sanyi, ta karasa falon a sanyaye ta isa inda dad din yake ta durkusa kasa ta gaishesa kanta a sunkuye, dago kai yyi yana kallonta, ya ajiye fork din hannunsa yana dan murmushi yace “lfya lau, kun xo lfya?” Ta dago Kai tace “lfya lau Abba,” dad yace “to madallah, ashe kuna ciki nayi xaton kun tafi ne” ta girgixa kai tace “ba mu tafi ba” Dad yace “to yyi kyau, ya jikin naki?” Tace “da sauki Abba” yace “to Allah ya sauwake, ko xa ki ci kankanan ne in dibar maki” tayi murmushi tace “Aa nagode Abba” dad yace “A’a baria debar maki dae” murmushi ta kuma yi bata ce komae ba don sae taji kankanan ya bata sha’awa, dad ya dauki wani plate ya shiga deban mata kankanan snn ya sa mata toothpick ya mika mata, akunyace ta karba tare da yi masa gdya, yace “tashi ki koma kujera toh” kin tashi tayi ta shiga cin fruit din nn inda take, sae ta ji ina ma Abbanta ne hka, tunanin hka ya sa kwalla ya taru a idonta.